'Yan sandan yankin Baidoa sun bayyana cewa, an samu fashewar bom da aka dasa cikin wata mota a wani otel dake yankin Baidoa, kana wani dan kunar bakin wake ya tada wani bom din dake jikinsa a wani otel na daban dake yankin.
Wadannan hare-haren biyu sun yi sanadiyyar mutuwar mutane a kalla 21, yawancinsu su ne fararen hula.
Ƙara sabon ra'ayi