Tsawaita Lokacin Zabe A Iran Har Sau Hudu
Ma'aikatar Harkokin Cikin Gida Ta Tsawaita Loakcin Zabe
Hukumar Zaben da ta ke a karkashin ma'aiaktar harkokin cikin gidan Iran, ta sanar da tsawaita lokacin kada kuri'a da sa'oi 2:a dare a dukkanin fadin kasa.
A wani bayani da ma'aiakatar ta fitar dazu ta yaba da yadda mutane su ka fito da yawa domin yin zaben 'yan majalisar shawarar musulunci da kuma majalisar kwararru, an tsawaita lokacin yin zaben da sa'oi 2 na dare.
Tun da safiyar yau juma'a ne dai miliyoyin mutane su ka fito domin zabar 'yan majalisun shawarar musulunci da kuma na kwararru. Da akwai mutane miliyan 55 da su ka cancanci kada kuri'a a Iran.
Ƙara sabon ra'ayi