Kamfanin Dillancin Labarun Faransa ya nakalto majiyar Saudiyya na cewa; Sojan kasar guda ya halaka sanadiyyar harbo makami daga kasar Yemen.
Mai magana da yawun ma'aikatar cikin gidan Saudiyya ya sanar da cewa; An harbo makamin ne akan sojojin da su ke sintiri a garin Najran da ke kan iyaka. Daya daga cikin sojojin ya mutu bayan da ya ji rauni mai tsanani.
Da dama daga sojojin Saudiyya ne dai su ka mutu a sanadiyyar harin da sojojin Yemen su ke kawo musu daga kan iyaka.
Kusan shekara guda kenan da Saudiyyar ta shelanta yaki akan kasar Yemen wanda kawo ya zuwa yanzu ya ci dubban rayukan 'yan kasar mafi yawancinsu fararen hula, musamman mai dai kananan yara da mata.
Ƙara sabon ra'ayi