Sojojin Gwamnatin Libya Na Samun Ci Gaba A Benghazi

Runbdunar sojojin kasar Libya ta bayyana cewa sojojin kasar suna samun ci gaba a fafatawar da suke da mayakan 'yan ta'adda na Daesh a garin Benghazi.
A rahoton da tashar talabijin ta Russia Today ta bayar, kakakin rundunar sojin kasar Libya Akram Bu-haliqa ya fadi a daren jiya Lahadi cewa, suna samun ci gaba matuka a yakinsu da 'yan ta'addan Daesh a Benghazi, kamar yadda kuma ya bayyana cewa sun kwace iko baki daya da garin Ajadabiya daga hannun 'yan ta'addan.
Kakakin rundunar sojin kasar ta Libya ya kara da cewa, a dauki-ba-dadin da aka yi jiya a garin na Benghazi tsakanin dakarun kasar da kuma 'yan ta'addan Daesh, sojoji 3 sun rasa rayukansu, yayin da 'yan ta'adda 15 suka halaka.

Ƙara sabon ra'ayi