Jiragen Saman Yakin Saudiyya Suna Ci Gaba Da Kai Hare-Hare Kan Kasar Yamen
Jiragen saman yakin masarautar Saudiyya da na kawayenta sun kai wasu jerin hare-haren wuce gona da iri kan yankuna daban daban na kasar Yamen lamarin da ya janyo hasarar rayuka da barnata dukiyoyi.
Kamfanin dillancin labaran kasar Yamen {SABA} a yau Lahadi ya watsa rahoton cewa: Jiragen saman yakin masarautar Saudiyya da na kawayenta sun kai wasu jerin hare-haren wuce gona da iri kan yankuna daban daban na kasar Yamen da suka hada da babban birnin kasar Sana'a, Sa'adah, Ta'az, Ma'arib, Lahaj da Umran.
Rahoton ya kara da cewa: A harin da jiragen saman yakin masarautar ta Saudiyya suka kaddamar kan yankunan da suke lardin Sa'adah sun kashe mutane fiye da 30 da suka hada da kananan yara 11 gami da mace guda tare da jikkata wasu adadi masu yawa.
Har ila yau jiragen saman yakin na Saudiyya sun yi luguden wuta kan babban filin jirgin saman kasa da kasa da ke birnin Sana'a fadar mulkin kasar ta Yamen, kamar yadda suka kai hare-haren rashin tausayi da imani kan gidajen talakawa a yankunan da suke lardunan Ta'az, Ma'arib, Lahaj, Umran da sauransu.
Ƙara sabon ra'ayi