An Tsawaita Dokar Ta Baci A Faransa

"yan majalisa sun amunce da gagarimin rinjaye da kudirin
Majalisar dokokin Faransa ta amunce da gagarimin rinjaye da bukatar gwamnatin kasar na tsawaita dokar ta baci da watanni uku a duk fadin kasar.
'yan majalisu 212 ne suka amunce da kudirin, yayin da 31 suka ki amuncewa da hakan a jefa kuri'a da aka yi jiyya Talata.
Dama kafin hakan majalisar datijan kasar ta maunce da wannan kudirin da gagarimin rinjaye.
kasar Faransa dai na cikin shirin ko- ta- kwana tun a watan Nowamba bara, bayan da hare-haren ta'adancin da aka kai a Paris babban birnin kasar wanda suka yi sanadin mutuwar mutane 130 tare da jikkata wasu sama da 350.

Ƙara sabon ra'ayi