"Yanto Da Mutane Da Dama Daga Hannun 'Yan Bokoharam

 Sojojin Najeriya Da Na Kamaru Sun 'Yanto da mutane masu yawa da kungiyar Bokoharam ta yi garkuwa da su.
Kakakin Sojan Najeriya Sani Usman ya fada a wani bayni da ya fitar cewa; A wani harin hadin guiwa a tsakanin sojojin Najeriya da Kamaru an kwato da mutane 112 da su ke karkashin kangin yan kungiyar ta Bokoharam.
Bayanin ya kunshi cewa; Mutanen da aka 'yanto a Jahar Borno da ke arewa maso gabacin kasar, sun kunshi maza 8 da mata 36 sai kuma kananan yara 68.
Kakakin Sojan na Najeriya ya ci gaba da cewa; "Yanto da mutanen ya zo ne a matsayin sakamakon hadin guiwa na kasashe biyu a fada da ayyukan ta'addanci.

Ƙara sabon ra'ayi