Dakarun Sriya Sun kame wata mota dauke makaman Isra'ila

 Dakarun tsaron kasar Siriya sun gano tare da kame wata Mota dake dauke da makamai kirar haramcecciyar kasar Isra'ila a gefen yammacin jihar Sawida.
Kamfanin dillancin labaran Siriya Sana ya habarta cewa a safiya jiya Lahadi Dakarun tsaron Siriya tare da goyon bayan Al'umma sun samu nasarar cabke wata mota shake da makamai kirar Haramcecciyar kasar Isra'ila da take aikewa ga 'yan ta'addar ISIS da kuma Annusra a gefen yammacin garin Sawida.
Makan dai sun hada da manyan bindigogi na zamani, makamai masu lizzami, gurnaiti masu yawa da saurensu.
kafin haka dai, dangane da alakar kungiyoyin 'yan ta'addar da magabatan haramcecciyar kasar Isra'ila, kafafen watsa labarai sun watsa labarin cewa kungiyar 'yan ta'addar ISIS na fasa kwabrin danyen man fetur din da ta sace daga kasashen Siriya da Iraki zuwa haramcecciyar kasar Isra'ila.

Ƙara sabon ra'ayi