Jagora Ya Kirayi Jami'an Iran Da Su Yi Taka Tsantsan Da Yaudarar Amurka
Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewar nasarar da Iran ta samu a yayin tattaunawar nukiliya da manyan kasashen duniya ta same ta albarkacin tsayin dakan al'ummar kasar da kuma kwarewar masananta yana mai kiran jami'an kasar da su yi taka tsantsan da yaudarar Amurkawa.
Jagoran ya bayyana hakan ne a wata ganawa da yayi yau din nan da jami’ai da masu gudanar da zaben majalisar shawarar Musulunci da kuma na majalisar kwararru ta jagoranci ta kasar inda ya ce: Nasarar da aka samu a fagen nukiliya, ta samu ne albarkacin kokarin masanan Iran, ciki kuwa har da shahidan nukiliyan su hudu masu girma bugu da kari kan goyon baya da tsayin dakan al’umma, sannan da kuma kokarin jami’an gwamnati wanda hakan ne ya tilasta wa makiya ja da baya a wasu bangarorin.
Har ila yau kuma yayin da yake magana kan manufar makiyan al'ummar Iran musamman Amurka wajen sanya wa Iran takunkumi da sauran matsin lamba, Ayatullah Khamenei ya bayyana cewar: Manufar makiya wajen sanya wadannan takunkumin, ita ce tunzura mutane da sanya su fitowa kan tituna don nuna rashin amincewarsu. To amma mutane sun tsaya kyam, sannan tare da jami’an gwamnati sun tabbatar da daukaka da mutumcin kasar nan.
A wani bangare na jawabin nasa, Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya jinjinawa dakarun kare juyin juya halin Musulunci na kasar saboda nasarar da suka samu wajen kame sojojin ruwan Amurka da suka shigo cikin ruwan Iran a kwanakin baya yana mai kiran sauran jami'an kasar da su yi koyi da dakarun kare juyin wajen sanya ido kan iyakokin kasar da kuma duk wani abin da zai cutar da ita, don su yi maganin hakan cikin gaggawa.
Ƙara sabon ra'ayi