Jagoran Juyin Islama A Iran Ya Yi Allawadai Da Kisan Gilla A Kan Sheikh Nimr

 Jagoran juyin juya halin muslunci a Iran Ayatollah Sayyid Ali Khamenei ya yi Allawadai daakkakusar murya dangane da matakin da masarautar Saudiyya ta dauka na kashe Sheikh Nimr saboda dalilai na siyasa.
Jagoran ya bayayna hakan ne a yau a lokacin zaman bayar da darasin fikihu da yake gabatarwa, inda ya ce wadanda suka aikata wanann aiki su ne suke zubar da jinin al'umma a kasashe daban-daban a yankin gabas ta tsakiya da hakan ya hada da Yemen da Bahrain da sauransu.
Ayatollah Khamenei ya ce ko shakka babu abin masarautar iyalan gidan ta Saud ta yi babban kure ne na siyasa, kuma babu makawa hakan zai jawo mata matsaloli da ba ta tsammani, domin kuwa Allah baya yafe jinin mumini da aka zubar a kan zalunci.
Ya kara da cewa hakika Sheikh Nimr wani babban jigo ne na zaman lafiya a Saudiyya, domin duk da irin zaluncin da al'ummar yankunan gabashin Saudiyya suke fuskanta tsawon shekaru, ya kasance a sahun gaba wajen kiran mutane da su guji duk wani abin da zai haifar da zubar da jini, kada kuma su dauki makamai domin yaki da gwamatin Saudiyya, amma su bayyana ma duniya zaluncin da take yi a kansu.

Ƙara sabon ra'ayi