Zanga-Zangar Allawadai Da Kashe Sheikh Nimr A Gabashin Saudiyya

 Dubban mutane a gabashin Saudiyya suna ci gaba da gudanar da zanga-zangar tir da Allawadai da kashe Sheikh Nimr da masarautar kasar ta yi.
Jaridar Al'ad ta kasar saudiyya ta bayar da rahoto a shafinta na yanar gizo cewa, tun bayan kashe babban malamin addini kuma jagoran mabiya mazhabar shi'a a Saudiyya da masarautar kasar ta yia aranar Asabar da ta gabata, har yanzu ana ci gaba da zanga-zanga a dukaknin yankunan gabashin kasar ta Saudiyya.
Rahoton ya ce masarautar Saudiyya ta jibge dubban 'yan sanda da sojojia a dukkanin yankunanan gabacin kasar, wadanda mazaunasu mabiya mazhabar shi'a ne, domin murkushe duk wani gangami ko zanga-zangar kina amincewa da abin da ya faru, inda a jiya jami'an tsaron masarautar Al Saud suka kashe wani daga cikin masu gangami a garin Awamiyya mai suna Ali Imran Dawudi a garin Al'awamiyyah, tare da jikkata wasu da dama

Ƙara sabon ra'ayi