SHADAR SAMIR QANTAR DAYA DAYA CIKIN KOMADOJIN KUNGIYAR HIZBULLAH

Samir Qantar dais hi ne dan kasar Lebanon wanda yake dadewa a cikin kurkukun
Shahadar Samir Qantar daya daga cikin komandojin kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon a kasar Syria ya gamu da maida martani da dama a kasar Lebanon da kuma sauran kasashen yankin.
Samir Qantar dais hi ne dan kasar Lebanon wanda yake dadewa a cikin kurkukun HKI, inda a lokacinda yake dan shekara 16 a duniya ya fada hannun yahudawan, sannan bayan ya share shekaru 30 a tsare, ya fi tare da taimakon kungiyar ta hizbullah inda ta yi musayarsa da wasu gawakin yahudawan da suke hannunta a shekara ta 2008.
A jiya asabar ne jirgin yakin HKI ta keta hurumin sararin samaniyar kasar Syria ta jefa makamai a kan anguwar Jurmana dake kudancin birnin Damascus inda mutane da dama suka rasa rayukansu wasu kuma suka ji rauni . daga cikin su samir qantar.
A cikin kasar Lebanon dai yan siyasa da malaman addini da dama suka yi All..wadai da kisan suka kuma mika ta’aziyarsu ga kungiyar Hizbullah.
Galib Qandeel shugaban binciken harshen larabci da kasa da kasa ya ce kungiyar hizbullah tana da hakkin maida martani kan kissan Samir qantar, sanna shahadarsa ya tabbatar mana cewa daurin da ya sha a cikin mafi yawan rayuwarsa bai sanya shi jada baya a kan manufarsa ta kasarsa da kuma Palasdinu sun sami enci daga hannun yahudawan da suke mamaye da su ba.
Walid Jomblat shugaban wata jam’iyyar siyasa gurguzu ta kasar Lebanon ya mika ta’aziyyarsa ga shugaban kungyar hizbullah ta kasar sayyeed Hassan nasarallah. Ya kuma ce Samir qantar kekyewar masala ne na mujahidin wanda baya daddara cikin gwagwarmaya da ya sa a gaba.
Kungiyoyin Palasdunin sun yi Al.. wadai da kisan Qantar sun kama bayyan cewa kungiyoyin masu gwagwarmaya sune da nasara a nan gaba.
Sami Abu zuhri kakakin Hamsa ya ce yahudawan sahyoyin suna bin dukkan majahidai inda suke don ganin bayansu. Kungiyar Fatah ta mahmod Abbas ta yi All..wadai da kisan qantar.
Sannan a nan JMI kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Husain Jabiri Ansari yay i All…wadai da kisan Samir qantar, a cikin kasar Syria daya ne daga cikin rashin mutunta dokokin kasa da kasa wanda HKI ta dade tana yi don kawo karshen kungiyoyi masu neman encin. Wannan kuma ya tabbatar da cewa HKI kasashe ta yan ta’adda wacce kuma take marawa yan ta’adda a kasashen duniya da dama don cimma mummunan manufofinta na mamayar kasashen musulmi da larabawa.

Ƙara sabon ra'ayi