Darul fatawa ta kasar Masar ta bayyana cewar gudanar da bukukuwan Darul Fatwa Ta Masar Ta Mayar Da Martani Ga Fatawar 'Yan Salafiya Kan Maulidin Annabi (S)
Maulidin haihuwar Manzon Allah (s) da kuma ci gaba da kwadaitar da hakan a matsayin wani aiki na halal sannan kuma daya daga cikin mafi kyawun ayyukan da suke samar da kusaci da Allah.
Darul fatawan ta bayyana hakan ne a matsayin mayar da martani ga wata fatawar da 'yan salafiyya suka fitar na rashin halalcin gudanar da maulidin Annabi da kuma kiran mutane da su guji halartar wajajen maulidin Annabi, inda Darul Fatawan ta bayyana cewar gudanar da irin wadannan tarurruka na murnar haihuwar Annabi da kuma kwadaitar da hakan ya halalta.
Har ila yau a cikin sanarwar nata, Darul Fatawan ta bayyana cewar bikin maulidin Annabi wata alama ce ta nuna farin ciki da ranar haihuwar Annabin Musulunci (s) da kuma kaunar Annabin.
Haka nan Darul Fatawar ta kara da cewa mafi yawa daga cikin malaman musulmi sun tafi kan halalcin gudanar da maulidin Annabi. Don haka suka yi watsi da fatawar malaman Salafiyyan.
Ƙara sabon ra'ayi