Akalla Mutane 6 Sun Rasu Sakamakon Harin Ta'addanci A Jihar Borno
Rahotanni daga Nijeriya sun bayyana cewar sojojin Nijeriya sun sanar da cewa wasu 'yan ta'adda sun kai wani hari a jihar Borno a yau din nan Laraba da yayi sanadiyyar mutuwar mutane 6 da raunana wasu da dama.
Kamfanin dillancin labaran Faransa ya bayyana cewar a cikin wata sanarwa da rundunar sojin Nijeriya ta fitar a yau din nan Laraba ta bayayana cewar wasu mutane 6 sun mutu kana wasu 24 kuma sun sami raunuka sakamakon harin ta'addancin da aka kai jihar Borno a yau din nan.
Sanarwar ta kara da cewa wasu mutane uku 'yan kungiyar Boko Haram ne suka kai harin ta'addancin ta hanyar tada wani bom a kusa da wata tasha a jihar ta Borno.
Sojojin dai sun sake jaddada aniyarsu ta ci gaba da fada da 'yan kungiyar Boko Haram din da suke ci gaba da kai hare-hare ta'addanci a bangarori daban-daban na Nijeriyan.
Ƙara sabon ra'ayi