Jiragen Yakin Rasha Sun Kai Farmaki Kan Sansanonin Yan ta'adda a kasar Syria
Gwamnatin kasar Rasha ta bayyana cewa sojojinta a kasar Syria sun kashe yan ta’adda 320 a hare haren
Gwamnatin kasar Rasha ta bayyana cewa sojojinta a kasar Syria sun kashe yan ta’adda 320 a hare haren da suka kaiwa sansanoninsu a cikin sa’oi 24 da suka gabata.
Kamfanin dillancin labaran AFP ya nakalto kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar yana fadar haka a jiya Laraba ya kuma kara da cewa , banda haka jiragen yakin kasar Rahsa daga sama daga kuma kan teku sun lalata tankunan yaki da motocin dakon albarkatun man fetur wadanda yan ta’addan suke kokarin fiddasu daga kasar zuwa kasar Turkiyya.
Labarin ya kara da cewa sojojin rasha a cikin kwanaki 70 da suka gabata sun lalata sansanonin yan ta’adda kimani dubu 8 a kasar Syria.
Ƙara sabon ra'ayi