Gwamnatocin Turkiya Da Isra'ila Na Shirin Farfado Da Alakarsu

Kafofin yada labaran Haramtacciyar kasar Isra’ila sun ce an gudanar da wata ganawa ta sirri a tsakanin shugaban kungiyar leken asiri ta Isra’ila Mossad, da kuma mataimakin ministan harkokin wajen kasar Turkiya a kasar Switzerland.

Tashar talabijin ta Channel 10 ta Isra’ila ta bayar da rahoton cewa, an gudanar da wannan tattaunawa ne a cikin sirri, kuma bangarorin biyu sun cimma matsaya kan batutuwa masu mihimmanci, da hakan ya hada da batun dawo da kyakkyawar alaka ta diplomasiyya a tsakaninsu, da kuma janye karar da Turkiya ta shigar a kan Isra’ila, dangane da harin da ta kai kan jirgin ruwan Turkiya na Marmar tare da kashe mutane a cikinsa da suke nufin isa Gaza.

 

Haka nan ita ma Turkiya ta yi alkawalin cewa za ta takura ayyukan kungiyar Hamas a cikin kasarta, yayin da Israila kuma za ta fara sayarwa Turkiya da Gas nan ba da jimawa ba.

 

Wannan mataki dai ya zo bayan da aka shiga takon saka tsakanin Turkuya da Rasha bayan harbor jirgin Rasha da Turkiya ta yi a kan iyakokin Syria, wanda hakan ya sa Rasha wadda take baiwa Turkiya mafi yawan iskar gas da take amfani da shi, ta kakaba wa Turkiya takunkumin cinikayya.

Ƙara sabon ra'ayi