Jaddadar Kwamitin Tsaro Kan Gudummawar Matasa Wajen Fada Da Tsaurin Ra'ayi A Duniya

A kwanakin baya ne kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya ya amince da wani kuduri da aka gabatar masa dangane da irin gagarumar rawar da matasa za su iya takawa wajen samar da sulhu da zaman lafiya da kuma fada da tsaurin ra'ayi da wuce gona da iri da ke yaduwa a duniya.

Yayin da yake magana kan hakan, kakakin babban sakataren Majalisar Dinkin Duniyan, Farhan Haq ya bayyana cewar dukkanin membobin kwamitin tsaron sun amince da wannan kudurin. Har ila yau shi ma a nasa bangaren, wakilin babban sakataren MDD na musamman kan harkokin matasa Ahmad Al-Handawi ya bayyana kudurin a matsayin wata gagarumar nasara wajen sauya irin tunanin da ake yi kan matasa da kuma amincewa da irin rawar da za su iya takawa wajen tabbatar da sulhu a duniya da kuma fada da tsaurin ra'ayi da wuce gona da iri da a halin yanzu yake yaduwa a duniya musamman a tsakanin matasa.

Amincewa da wannan kuduri da kwamitin tsaron MDD yayi ya zo ne a daidai lokacin da bai wuce kimanin makonni biyu ba kenan da Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya aike da wasikarsa ta biyu ga matasan Turai inda ya bayyana harin ta'addancin da aka kai kasar Faransa a matsayin wani lamari mai sosa rai. A cikin wasikar kai tsaye Jagoran yayi magana da matasan ne a matsayinsu na wadanda suka fada tarkon akidar wuce gona da iri da ta'addanci da kuma wasa da hankalin da wasu 'yan siyasa suke yi da su.

Tambayoyin da batutuwan da Jagoran ya gabatar da su cikin dukkanin wasikun nasa guda biyu ga matasan (wato ta farko da ya aike a watan Janairun 2014 da kuma wannan ta biyu da ya aike ta a watan Nuwamban wannan shekara ta 2015), wata dama ce ta gabatar da wani sabon tunani da za su iya share kofar isa ga mafita da magani na hakika na magance wannan babban bala'i da tsaurin ra'ayi da kuma ayyukan ta'addanci da suka addabi duniya.

Kamar wasikar tasa ta farko, a wannan wasika ta biyu ma Ayatullah Khamenei yayi magana ne kai tsaye da matasan Turai din don kuwa ko shakka babu matasa a matsayinsu na manyan gobe, matukar aka saita musu tunaninsu, to kuwa za a iya magance da dama daga cikin matsalolin da suka addabi duniya wadanda manyan 'yan siyasa da kuma amfani da karfi na soji suka gagara magance su.

Ko Shakka babu babbar hanyar fahimtar matsalar da ake fuskanta ita ce tunani dangane da tushen wannan matsalar. Don haka fahimtar hanyar magance matsalar tsaurin ra'ayi da tashin hankali da ya addabi duniya a halin yanzu ita ce tuntuni kan tushen tashin hankali da tsaurin ra'ayin wanda ba wai kawai sun ta'allaka da yankin Gabas ta tsakiya ba ne, face dai ana iya ganin misalan hakan da yawa a Turai da Amurka da Afirka, sannan kuma bai takaita kawai ga musulmi ba.

A hakikanin gaskiya irin al'adun kasashen Yammaci ta wani bangaren sun taimaka wajen haifar da irin wannan tsaurin ra'ayi da tashin hankali da ke yaduwa tsakanin matasa musamman na Turai din.

A don haka ne da dama suke ganin fitar da irin wannan kuduri da kwamitin tsaron yayi yana a matsayin share fagen samar da wani irin yunkuri na gano tushen wannan matsala ta ta'addanci da wuce gona da iri, to sai dai kuma abin da babu kokwanto cikinsa shi ne wajibcin fahimtar wannan matsala ta hakika da kuma gano cewa ta'addanci da tsaurin ra'ayi da wuce gona da iri wani bala'i ne da al'ummomin duniya suka yi tarayya cikinsa kamar yadda Jagoran yayi ishara da hakan cikin wasikar tasa, wanda wajibi ne a hada hannu waje guda wajen kawo karshensa.

Ƙara sabon ra'ayi