Gwamnatin Rasha Ta Yi Gargadi Kan Bullar Kungiyar Da'ish A Afganistan
A bayanin da ma’aikatar harkokin wajen kasar Rasha ta fitar yana dauke da gargadi kan yiyuwar bullar ayyukan ta’addancin kungiyar Da’ish a kasar Afganistan musamman bayan samun tabbacin cewa ‘yan kungiyar ta Da’ish sun samu damar kafa sansanoninsu a lardunan kasar guda hudu.
Bayanin ya kara da cewa; A halin yanzu haka ‘yan kungiyar ta Da’ish suna ci gaba da shirye-shiryen samun gidin zama a kasar ta Afganistan ne kafin shelanta kansu, kuma ga dukkan alamu nan da wata guda ne zasu sanar da samuwarsu a cikin kasar.
Har ya zuwa yanzu dai kungiyar Taliban mai fada da gwamnatin Afganistan bata shelanta goyon bayanta ga kungiyar Da’ish ba, kuma a gefe guda babu wani karin haske da ya fito daga mahukuntan kasar ta Afganistan kan wannan sanarwa ta gwamnatin Rasha.
Ƙara sabon ra'ayi