Majalisar Dinkin Duniya Ta Ce Rikicin Kasar Burundi Ya Lashe Rayukan Mutane Akalla 300
Majalisar Dinkin Duniya ta sanar da cewa; Dambaruwar siyasar kasar Burundi ta lashe rayukan mutane fiye da 300.
A rahoton da Kwamitin kolin kula da hakkokin bil-Adama na Majalisar Dinkin Duniya ya fitar a jiya Alhamis ya bayyana cewa; Tun bayan bullar rikicin siyasa a kasar Burundi a cikin watan Aprilun wannan shekara ta 2015 zuwa yanzu, akwai tabbacin mutane fiye da 300 uku ne suka rasa rayukansu.
Wakilin kwamitin kolin kula da hakkokin bil-Adama na Majalisar Dinkin Duniya a kasar ta Burundi Patrice Vahard ya bayyana cewar suna da tabbacin adadin mutanen da rikicin siyasar ya lashe rayukansu sun haura mutane 300 amma sun sanar da wannan adadin ne a matsayin adadin da dukkanin bangarorin siyasar kasar suka amince da shi.
Patrice Vahard ya kuma kara jaddada damuwarsa kan karin habakar tashe-tashen hankula a kasar musamman ganin yadda kungiyoyi masu adawa da gwamnatin Burundi suke kara yawaita tare da sabar makamai.
Rikicin siyasa a kasar ta Burundi ta kunno kai ne tun bayan matakin da shugaba Pierre Nkurunziza ya dauka na yin tazarce a kan karagar shugabancin kasar a wa’adi na uku duk da cewa kundin tsarin mulkin kasar ya haramta masa yin hakan.
Ƙara sabon ra'ayi