Sandararren Tunanin Wahabiyawa
Sandararren Tunanin Wahabiyawa
A kullum wahabiyawa ba sa rasa mummunan sandararren tunani kan sha’anin addini ko na rayuwar al’umma don haka ne ma suka addabi sauran musulmi da kafirtawa. Misali karami kan hakan da na so nuni das hi yadda wasu ‘yan izala da sauran salafawa suke ta kwakwazon cewa ‘yan shi’a suna sanya wa gawarsu akwati ko fulawa ko suna yi wa kabari ado. Su sun dauka al’adun saudiyya na jafa’I da wahabiyanci ya gadar wa mazhabarsu shi ne addini.
Baban misali a addini ba a kayyade wa abubuwa irin wadannan wata iyaka ba, kamar yaya za a dauki mamaci, a cikin me za a kaishi, da sauransu. Mafi girman misali zamu ga yadda ummul muminin zainab bintu Jahsh ta nuna wa sayyida Zahra (s) yadda ake kai gawa a cikin wani abu mai kamar akwati sai kuma a rufe saman tad a yadi don ka da mutane su gan ta, kamar yadda kiristoci suke yi a Habasha. Ita zainab ta ga haka ne yayin da suke rayuwa a Habasha. Sai kuma sayyida Zahra ta yi umarni idan ta mutu a yi mata hakan kuma haka aka yi.
Misalin yadda ake kera dirhami da yi masa tambari shi ma wani muhimmin lamari ne da zamu iya bayar da misali da shi wanda zamu ga yadda malaman musulmi hatta ma da imam Baqir (s) yana cikin wadanda suka bayar da shawarar hakan ga Hisham da lokacin Sarakunan Abbasawa ma.
Don haka wahabiyanci ba wani abu ba ne sai wani sandararren tunani da aka kafa cikin al’ummar musulmi domin rusa musulunci da shi. Kuma abin da salafawa wahabiyawan jihadi da ma wadanda ba na jiahdi ba suke yi a yau a duniya musulmi babban misali ne kan hakan.
Aliyyu A Abdullahi
Zainab Husain
Ƙara sabon ra'ayi