Kashe ‘yan Makaranta 29

Kashe ‘yan Makaranta 29

Salafawa Wahabiyawan Da’ish sun kashe kusan ‘yan mata 29 da mutanen gidan baki daya a garin Mousili na Iraqi da suka kama watannin baya saboda kawai sun yi bukin gama karatun kawarsu a gidan. Wannan shi ne ainihin Boko Haram a Iraki dab a su da wani hadafi sai neman gamawa da dukkan musulmi da kawar da iliminsu baki daya.

Babban hadafinsu bai wuce kasha musulmi da rusa tattalin arzikinsu da iliminsu da karatunsu ba. Su dai sun mamayi kasashen musulmi da sunan jihadin musulunci don bata sunan musulunci da rusa musulmi baki daya kamar yadda aka san hakan ga kungiyoyin salafawa wahabiyawan jihadi.

 Labarai daga Aliyyu A Abdullahi

 

Ƙara sabon ra'ayi