Jihadun Nikhah (Jihadin Aure)

Jihadun Nikhah (Jihadin Aure)
Fyade ga Maza da Mata da Sunan Musulunci a kasar Siriya
MAI KARATU KARANTA WANNAN HIRAR DA MUTANE DABAN-DABAN KA JI KAZAMIN AIKIN WAHABIYAWA/SALAFAWA A WANNAN DUNIYAR DA MUKE CIKI BA WAI MAFARKI BA, DAGA BAKIN MUTANEN SIRIYA. ALLAH YA TARWATSA ANIYARSU YA YI KACA-KACA DA SU, YA YAGALGALA SU.
Jihadin Aure wani fasikanci ne na wahabiyawa salafawa na yin fyade kan 'yan mata da kwanciya da su ta karfin tsiya bayan an sato su daga gidajensu da sunan biyan bukatun sha'awa don masu jihadi su sami karfin yin jihadinsu. Satar 'yan mata da matan mutane wani abu ne da wahabiyawa tun farko suka kware kansa, tayiwu wannan yana kasancewa sakamakon wahabiyawan sun halatta jini da dukiyar musulmi da mutunci da farjin matan musulmi bayan sun kafirta su. Lamarin bai tsaya nan ba har sai da ta kai ga yi wa samari fyade idan aka rasa mata da 'yan mata kuma ga masu jihadi suna bukatar jima'i.

LABARIN JIHADIN AURE (JIHADIN NIKAH)
Lamari ne mummuna abinkunya ga masu kafirta mutane daga wahabiyawan.
JIHADIN AURE KO YAKAR Allah !
WATA HIRA DA WASU MUTANE:
Na hadu da wani mutum mai sunan Basshar Iwaz, sai ya nemi in shiga cikin mayaka
Domin in dauki makami in yi yaki da gwamnati, na shiga cikin mayaka na karbi makami,
Daga nan sai na karbi hutu na koma, na shiga cikin jama'ar Saiful Islam da umarnin Basshar Iwaz wanda yake bin jama'ar Sugurus Shama.
A Jabhatun Nusra karkashin umarnin Basshar Ali, Basshar Iwaz, Abu Abdu, sai suka ce da ni: Kana da mata?.
Sai na ce: Ina da wacce na saka, kuma ina da biyu da nake ciyarwa, sai suka nemi in kawo daya daga cikin matana domin yin jihadin Aure.
Ya gaya mini: Kai dana wannan jihadin a kan tafarkin Allah ne kuma kai zaka shiga aljanna.
Wadannan mayakan da suke nan ba su da kowa, ba mata, ba komai, sai na yi wa matata Fatima waya ...,
(Sai matar ta ce:) Ya ce da ni! Fatima zo daki kaza da ke wurin lambu kaza, amma ka da ki zo da danki, sai ta ce: To. Sai na dora ni kan babur ya kai ne wani lambu ...,
Lokacin da na isa lambu.
Basshar Iwaz da ake ce masa Abu Abd sa na gan shi a zaune, shi mutum ne mai bulun idanuwa da dogon gemu da kwallai a ido
Sai ya ce da ni: Kina son ki yi tarayya a Jihadun Nikah? Sai na ce: Yaya fa? Ban san me ye jihadun nikah ba, wannan ne farkon lokacin da na ji wannan kalma a rayuwata.
Ina nufin kina son kwanciya da maza da yawa? Sai na ce: Yaya fa? Sai ya ce ki sadu da su nake nufi.
Sai na ce masa cikin izgili, me zai hana saboda idanuwanka.
Sai ya ce: 'Yata wannan jihadi ne a tafarkin Allah, kuma wadannan masu jihadin ba su da kowa a nan, sun bar matansu da 'ya'yansu baki daya.
Sai ya kawo shayi da koffi amma ban sha ba, sai na fahimci na fada cikin tarko ne.
Bayan na zauna rabin awa sai ban ga mijina ba, ya ba wa mijina dubu biyar.
(Mijin ya ce:) Sai na bar matata a wurin, na tafi na zauna har karfe sha daya na dare. (Matar ta ce): Sai shi kuma ya shigar da maza shida cikin dakin.
Ya daure mani hannaye, kuma ya yi mini wani mari mai zafin gaske, ya sanya ni kan gado.
Sai ya ce da ni: Ga maza shida nan a wurinki, dukkansu suna son su yi aure da ke, wannan kuwa fatawar sheikh ce da ya bayar.
Wannan jihadi ne a tafarkin Allah, dukkansu sun bar gidajensu, kuma suna yi miki kariya da ke da 'ya'yanki da kasarki, ka da ki yi tsammanin su 'yan ta'adda ne.
Sai na ce masa: A kan me? Sai ya mare ni, na yi shiru, na kasa magana. Sai ya sake ce mini, idan kika yi kalma daya to rayuwarki da danki ta gama yawo ke nan.
Na ce: Haka nan rayuwata ta kare da wannan zalunci, abin ya yi muni gare ni in yi shimfida tare da kai, gama da ni kawai.
Ya ce ba komai, sai ya fara yi mini fada, sai na yi shiru, sai ya bude idanuwana da hannayena, sai na ga mutane shida, ga mutane uku a waje.
Ya sanya mutane uku gurina, sai ya ce da dayan cikinsu kawo hannunka. Ya ce: Ka karba? Sai ya ce: Na karba. Sai ya ce: Na aura miki wanda ya wakilta ni.
Na aura muku bisa sunnar Allah da annabinsa, kuma ya karanta fatiha. Ya kwanta da ni awa biyu, sai kuma ya kawo wani mutumin daban.
Duk awa biyu ana kawo mutum daya har karfe sha daya na dare.
Sai ya fita da karfe goma sha daya ya gan ni cikin fushi, sai ya ce da ni: Fatima me ya faru ne na gan ki cikin fushi? Me ya same ki ne?.
Na ce masa: Kai mutum ne da ba ya tsoron Allah. Ban san me kuma zasu yi ba nan gaba, amma dai ya shiru bai bayar da amsa ba.
Sai na ce masa: Ka rabu da ni. Kai namiji ne da ba ka dace da ni ba, ni daga yanzu ba ta ka ba ce kuma ba na kaunarka sam.
Ni ba na son ka, ina son in rabu da kai, ba na son ka kuma.
Bayan kwanaki ishirin ne sai na yi wa mijina waya na ce masa, ina kike ne? Sai ya ce: Ina cikin gona da ke wuri kaza. Sai na ce ina son in zo wurinka.
Matata ta ce: Ina nan zuwa wurin bayan gonar nan ta Basshar Awaz.
Na je wurinsa.
Sai na ce wa Basshar Awaz Fatima tana son ta koma.
Sai lamarin ya sake maimaituwa, ya kawo mutane hudu ya ce dole ne ta zabi mutum daya.
Sai na ce: Kai Basshar. Sai ya ce: Dana wannan duk jihadi ne a tafarkin Allah, kuma kai zaka shiga aljanna, kuma wannan ba aikin haram ba ne, duk halal ne.
Sai na zabi mutum daya.
Wannan lamarin an daura shi bisa sunnar Allah da manzonsa.
Bayan rabin awa ne sai ya ba wa Khalid (mijin) Lira dubu biyar ya wuce, sai ya ce da ni: Zabi wani mutumin kuma, sai na zabi wani mutum mai suna Mu'utaza.
Dogo ne, kyakkyawa da dan gemu, ya aske gashin bakinsa, kuma akwai wani tabo a kumatunsa, sai ya kwanta da ni awa biyu.
Sannan sai ya sake ni ya ce: Ke sakakkiya ce, sakakkiya ce, sakakkiya ce. Na biyu ya shigo mai suna Ahmad ga shi da dogon gemu.
Kakkaura ne, kuma gajere, akwa ciwo a fuskarsa.
Duk dai awa biyu sheikh Khamis da Ali Salih da Basshar Awaz suna kulla wa wani aure da matata.
Kuma ana sakin ta, a sake daura mata aure da wani.
Bayan wadannan mutane biyu sai ya sake kawo wasu mutanen biyu ya ce: Wadannan biyun dole ne su yi su ma.
Ya ba ni Lira dubu biyar kimar kudin matata na kowanne mutum a cikinsu.
WATA HIRAR DA WASU MUTANEN:
Shekara goma sha uku ke nan da yin aure na amma ban taba samun kwanciyar rai ba, jikina babu hutu, na je kasuwar 'ya'yan itaciya sai na ga wani mutum mai suna Abuzu'aib.
Ya ce: Ina son in san ka, sai na ce to na yarda. Sai ya ce: Ni na dade ina kaunar ka.
Sai ya gayyace ni mu je gidansa, ni ma na tafi, farkon lokacin da na zo wurinsa sai na duba, sai na ga makamai goma na harbi.
Na ga wata tuta na ce wannan mene ne? Sai ya ce: Wannan na Jabhatun Nusra ne, kuma ni kwamandan Usudut Tauhid nake.
Sai na ce masa: Ni kam ina jin tsoron hakan. Ya ce: Ka da ka ji tsoron komai, kai kana tare da kwamandan wannan jama'ar ne, kuma ni ina kaunar ka.
Kuma yanzu ina son in kulla aure da ke. Sai na ce masa ina son in tafi ne a yau ba na jin dadi, zan zo bayan kwanaki uku ne.
Bayan kwanaki uku sai na zo wurinsa, na ce: Na yarda ka aure ni.
Sheikh Iyad I'iwijan ya kawo Abunazir ya daura mini aure, ya sanya hannaye na haka, kuma ya jefa mini wata tuta, ya karanta surar Fatiha, sheikh Iyad ya fita waje.
Bayan nan sai ya yi raka'a biyu, ya yi kwanciya da ni, sannan ya zauna kadan, sannan sai na tafi gidana, sai dai kowane lokaci ina zuwa wurinsa ne.
Duk sati nakan je sau daya, biyu, uku. Sai ya ce da ni: Gobe zan yi wata magana da ke.
Na ce me ye? Sai ya ce da ni: Kina so ki yi aiki tare da mu?
Na ce: To ni me zan yi kuwa? Sai ya ce: Ina son ki yi aiki tare da mu kamar yadda na aure ki a addini.
Ina son in daura miki aure da wasu. Sai na ce: Ni ban yarda ba. Kai kana kowanto na ne, ta haka ne kake son ka zo mini da wani abin kuma.
Sai ya ce: Zaki samu aljanna ne kai tsaye idan kika yi wannan aikin.
Sai na ce masa: Dole ne in yi tunani. Sai ya ce: Duk yadda kika so. Sai na zauna gunsa sannan sai na tafi gida, na yi tunani.
Na yi tunanin cewa kai tsaye zan shiga aljanna idan na yi aiki da shi, na ce; yanzu in yi aiki tare da shi kan makiya ke nan.
In kuma shiga aljanna ke nan. Sai na zo wurinsa na ce masa: Na yarda, ina son yin aiki tare da ku. Sai ya kawo wani mutumgun sheikh Iyad I'iwijan Abunazir.
Sai ya aura mini shi. Ya sanya hannayensa haka, ya karanta fatiha, ya kulla aurena da shi, ya ce masa:
Amma idan ka gama da ita zaka fita sai ka sake ta fa. Sai dai mutumin ya so ya kwanta da ni amma ni na ki yarda da hakan.
Bayan kusan rabin awa ne ko mintina arba'in da biyar sai ya kwanta da ni, kuma lokacin da zai fita sai Iyad ya sake ni, na huta rabin awa.
Sai kuma wani mutumin ya zo. Bayan na tafi bandaki ne sai wani mutum mai suna Ali ya daura mini aure da shi ya ce masa:
Duk lokacin da ka gama zaka fita waje sai ka sake ta, shi ma kuma kusan rabin awa ya kwanta da ni, sai ya fita waje, ni ma na tafi wanka.
Sai kuma ya kawo wani mutum mai suna Muhammad Husain ya shigo, ya kulla mini aure da shi, kamar dai yadda na kafinsa ya yi shi ma sai ya kwanta da ni kuma ya sake ni.
Bayan nan sai na fita daga wurinsa, yayin fitowa sai mijina ya gan ni, da na je gida na yi tsammanin mijina yana cikin bakin ciki ne da rashin jin dadi.
Sai na ce masa: Me ya faru ne Faisal? Sai ya ce: Babu komai. Sai na ce masa: Dole ne ka fada me ya faru ne kake cikin bakin ciki haka.
Sai ya ce: Ke me kike yi gun Abuziyab? Sai na ce: Ni ban kasance gun Abuziyab ba. Sai ya ce: Ka da ki yi mini karya, me kike yi gun Abuziyab?
Na ce: Ni da Abuziyab wani abu muka yi. Ya ce: Me ye? Sai na ce: Jihadun Nikah.
Ya ce: Me ya sa kika yi haka? Sai na ce: Na ga mijina bai damu ba, kuma ba ya gaya mini komai. Bayan wani lokaci sai na tafi gun Abuziyab.
Sai na yi masa sallama na zauna gun sa. Sai ya ce: Sheikh Iyad yana son ya shigo wurinki. Na ce: Ba yau ba, sai gobe. Na tafi gobe na dawo.
Na ce: Na yarda. Ya ce: To. Sheikh Iyad ya kulla auren kamar dai yadda suka yi a da, ya dora hannunsa kan juna, ya yi salla raka'a biyu.
Ya sake kwanciya da ni, ya kuma sake ni. Sheikh Iyad ya gama aikinsa ya fita waje, ni ma na fita daga wurin, amma dai a wurin mata da 'yan mata masu yawa ne.
Kuma mata da 'yan mata masu yawa ne a wurin na gani, na je wurin Abuziyab na ce: Me wadannan matan da 'yan matan su ke yi a wurinka, wannan yana nufin ke nan.
Kai kana yi mini isgili ne ko kuwa, me duk wadannan matan da 'yan matan masu yawa haka suke yi a wurinka da kake yin aure da shi aure?, ya ce: A'a ke mahaukaciya.
Wadannan matan da 'yan matan ba nawa ba ne, na samari ne, domin samari sun yi nesa da matansu.
Na ce: Haka ne!. sai dai wani tunani ya riga ya daure mini kai. Na ce masa: Zo mu zauna ina da magana da kai ne. Na ce: Wadannan 'yan matan da suke gun ka.
Yaya kuke nuna musu jihadin aure ne? sai ya ce: Sheikh mai bayar da fatawa ne ya bayar da fatawar yin hakan.
Mai fatawa Sheikh Iyad I'iwijan Abunazir ne ya bayar da fatawar ku yi hakan ku kwanta da wadannan 'yan matan!
Na ce: Sai dai akwai mamaki wadannan 'yan matan !
Ya ce: Kin dai fahimta sosai ko.
Na ce: Mata fa?
Ya ce: Ga mutum nawa!!!
Kafin lamarin Siriya da lokacin yaki da kafa Jabhatun Nusra suna amfani da wannan.
WATA HIRAR DA WASU MUTANEN:
Da farko na shiga cikin al'ka'ida ne, na kasance ina karatu a aji na goma a ilimin addini a masallacin limamin garin Bukman.
Akwai wani malami mai suna Abu Muhammad a masallacin malamina da yake zuwa daga Iraki kuma yana ba mu karatu na musamman na Al'ka'ida.
Da farko 'yan mata goma ne mu, sai dai daga baya 'yan mata da yawa suka shigo cikinmu, muka zama masu yawa, yawancin abin da muke yi.
Shi ne jihadin nikah (jihadin aure), kowane mutum daga cikin 'yan al'ka'ida yana kwanciya da mu.
Da farko ana amfani da ayoyin Kur'ani da suka jirkita ne, da wasu ruwayoyin annabi da aka yi wa jurwaye.
Kuma mu 'yan matan al'ka'ida an ba mu umarnin kwanciya da duk wani mutum daga al'ka'ida da kuma dan Jabhatun Nusra.
Suna ce mana wannan lamarin wajibi ne kan mu tun da mu 'yan al'ka'ida ne. Bayan farkon faruwar abin da yake faruwa a Siriya lokacin ina ba wa 'yan mata karatu ne.
Na kasance ina kwadaitar da su addini, ina ganin suna shiga masallaci ba tare da alwala ba, suna yin salla haka nan. Kuma suna karanta Kur'ani ba tare da alwala ba.
Na kasance ina aiki da al'ka'ida, ina kai musu makamai, ina hada musu tarayyar samari da 'yan mata.
Ina shigar da 'yan mata cikin kungiya, da farkon lokacin da Ahmad ya nemi yin auren jihadun nikah da ni, kuma wannan fatawar ta zama wajibi ne kanmu.
Cewa dole ne mu yi jihadun nikah da kowane mutum daga jabhatun nusra mu kwanta da shi, kuma dole ne mu rika kwanciya da abokan karatunmu da mutanen da suke wajen makaranta.
Babu 'yan Siriya da zamu yi jihadun Nikah da su, akwai mutane biyu daga Libiya, da wani daga Tunis, da wani daga Maroko, da wani daga Misira, da wani daga Turkiyya.
Wani daga faransa, Saudiyya, Katar, kuma dukkansu kowanne yana kwanciya da mu, kuma muna karbar kudi a wurinsa.
Idan akwai wani wanda ba ya daukar makami kuma ba ya zuwa yaki to ba ma kwantawa da shi, ko da kuwa yana bayar da kudi ga Jabhatun Nusra.
Duk wani wanda ya kwanta da mu sai ya dauki film din kwanciyar, ya yi mana gargadin cewa idan muka gaya wa wani mutum to zai yada wannan film din.
Suna daukar kwanciyar da mobile da kuma camera digital, don ka da mu ce wani abu game da lamarin, don haka ne duk wani wanda ya kwanta da mu sai a dauki film din kwanciyar.
Wasu suna kiyaye film din a cikin mobile, wasu kuwa a cikin labtab. Kuma na yi aiki da jama'ar sahabbai a sham, kuma ina kai musu makamai.
Ina tarayya da su a yaki fagen daga, ina kai musu motocin kayan bama-bamai.
Kowane sheihi da duk wani kwamanda yana maganar jihadun nikah.
Idan ya dora hannunsa kan budurwa ko wata mata, sai ya ce Allahu Akbar sau uku, to ta zama halal gare shi.
WATA HIRAR DA WASU MUTANEN:
Abin da na gani da idanuwana shi ne yadda sukan kiwaye mace mai kyawun gaske su yi mata kawanya sai su yi kabbara a kanta, sai su kwanta da ita.
A kungiyar Attauhid mai bin Jabhatun Nusra akwai wani abu da ya faru, da suka yanke kan wani malami, wani mutumin chechen ne ya yanke kansa.
Dalilin yanke kan wannan malamin shi ne; wannan mutumin chechen ne ya bi matar malamin wannan yankin, ya yi mata kabbara ya kuma kwanta da ita. Yayin da sheihin ya zo wurin matarsa.
Sai ya ga wannan dan chechen ya kwanta da matarsa. Sai sheihin ya ce masa: Me ya sa ka yi hakan? Sai dan chechen ya ce: Ni na yi kabbara ga matarka, kuma ta zama halal gare ni.
Sai shehin ya bar shi ya fita, ya je ya samu matar wannan dan chechen ya dora hannunsa kanta sau uku ya yi kabbara, daga nan kuma sai da shi da matar dan chechen suka kwanta !.
Dan chechen ya zo ya ce da sheihin me ya sa ka yi hakan? Sai shehin ya ce: Kai ka yi kabbara ga matata ka kwanta da ita, ni ma na yi kabbara ga matarka na kwanta da ita!. Sai dan chechen ya ce: Kai bai halatta gare ka yin haka ba.
Ni ya halatta in yi wa matarka kabbara, amma kai bai halatta ka yi wa matata kabbara ka kwanta da ita ba!. Sai sheihin ya ce: Halan ubangijin da muke bi ya bambanta da naka ubangijin ne !!!
[Balle hukuncin ubangijinka da namu ubangijin ya zama ya bambanta]
Daga nan ne fa sai dan chechen ya cire wuyan wannan sheihin, kuma ni na yi matukar tsorata kan wannan lamarin.
WATA HIRAR DA WASU MUTANEN:
Na ji tsoron cewa a yi wa matata kabbara. Kuma ta zama halal gare su! Kuma ta zama halal gare su!.
Wannan lamarin ya faru a Halab, wata yarinya ta zo tare da mu daga mutanen Halab! Sai wani bachechene ya ga yarinyar a kan hanya sai ya so ya yi mata kabbara !.
Amma kafin dan chechen sai babar yarinyar ta yi mata kabbara sau uku ta shelanta cewa 'yata ce, wannan 'yar'uwarka ce! Sun so su kwanta da ita awa daya ko biyu ne kawai !.
Hatta ma idan namiji ya yi musu maganar me ya sa suka kwanta da matarsa ! To shi ma namijin sai su yi masa kabbara su yi luwadi da shi !!!.
Su yi masa fyade da karfin tsiya, kuma suna ganin babu wata matsala kan wannan lamarin !.
Ni ban san me ya sa suka yi wasa da tunanin mutane haka ba, duk kuma wannan sunansa jihadi a tafarkin Allah ! wai ya zama babu wata matsala a yi ta aure kan aure kuma duk wannan cikin sauki haka. Haka na fada cikin wannan bala'in ni ma.
Duk wanda yake son shiga cikin Jaishul Hur babu wata matsala ! ko da kuwa dan shekaru bakwai ne babu wata matsala! Muhimmi kawai shi ne ya zama za a iya kwanciya da shi ko ita komai karancin shekarunsu !.
Har ma suna yi gasar rigen cewa duk wanda ya riga saura yin kabbara ga wata mata ko budurwa ko saurayi idan an rasa mata to wannan ya zama nasa na awa daya ko awa biyu, kuma ya zama halaliyarsa.
MASU FASSARA WANAN HIRAR;
A YUNUS IBRAHIM
A A ABDULLAHI
ADAMU MUHAMMAD

 

Ƙara sabon ra'ayi