Shi'awa da Shi'anci - 4
SHI'AWA DA SHI'ANCI
Jama'ar ja'afariyya imamiyya
1-Wannan jama'ar ita ce aka fi sani da Shi'a Imamiyya Ja'afariyya, Jama'a ce mai yawa a wannan zamani namu, kuma ana kaddara adadinisu da kusan kwata na yawan al'ummar musulmi gaba daya, kuma asalinsu a tarihi ya taso ne daga ranar saukar fadin Allah madaukaki a surar bayyina: wadannan da suka yi imani kuma da aiki na gari, wadannan su ne mafifitan al'umma .
Sai Manzo (s.a.w) ya dora hannunsa a kan kafadar Ali dan Abi Dalib (a.s) kuma sahabbai suna wajen, ya ce: Ya Ali kai da shi'arka ku ne mafifitan al'umma. (Ana iya duba misali: a tafirin dabari –jami'ul bayan- da durrul Mansur na suyudi bashafi'e, da tafsirul ma'ani na Alusi bagdadi bashafi'e game da tafsirin wannan aya).
Daga nan ne aka kira wannan al'umma da Shi'a wacce ake danganta ta zuwa ga imam Ja'afar Assadik (a.s) saboda suna bin fikihunsa (da ya zo daga manzon Allah da alayensa har zuwa kan Imam Ja'afar Sadik).
2-Ana samun wannan jama'a da yawa a kasashe kamar Iran da Irak, da Pakistan, da Afganistan, da Indiya, kuma sun yadu da yawa a kasashen Kogin farisa, da Turkiyya, da Siriya, da Labanon, da Rasha da kasashen da suka rabe daga gareta. Kuma suna yaduwa a kasashen turai kamar Ingila, da Jamane, da Paransa, da Amurka, da Yankin Afrika, da kasashen Asiya ta gabas, suna da masallatai da cibiyoyin ilimi da ilmantarwa da ta shafi lamarin zamantakewar al'umma.
3-Su jama'a ce daga jinsina daban-daban da luggogi, da launuka, kuma suna rayuwa tare da 'yan'uwansu sauran musulmi daga sauran jama'u na sauran mazhabobi cikin aminci da soyayya, da taimakekeniya a dukkan fagagen rayuwa da gaskiya da ikhlasi, dogaro da fadin Ubangiji madaukaki: Hakika muminai 'yan'uwan juna ne .
Da fadinsa: Ku yi taimakekeniya a kan biyayya da takawa . Da kuma riko da fadinsa mai girma (s.a.w): Musulmi hannu daya ne a kan waninsu . Da fadinsa: Muminai kamar jiki daya ne .
4-Suna da ayyuka muhimmai da suka yi a tarihi masu girma na kariya ga musulunci, da kuma al'ummar musulmi, kamar yadda sun yi dauloli da hukumomi da suka yi hidima don ci gaban musulunci, da kuma malamai masu ilimi da suka bayar da gudummuwa wajen wadatar da littattafan musulunci da wallafe-wallafe masu yawa da suka kai daruruwan dubunnai kanana da manya a fagagen tafsirin Kur'ani, Hadisi, Akida, Fikihu, Usul, Halaye, Rijal, Falsafa, Shiryarwa, Siyasa, Zamantakewa, Lugga, Magani, Adabi, Pizik, Kimiyya, Lissafi, Ilimin Falaki, da sauran ilimomi na rayuwa. Kuma suna da muhimmiyar rawar da suka taka ta asasi wajen assasa ilimomi daban-daban: (A duba, littattafan: Ta'asisus Shi'a li ulumil Islam, da zari'a ila tasanifis Shi'a na Aga buzurg mai mujalladi 29, da kashaful zunun na Afande, da mu'ujamul mu'allafin na Kahala, da A'ayanus Shi'a na sayyid muhsin amin amuli, da sauransu).
5-Sun yi imani da Allah daya makadaici wanda bai haifa ba, kuma ba a haife shi ba, kuma wani bai kasance tamka da tsara gareshi ba. Suna kore wa Allah jiki da jiha, da wuri, da zamani, da canjawa, da motsi, da hawa, da sauka, da dukkan abin da bai dace da Ubangiji madaukaki ba.
Kuma suna yin imani da cewa babu wani abin bauta sai shi, kuma hukunci da shar'antawa duka suna hannunsa ne shi kadai ba tare da waninsa ba, kuma shirka da dukkan nau'o'inta karama ce ko babba, ta boye ko ta sarari, duka zalunci ne mai girma kuma zunubi ne da ba a yafewa.
Kuma dukkan wannan sun dogara ne da hankali mai hujja da aka karfafe shi da littafin Allah mai girma, da Sunna madaukakiya.
Ba sa karbar hadisan isra'ilanci (wanda ya samo asali daga gurbatacciyar koyarwa ‘yan Attaura da Injila) ko na majusanci da suka dauka Allah yana da jiki, kuma suke kamanta shi da bayinsa.
Ko kuma suke danganta zalunci zuwa ga Allah madaukaki. Ko kuma suke danganta aikata mummuna zuwa ga annabawa tsarkaka ma'asumai.
6-Sun yi imani cewa Allah adali mai hikima, ya halicci halittarsa da adalci da hikima, bai yi halittar wani abu don wasa ba, sandararre ne, ko tsiro, dabba ne ko mutum, sama yake ko kasa, domin wasa ya koru ga Allah wanda yake mai dukkan kamala korarre daga dukkan tawaya da aibi.
Mun dauko daga Face Book: page; (Haidar Center Enlightenment)
MAWALLAFI; SHEIKH JA'AFARUL HADI
MAFASSARI; HAFIZ MUHAMMAD Sa'id
hfazah@yahoo.com
Masu tsarawa da kula da shafin:
Aliyyu A Abdullahi
Zainabu Husaini
Ƙara sabon ra'ayi