Shi'awa da Shi'anci - 3
SHI'AWA DA SHI'ANCI
Bukatar Sanayyar Juna
Ubangiji Madaukaki yana cewa: “…Muka sanya ku jama'u da kabilu domin ku san juna…”, Hujurat: 13.
Musulunci ya zo alhalin jama'u suna rarrabe masu kyamar juna, masu fada da yake-yake, amma sai ya gaugauta domin warware wannan ya mayar da sanayya mahallin kiyayya da kyama, ya sanya taimakekeniya mahallin jayayya da husuma, ya sanya sadarwa tsakanin juna a mahallin yankewa, wannan kuwa duk da albarkacin koyarwar musulunci ta Tauhidi da Kadaita Allah ne. Sai a sakamkon haka aka samu bayyanar wata al'umma mai girma da wayewa da ci gaba mai girma, kamar yadda ta kare al'ummunta daga zaluncin dukkan wani azzalumi mai danniya, wannan al'umma ta zamanto mai kwarjini da ban tsoro a idanun duk wani azzalumi mai dagawa.
Wannan kuwa duk bai samu ba sai da albarkacin hadin kai da sadarwa tsakanin jama'u wadanda suka taru karkashin inuwar musulunci guda daya, duk da kuwa nau'o'in jinsinsu, da sabanin ijtihadodinsu, da yawaitar kabilunsu da sabanin al'adunsu, don haduwa a asasi da asali da farillai da wajibai ya ishe su, don haka hadin kai karfi ne, amma rarraba rauni ce.
Al'amarin ya ci gaba da haka har sai da aka sake mayar da wannan soyayya ta koma kiyayya, fahimtar juna ta koma kyamar juna, sashensu suka kafirta sashe, aka yi doke-doke tsakanin juna.
Sai wannan girma da izza suka kawu daga cikinsu, azzalumai suka sake yi musu hawan kawara, suka kutsa cikin gidajensu kwararo-kwararo, suka daidaice, suka warwatse, aka wawashe arzikinsu, aka wulakanta huruminsu, aka keta mutuncinsu karkashin fajirai, suka rika yin kasa-kasa kullum, da rushewa da take bin su faduwa bayan faduwa.
Da shan kashi a hannu a Andulus, da Bukhara, da Samarkand, da Daskand, da Bagdad, a da can, da kuma a yau a Falasdin da Afganistan.
Idan ta yi kira ba a amsa mata, idan ta nemi taimkao ba a taimaka mata, yaya kuwa haka ba zata faru ba alhalin cutarta wani abu ne daban, maganinta wani abu daban ake ba ta.
Alhalin Allah ba zai yarda ba, sai dai al'amura su tafi daidai gwargwadon sababinsu, kuma karshen wannan al'umma ba zai gyaru ba sai da abin da farkonta ya gyaru da shi.
A yau da muke ganin al'umma tana cikin mafi munin harin makiya a kan samuwarta da akidarta, kuma hadin kanta yana cikin mafi munin harin makiya, ta hanyar samar da matsala a rayuwarta ta addini da mazhaba da ijtihadi, kuma ga wannan harin yana kusan kai wa ga gaci. Shin ba yana kan ita al'ummar ba ta yi kokarin ganin hada sawunta da karfafa alakarta.
Duk da kuwa nau'in rarraba ta mazhabobi da take da ita, amma ta yi tarayya a littafi da Sunna a matsayin madogara, kuma ta yi tarayya a tauhidi, da annabta, da imani da lahira, da salla, da azumi, da hajji, da zakka, da jihadi, da halal, da haram, da kuma son ahlin gidan Annabi (s.a.w) da kuma kin makiyansu, duk da wasu sun fi wasu.
Sassabawar tana kasancewa ne kamar sassabawar 'ya'yan yatsu na hannu daya da dukkaninsu suna tukewa ne zuwa ga gaba daya duk da kuwa tsakaninsu sun sassaba a tsayi da fadi da shakalin kira, wannan al'umma kamar gabobin jiki ne da suka sassaba amma dukkaninsu sun yi tarayya wajen tafiyar da jiki domin hada samuwar dan Adam ta wata fuska tare da kuwa sabanin kirarsu.
Kuma kamanta wannan al'umma da hannu daya ko kuma jiki daya yana nuni ne zuwa ga wannan lamarin.
Tun da can malamai ma'abota mazhabobi mabambanta sun kasance suna rayuwa da juna ba tare da wata jayayya ko taho mu gama ba, sau da yawa sukan yi taimakekeniya tsakaninsu, har ma wani ya yi sharhin littafin wani na fikihu ne ko na akida, kuma daliban wasu suka yi karatu wajen wasu, kuma wasu su karfafi ra'ayin wasu, wasu kuma su ba wa wasu izinin ruwaya ga wasu, wasu kuma suna bayar da izinin ruwaitowa daga littafin mazhabinsa da jama'arsa ga wasu.
Kuma suka yi salla bayan juna, suka yi kyakkyawar sheda ga juna, suka yarda da juna, kuma suna rayuwa tare waje daya, har ma ta bayyana cewa kamar babu wani sabani tsakaninsu, duk da kuwa wani lokaci a kan samu raddi na ladabi tsakaninsu, raddi na ilimi da dalili.
Da yawa aka samu dalilai na tarihi mai yawa game da wannan lamari da taimakekeniya mai zurfi tsakaninsu, kuma malaman musulunci sun cika koyarwarsa da kayan tarihi na rubuce-rubuce, kamar yadda da wannan aiki nasu suka bayar da kyakkyawan misali mai girma game da 'yancin mazhabanci, hada da cewa sun iya janyo hankalin duniya zuwa ga himmantuwa da su, kuma suka kiyaye girmansu.
Mu sani ba wani abu ne mai wahala ba malaman wannan al'umma su hadu cikin sauki da nutsuwa su tattauna da ikhlasi da gaskiyar niyya game da abin da aka sassaba a cikinsa da kuma sanin dalilan kowace al'umma da kuma hujjar da take da ita.
Kamar yadda yana da kyau kuma abu ne na hankali kowace al'umma ko jama'a ta bijiro da akidunta, da matsayin ta na tunani da fikihu a cikin 'yanci a fili, domin rashin ingancin abin da ake jifanta na tuhumomi da shubuhohi ya bayyana a fili, kuma kowa ya san bambance-bambancen da yake tsakaninsa da waninsa, kuma su san cewa abin da ya hada kan musulmi ya fi abin da yake rarraba su yawa.
Wannan dan littafi mataki ne zuwa ga kai wa ga wannan gaci, kuma domin gaskiya ta bayyana ta fito a fili kowa ya san ta kamar yadda take, Allah ya sa mu dace.
Mun dauko daga Face Book: page; (Haidar Center Enlightenment)
MAWALLAFI; SHEIKH JA'AFARUL HADI
MAFASSARI; HAFIZ MUHAMMAD Sa'id
hfazah@yahoo.com
Masu tsarawa da kula da shafin:
Aliyyu A Abdullahi
Zainabu Husaini
Ƙara sabon ra'ayi