Rayuwar Iyali a Musulunci

Rayuwar Iyali

Aure alaka ce mai karfi tsakanin jinsin namiji da mace, kuma tsari ne da rayuwar dan'adam ta ginu a kansa, babu bambanci tsakanin mutumin zamanin farko da na wannan zamanin, ko mutumin gabas da na yamma.
Addinin Allah tun daga annabawan farko har na karshe sun ba wannan lamarin muhimmanci, sun shata wa kowane jinsi iyakokinsa bisa tsari mai kayatarwa da zai kai ga tausayi da jin kai da taimakekeniya tsakanin wannan jinsin guda biyu domin samun alakar halas da ci gaban samuwar dan'adam.
Tun farko idan za a farar da alaka tsanin namiji da mace a matakin farko ana sanya hankali ne domin rayuwa ta yi karfi da inganci, amma bayan an shiga fagen rayuwar tare wato bayan aure, to a lokacin kuma ana son yin alakar soyayya ne. Don haka wadanda suke fara rayuwarsu da soyayya suka yi wurgi da hankali to ba zasu ji dadin rayuwarsu ba lokacin da suka shiga fagen rayuwar aure, don haka hankali ne matakin farko sai soyayya ta biyo baya. Masu juya lamarin su fara da soyayya sannan kuma daga baya su ce zasu sanya hankali a rayuwarsu zasu samu cewa lokaci ya kure masu ba zasu iya ba.
Wannan ne ake nufi da cewar masu fara rayuwa bisa dogaro da hankali to zasu iya ci gaba da rayuwa bisa soyayya, amma wadanda suke fara rayuwa bisa soyayya to ba zasu iya ci gaba da rayuwa bisa hankali ba. Idan rayuwar ma'aurata ta fara da tsari da hankali da tunani mai kyau to zata kai su ga cin nasara da samun nutsuwar rayuwa, al'ummar da ta doru kan wannan tunanin zata samu rayuwar iyalinta cikin annashuwa da nutsuwar rai da jin dadin rayuwar tare. Al'ummar da ta saba wa wannan lamarin zata fuskanci rayuwa mai dacin gaske.
Kuma tun da tsarin nan yana bukatar wanda ba shi da wata maslaha a cikinsa kuma ya san halittar mutum da bukatunsa, don haka da bukatar koma wa mahaliccin mutum don sanin takamaimai me ya dace da shi da rayuwarsa a daidakunsa ko a al'ummance. Wannan lamarin ne ya sanya muke jin kiraye-kiraye a kasashen yammacin duniya kan a koma wa addinan Allah cikin abin da ya shafi tsarin rayuwar iyali don samun nutsuwa da daidaito a ciki.
Idan muka duba Musulunci zamu ga yadda ya ba wa gina iyali da rayuwar aure muhimmancin gaske don karfafa matakin farko na gina al'umma, sai ya sanya wasu ladabobi, da ka'idoji, da sharadodi masu kiyaye wa kowane bangare yanayin halittarsa ta yadda babu wani bangare da ya dora wa wani abu da ba zai iya yin sa ba, tare da kiyaye alakar kauna da so da tausaya wa juna, da kuma karfafa alakarsu ta yadda zasu kasance tamkar jiki da rai, da kare su daga tozarta da bin son rai mai lalata rayuwarsu.
Sai ya kalli rayuwarsu tun kafin su yi aure, da lokacin yin aure kafin haihuwa, da bayan haihuwa, da bayan aure ma, ya sanya wa kowace marhala dokar da ta dace da ita, ya kawo dokokin alaka tsakanin daidaikun mutane da suke cikin iyali daya. Mu a nan zamu so kawo muku bayanai ne masu muhimmanci kan wadannan lamuran da suka hada zabar abokin/abokiyar rayuwa, yadda ake gina rayuwar iyali, hakkokin iyali, sabani tsakanin iyali da hanyar magance shi, alakar da take tsakanin iyali da mutanen da suke kusa da su, alakar da take tsakanin jinsin namiji da mace, da wani abu da ya shafi hukuncin muharramai (wadanda aka haramta aurensu).

GINA IYALI
Iyali a nan muna nufin mutanen gida daya masu damfaruwa da juna da kusancin jini, nasaba, auratayya, wato su ne wadanda suke da alakar gina zuriya da take kunsar miji, mata, da 'ya'yansu, wani lokaci tana hada uwa, uba, kaka, jika, 'yan'uwa, surukai, da sauran makusanta a gida daya . Yin aure wani abu ne da yake mustahabbi a shari'a kuma yana da muhimmanci mai girma domin shi ne hanyar hayayyafar iyali da kiyaye cigaban samuwar dan'adam, don haka ne sai mustahabbancinsa ya zama mai karfi sosai.
Aure shi ne hanyar samar da alaka da sabawa da soyayya da shakuwa da juna, da taimakon al'umma kan kamewa daga fasadi, da kawar mata matsalar tunani da rashin nutsuwar rai, da kawar mata da bala'in fasadi, don haka ne sai aure ya kasance wani mustahbbai mai karfi kuma sunnar annabin rahama (s.a.w) da ya kwadaitar. Hatta da bayi da wancan lokacin akwaisu Musulunci ya yi musu hukunci daya kan wannan lamarin a matsayinsu na mutane yayin da yake cewa: "Ku aurar da bayi daga cikinku da salihai daga bayinku maza da mata, idan sun kasance matalauta to da sannu Allah zai wadatar da su daga falalarsa, kuma Allah mai yalwatarwa masani ne" .
Ruwayoyi masu yawa ne suka zo suna kwadaitar da yin aure, kuma shi ne babbar kariya daga duk wani rashin nutsuwar rai da hankali, da kare mutum daga fadawa munanan halaye da sabo. Sai ya sanya mutum ya zama mai iyakantuwa da hankali da watsar da son rai da sha'awa da suke yi masa dabaibayi suke shagaltar da shi da dauke masa hankai daga matsayinsa na rayuwa.  Manzon Allah (s.a.w) yana cewa: "Wanda ya so sunnata, to aure yana daga sunnata" . Da fadinsa: "Me yake hana mutum yin iyali ne, ta yiwu Allah ya arzuta shi da 'ya'ya da zasu cika duniya da fadin La'ilaha illal-Lah" . Da fadinsa: "Wanda ya yi aure ya kare rabin addininsa, to sai ya ji tsoron Allah a cikin sauran rabi" . Da fadinsa: "Raka'a biyu da mai aure yake yi, ta fi raka'a saba'in da maras aure yake yi" .
Muhimmancin da aure yake da shi ne ya sanya shi matakin daraja ta biyu bayan Musulunci; babu wani abu da ya fi zama ni'ima bayan Musulunci irin matar da idan mijinta ya kalle ta sai ta faranta masa rai, idan ya umarce ta sai ta bi shi, idan ba ya nan sai ta kare masa kanta da dukiyarsa. Munin gwagwarci ne ya sanya Musulunci ya karhanta shi domin yana kai wa zuwa ga halaye munana da sanya mutum mai matsalolin fushi da kuncin rayuwa, da jefar da bukatun asasi na sha'awa, ko dai ta hanyar yakar su, ko kuma ta hanyar jefa rai cikin ayyukan fasadi masu hadari.
Wasu mutane suna kin yin aure saboda tsoron talauci, sai dai tsoron talauci ya saba da talauci, idan mutum ya ki yin aure saboda yana da talauci wannan yana da uzuri kuma shari'a ta ba shi shawarar yin azumi. Wasu kuwa suna iya auren amma suna tsoron ka da su yi aure abin da suke rayuwa da shi ya yi musu karanci, tare da cewa suna da sana'a da ta dace da halin yanayinsu da matsayinsu gwargwadon yadda ya dace da rayuwarsu, to irin wadannan mutanen ne shari'a ta soke su. Manzon Allah (s.a.w) yana cewa: " Duk wanda ya bar yin aure don tsoron talauci to hakika ya munana wa Allah zato" .
Bincike ya tabbatar da cewa mafi munin mutane karkacewa daga hanya ta gari su ne wadanda suke gwagware, domin mai aure yana da abin da ya yi masa iyakar da yakan samu karancin tunanin saba wa sha'awarsa musamman don kare mutuncin matarsa, iyalinsa, 'ya'yansa da danginsa, sai wannan lamarin ya sanya shi ya fi kusa da nisantar alfahasha, hada da cewa yana da inda yake iyakance shi duk lokacin da sha'awa ta dame shi.
Munin gwagwarci ne ya sanya Musulunci ya yi wasiyya ga wadanda ba zasu iya yin aure ba da su karfafi yin azumi . Yin azumi wata garkuwa ce da take iya kashe fushin sha'awar da take addabar su. Da azumi ne saurayi zai iya rage karfin sha'awar da take addabarsa ya rage mata tasirin bacin rai, da damuwar rai da bakin cikinta da yake iya bujuro masa sakamakon rashin aure ba tare da ya yaki sha'awarsa ko ya fada cikin fasadi da lalacewar halaye ba. Hada da cewa mazhabar da ta yarda da auren mutu'a ta sanya shi daya daga cikin hanyoyin da zasu kawar da fasadi cikin al'umma. Yayin da wasu mazhabobin suka karhanta ko suka haramta saboda ittifakin da aka samu cewa sarkin musulmi Umar dan Khaddabi ya haramta shi.
Bayan mustahabbantar da aure sai Musulunci ya zarce wannan marhalar ya kwadaitar da mutane masu yalwa da wadata ko gwamnati da su taimaka wurin aurar da gwagware, zaurawa, 'yan mata, da samari.  Wanda ma kuma ba shi da wannan ikon yin haka to ya taimaka wurin hada aure idan ya samu dama. Manzon Allah (s.a.w) yana cewa: "Wanda ya yi kokari wurin hada aure tsakanin muminai biyu har ya hada tsakaninsu to Allah zai aura masa hurul'in dubu daya" . Kuma yana cewa: "Mutane Uku zasu shiga inuwar al'arshi ranar kiyama ranar da babu wata inuwa sai inuwarsa: Mutumin da ya aurar da dan'uwansa musulmi, ko ya yi masa hidima, ko ya boye masa sirrinsa" .

Hafiz Muhammad Sa'id
hfazah@yahoo.com
Haidar Center for Islamic Propagation (HAIDARCIP)
Text Only or ; 1-WhatsApp 2-Tango 3-Viber (+234 803 215 6884)
Mun dauko daga facebook; (Haidar Center Enlightenment)

Ƙara sabon ra'ayi