Rayuwar Aure
Rayuwar Aure
Mafi muhimmancin lokacin mutum a rayuwarsa shi ne lokacin da ya samu kansa yana son kafa iyali da shiga cikin rayuwar iyali, a nan ne saurayi ko budurwa zasu shata wa kansu rayuwar da zasu zaba wacce zata yi musu tasiri a rayuwarsu har mutuwarsu, a nan ne muhimmancin wannan lokacin zai fito a fili, don haka ne sanya hankali yake da muhimmanci a wannan marhalar.
A wannan marhalar ce saurayi ko budurwa zasu zaba wa kawukansu uba ko uwar 'ya'yansu, don haka marhala ce da take bukatar dubara da zurfafa tunani da hankali. Idan mun lura sosai zamu ga Musulunci ya sanya wa yaro da yarinya budurwa waliyyi a wannan marhalar domin amfani da hankalinsu wurin zaba wa yara abokan zamansu. Don haka ne aure ya zama karkashin izinin yara da iyayensu duka biyu, wannan kuwa domin a hada son yara ga abin da suka zaba wa kansu, da kuma hankalin manya mai lura da abin da zai zama mai amfani ga yara a wannan marhalar.
Sanya hankalin manya a wannan marhala zai sanya yara su sami zabi mai cika amfani da yake kunshe da darussar rayuwa da manya suka samu a tsawon shekarunsu. Idan manya suka sanya hanakli a nan zasu yi kokarin ganin sun kauce wa irin kuskuren da suka yi a nasu zabin, domin ka da su sanya 'ya'yansu cikin irin nadamar da suka samu kanta, ko kuma kauce wa nadamar da suka ga wasu sun fada cikinta. Irin wadannan darussa sabon jini budurwa ko saurayi ba su san su ba domin yanzu idanuwansu suka fara bude wa lamurran duniya da rayuwa. Don haka amfani da hankalin manya a nan zai sanya saurayi da budurwa su samu amfani daga wadannan darussan a rayuwarsu kamar dai sun yi tsawon rayuwar manyan.
A farkon rayuwa saurayi da budurwa suna bukatar abokin zama da zai taya su farin ciki da bakin ciki duka, su taimaka wa juna a komai, don komai. Gina rayuwar iyali yana kama da ginin gida ne da yake bukatar fondeshan mai karfi da asasi mai kyau ta yadda idan aka yi wannan ginin ba zai rushe ta kasansa ba, kuma bangonsa ba zai fara burbushewa ba, sannan rufin kwanonsa ba zai fara fara yowon ruwa ba, idan kuwa ya fara da irin haka, to nan da nan da wuri zai rushe.
Hadafin Aure
Rashin sanin hadafin aure shi ne mafi girman matsalar da ta baibaye lamarin aure, misali wasu 'yan matan suna ganin an aurar da su ne don an gaji da su, idan kuwa budurwa ta sanya wannan a ranta to ba zamu sami wani kyakkyawan misali a rayuwar aurenta ba. Wasu kuwa suna yin aure ne saboda suna ganin lokaci ya yi da zasu samu biyan bukatar sha'awarsu, ko kuma suna da wani buri na matsayi ko dukiya da suke son samu idan sun yi auren.
Wasu kuwa suna ganin aure wata wahala ce da mutum yake yi don dai kawai ya zama dole ne a rayuwa, amma babu komai a cikinsa sai wahala da dawainiya kawai. Yayin da wasu suna yin aure ne don suna ganin sa a matsayin hanyar kawar da wata damuwa ko bakin ciki da yake damunsu. Sai dai mu a nan zamu yi nuni da wasu daga cikinsu da zamu yi nuni da su kamar haka:
1- Nutsuwar Rai
Sanin hadafin aure yana da muhimmanci wurin shata rayuwar da ma'aurata ya kamata su doru a kanta, Kur'ani mai girma ya kawo muhimmin lamarin samun nutsuwa da fadinsa "... ya sanya kauna da tausayi a tsakaninsu ... domin samun nutsuwa wurinta...", ke nan samun nutsuwar rai ya zama shi ne asasin hadafin farko na yin aure.
Idan mutum bai samu nutsuwar rai ba to zai daidaice ya rasa makamar rayuwa baki daya, babu wani abu a rayuwa da zai yi masa dadi, kasuwancinsa, karatunsa, rayuwarsa, lamarinsa, baki daya zasu sukurkuce. Da wannan ne zamu fahimci cewa lamarin samun nutsuwar rai shi ne asasin farko na hadafin yin aure.
Idan mutum ya balaga yana samun canji a rayuwarsa a jiki da rai da fikira kuma wadannan canje-canjen suna bukatar sabuwar rayuwa ta hanyar aure domin isuwa zuwa ga hadafinsu. A wannan marhalar mutum ba shi da wata mafita sai amsa wa wannan bukatun nasa, idan kuwa ya ki to zai fuskanci rashin nutsuwar rai da zai damu rayuwarsa. Lallai samun nutsuwar rai, da jiki, da tunani, shi ne mafi girman hadafin yin aure. Kuma da wannan ne muhimmancin kiyaye wannan nutsuwar bayan aure zai bayyana, kuma ya kamata ga ma'aurata su yi matukar kokarin ganin sun kiyaye wannan nutsuwar rai bayan aure ta hanyar kiyaye kauna da soyayya da tausaya wa juna da abin da zai karfafa hakan.
2- Neman Kamala: Shi ne lamari na biyu da yake shata mana hadafin aure, idan mutum ya kai shekarun balaga yana fara jin tawaya idan bai kafa nasa iyalin ba, da ya yi aure zai fara jin ya samu kamala, kuma yana samun haihuwar farko sai ya ji kamalar ta karu, daga nan ne sai alakar ma'aurata ta sake samun wani karfi kuma ta dauki wani salo na kusanci da babu shi kafin haihuwa.
3- Kariyar Addini: Tana daga cikin baban hadafin yin aure kamar yadda wasu ruwayoyi suka yi ishara da hakan, idan mutum ya yi aure to zai samu kariya daga ribatar shedan a rabin addininsa. Da yin aure ne ake samun kariya daga ribatar shedan da farautarsa. Idan mutum ya samu kariya ta wannan bangaren sai ya kiyaye sauran bangarorin kamar ha'inci, karya, da zina. Auren da bai sanya mutum ya kare kansa daga haram ba to ba shi da kalama, auren da bai samar da nutsuwar rai da kamewa ba, aure ne tauyayye.
4- Yaduwar Mutum: Ci gaban yaduwar dan'adam a duniya yana kasancewa ne ta hanyar aure a matsayin hanyar da ubangiji madaukaki ya yardar wa mutum ita, kuma samun 'ya'ya shi ne natijar aure. Aure ba kawai biyan bukatar sha'awar rai ba ne yana da wata ma'ana mai daraja ta samar da jinsin dan'adam da kare shi daga karewa. Idan jinsin dan'adam ya kawu daga duniya to babu wata kima da zata rage mata.
Ci gaban yaduwar mutane a duniya ta hanyar aure wani abu ne da yake tilas a kan dan'adam, idan suka nisanci yin aure suka nisanci jinsin juna da zai samar da wannan ci gaban, to babu wata kima da zata rage wa mutum, kuma fushin Allah madaukaki zai sauka kan al'umma ke nan. Don haka yana da muhimmanci mu san cewa yin aure zartar da umarnin Allah na yada samuwar mutum a duniya ne, ba wani abu ne na neman kudi ko matsayi ko neman sha'awa ba.
Hafiz Muhammad Sa'id
hfazah@yahoo.com
Haidar Center for Islamic Propagation (HAIDARCIP)
Text Only or ; 1-WhatsApp 2-Tango 3-Viber (+234 803 215 6884)

Normal
0
false
false
false
EN-US
X-NONE
FA
/* Style Definitions */
table.MsoNormalTable
{mso-style-name:"Table Normal";
mso-tstyle-rowband-size:0;
mso-tstyle-colband-size:0;
mso-style-noshow:yes;
mso-style-priority:99;
mso-style-qformat:yes;
mso-style-parent:"";
mso-padding-alt:0cm 5.4pt 0cm 5.4pt;
mso-para-margin-top:0cm;
mso-para-margin-right:0cm;
mso-para-margin-bottom:10.0pt;
mso-para-margin-left:0cm;
line-height:115%;
mso-pagination:widow-orphan;
font-size:11.0pt;
font-family:"Calibri","sans-serif";
mso-ascii-font-family:Calibri;
mso-ascii-theme-font:minor-latin;
mso-hansi-font-family:Calibri;
mso-hansi-theme-font:minor-latin;
mso-bidi-font-family:Arial;
mso-bidi-theme-font:minor-bidi;}
Ƙara sabon ra'ayi