Wasiyyar Imam Ali ga Hasan

Wasiyyar Imam Ali ga Hasan

Tarbiyyar Yara

Wasiyyar Amirul Muminina Ali (A.S) Ga 'Ya'yansa Imam Hasan da Husain (A.S) a hanyarsa Ta Dawowa Daga Yakin Siffin

Wannan nasiha ta fito ne daga mahaifin da ba da jimawa ba zai bar duniya, wanda ya gano wahalhalu na rayuwa, wanda ya tsufa a (duniya), wanda ya ba da kansa ga bala'oin zamani, wanda ya fahimci sharrin duniya, wanda yake rayuwa a wajen rayuwar matattu kana kuma wanda zai bar duniya nan ba da jimawa ba; zuwa ga dansa wanda yake burin abin da ba za'a kai gare shi ba, wanda yake tafiya akan tafarkin wadanda suka mutu, wanda ya kasance wahalhalu sun shafe shi, wanda yake cikin damuwa ta wannan zamani, wanda kuma ya kasance hadafi na cututtuka, bawan duniya (wanda fadi tashinta suka dabaibaye shi), attajirin yaudarar duniya, wanda ke da bashin burace-burace, fursunan mutuwa, ma'abucin damuwa, makwabcin bakin ciki, wanda sha'auce-sha'auce suka galabce shi, sannan kuma wanda ya kasance halifan matattu. Bayan haka (ya kamata ka gane cewa) daga abubuwan da na koya daga irin juya bayan da duniya ta min(2) , irin fuskanta ta da lokaci yake yi da kuma kusanto ni da lahira take yi, ya isa ya nesantar da ni daga tunanin kowa in ba kaina ba da kuma kula da wani abu in ba nawa ba. To amma lokacin da na kebance kaina da damuwata, na bar damuwar mutane, sai ra'ayina ya kare ni daga soyace-soyacen zuciyata, sannan kuma ya fayyace min al'amurrana, kana kuma ya sanya ni ba da muhimmanci da babu wasa a ciki, sannan da kuma gaskiya wacce babu karya cikinta. A nan na same ka a matsayin wani sashi na jikina, kai na ma same ka a matsayin dukkan jikina, ta yadda idan har da wani abu zai same ka, to zan ji tamkar ya same ni ne, kana kuma idan da mutuwa za ta riske ka, to tamkar ta riske ni ne. sannan kuma al'amurranka suna da muhimmanci a gare ni, kamar yadda nawa suke. Don haka ne na rubuta maka wannan wasika don ta kasance abin taimako gare ka, shin ina tare da kai ne ko kuma bayan raina.

 

 

Abubuwan Da ke Raya Zuciya Ya dana, ina maka wasicci da tsoron Allah da kuma kiyaye umurninSa da cika zuciyarka da ambatonSa da kuma riko da igiyarSa. Wace alaka ce ta fi karfi a kan alakar da take tsakaninka da Ubangijinka, matukar ka yi riko da ita. Ka raya zuciyarka da wa'azi, ka kashe ta kuma da nuna halin ko in kula, ka karfafa ta da karfa-feffen imani da yakini, ka haskaka ta da hikima, ka kaskantar da ita ta hanyar tuna mutuwa, ka tabbatar mata da cewa ita mai gushewa ce, ka fahimtar da ita bala'oin duniya, ka gargade ta da karfin zamani da kuma tsananin canje-canjen darare da ranaku, ka bijiro mata da labaran al'ummomin da suka gabata, ka tunasar da ita abubuwan da suka faru ga wadanda suka gabace ka, ka tafi cikin garuruwa da kuma abubuwan da suka bari, sannan ka yi dubi cikin abubuwan da suka aikata da kuma wadanda suka guje musu, da inda suka je da kuma inda suka tsaya! Lalle za ka ga cewa sun guji masoya (na nan gidan duniya), sannan kuma sun kasance cikin kadaitaka (a cikin kabari). Nan ba da jimawa ba kai ma za ka zama kamar daya daga cikinsu(3). Don haka, ka shirya wajen da za ka zauna, sannan kuma kada ka sayar da lahirarka da duniyarka. Ka nesanci magana kan abin da ba ka sani ba da kuma abin da bai shafe ka ba. Ka nesanci bin hanyar (tafarki) da kake tsoron za ka bace, don kuwa nesantar abin da kake tsoron zai batar da kai shi ya fi a kan shiga cikin hatsari. Ka umurci (mutane) da ayyukan alheri, sai ka zamanto daga cikin masu aikata alheri, sannan kuma ka ki mummunan aiki da hannaye da harshenka, kuma ka nesanci mai aikata munanan ayyuka iyakacin iyawarka, ka yi jihadi don Allah kamar yadda Ya cancanta kuma kada ka ji tsoron zargin mai zargi cikin al'amurran Ubangiji. Ka kutsa cikin hatsari saboda (kare) gaskiya a duk inda take. Ka tarbiyyantar da kanka da jure wa wahalhalu da abubuwan ki don kuwa adon dabi'un mutum shi ne hakuri a kan gaskiya. Ka mika dukkan al'amurranka ga Ubangijinka, don kuwa ta haka ka mika su ne ga amintaccen wuri da kuma karfafaffi-yar garkuwa. (Idan kana son wani abu) Ka roki Ubangijinka kawai, don kuwa a hannunSa ne bayarwa da hanawa suke, sannan kuma ka yawaita mika komai ga Allah. Ka fahimci wannan nasiha tawa, kada ka juya mata baya, don kuwa mafificiyar magana ita ce wacce ta amfanar. Ka san cewa babu alheri cikin ilimin da bai amfanarwa, kana kuma duk ilimin da babu amfanarwa cikinsa ba a cim ma burin nemansa ba.

Daukan Darasi Daga Rayuwar Magabata

 Ya kai dana, lokacin da na ga na kai tsufa kuma rauni ya fara kama ni, don haka na gaggauta nasihata gare ka da kuma rubuta maka ita don kada ajali na ya zo kafin in sanar da kai abin da ke cikin zuciyata, don kada in sami rauni cikin fahimtata kamar yadda jikina ya yi rauni, ko kuma dakarun sha'awa ko kuma fitinun duniya su galabce ka, su maishe ka kamar mahaukacin rakumi. Hakika, zuciyar matashi kamar kasar da ba a shuka ta ba ne, takan karbi duk abin da aka shuka a cikinta. Don haka na yi kokarin shiryar da kai kafin zuciyarka ta kekashe, kana kuma kwakwalwarka ta kasance cike da abubuwa, don ka kasance cikin shirin karbar tajruban (kwarewa) wasu, ta hanyar amfani da hankali, don ka tsira daga fuskantar irin wadannan tajrubobi da darussa. Ta haka ne, za ka wadatu daga wahalar nemansu da kuma gwada su. Ta haka, za ka san abubuwan da muka riga muka gani da ma wadanda suka tsere mana. Ya dana, duk da cewa ban kai shekarun da wadanda suka gabace ni suka kai ba, to amma duk da haka na yi dubi cikin ayyukansu da kuma tunani kan abubuwan da suka faru da su cikin rayuwarsu. Na yi tafiya cikin abubuwan da suka bari har sai da na zama kamar daya daga cikinsu.

A hakikanin gaskiya ma dai, ta hanyar al'amurransu da na riga na sani sun sanya tamkar na zauna da su tun daga na farkonsu har zuwa na karshensu. Ta haka ne na samu damar tace maras kyau daga mai kyau da kuma maras amfani daga mai amfani. Na zaba maka abubuwan da suka fi cancanta daga cikin wadannan abubuwa, na kuma tanadar maka abubuwa masu kyau kana tacaccu daga cikinsu na kuma nesantar da munanansu daga gare ka. Da yake na damu da al'amurranka kamar yadda ya kamata kowane uba ya yi wa dansa da kuma kokarin da nake yi na tarbiyyantar da kai, na ga ya dace in yi hakan a lokacin da shekarunka suka dada karuwa da kuma fuskantar sabon yanayi na rayuwa, kana mai mallakar kyakkyawar niyya da kuma tsarkakakkiyar zuciya. Don haka na yanke in fara da koyar da kai Littafin Allah Madaukakin Sarki da kuma tawilce-tawilcensa, dokoki da shari'o'in Musulunci, halal da haram, sannan kuma kada in ketare (wadannan koyarwan) da kai. Daga nan, sai na ji tsoron kada ka rudu kamar yadda sauran mutane suka rudu saboda son zuciya da bambance-bambancen ra'ayinsu. Don haka, duk da cewa ba na kaunar abin da zai dame ka, na ga ya dace in bayyana maka wannan lamari maimaikon in bar ka a wurin da ba na ganin za ka tsira daga fadawa cikin halaka. Ina mai fatan Allah Zai taimake ka a kan abin da kake kai da kuma shiryar da kai. Don haka nake rubuta maka wannan wasiyya tawa.

Tsoron Allah da Kula da Ayyukan Wajibi

Ka sani, ya kai dana, mafi girman abin da nake so ka dauka daga cikin wannan wasiyya tawa shi ne ka ji tsoron Allah da kuma kula da abubuwan da Ya wajabta maka, sannan ka yi koyi da ayyukan iyayenka da suka gabata da kuma salihan mutane daga zuriyarka, don kuwa ba su gaza ba wajen gane wa kansu abin da kai kake gane wa kanka, suna tunani kamar yadda kake yi. Daga baya kuma tunanin nasu ya sanya su aikata abubuwan da suka hau kansu wadanda suka sani, sannan kuma suka nesanci abubuwan da ba a kallafa musu ba. Idan har zuciyarka ta ki yarda da hakan ba tare da ka nemi sani kamar yadda su suka nema ba, to dole ne bukatunka (ra'ayinka) su kasance ta hanyar fahimta da kuma masaniya ba ta hanyar fadawa cikin kokwanto ko kuma shiga cikin rikice-rikice ba. Ka nemi taimakon Ubangiji da komawa gare Shi kafin ka tabbatar da ra'ayinka kan hakan, da kuma nesantar duk wani abin da zai sanya ka cikin rudu ko kuma halaka. A duk lokacin da ka tabbatar cewa zuciyarka a tsarkake take kuma ta kaskanta, sannan kuma tunaninka ya taru waje guda, kuma dukkan kokarinka kan hakan ya taru waje guda, to daga nan ka dubi abin da na yi maka bayaninsa; to matukar dai ba ka cim ma abin da kake so da kuma kwanciyar hankali ba, ka san cewa kana taka kasa ne kamar makauniyar rakuma da kuma fadawa cikin duhu, duk kuwa da cewa mai neman addini bai kamata ya fada cikin duhu ko kuma rudu ba. Lalle kamewa daga hakan shi ya fi.

 Ya dana, ka fahimci wannan wasiyya tawa, ka san cewa Mamallakin mutuwa Shi ne kuma Mamallakin rayuwa, kuma Mahalicci Shi ne Mai kashewa, kuma Mai kawarwa Shi ne dai Mai dawo da (abin da ya kawu), kuma Wanda yake kawo cuta, Shi ne kuma dai Mai magani, kuma wannan duniya ba za ta ci gaba da tafiya ba face a kan abin da Allah Ya ajiye na daga ni'imomi, jarrabawa, sakamakon ranar lahira, ko kuma abin da Ya so wanda ba ka sani ba.

Idan har ba ka gane wani abu daga cikin wannan abu ba, to ka jingina shi ga jahilcinka gare shi, don kuwa tun lokacin da aka halicce ka, an halicce ka a jahili ne, kafin daga baya ka san abubuwa. Akwai abubuwa da dama da ka jahilce su, kuma idanuwanka suka yi mamakin ganinsu, to amma daga baya ka fahimce su! Don haka ka yi riko da Shi Wanda Ya halicce ka, Ya arzurtaka da kuma tabbatar da kai, saboda haka dole ne ibadarka ta kasance gare Shi, haka nan kuma bukatunka su kasance gare Shi, sannan kuma Shi kadai za ka ji tsoro. Ka sani Ya dana, babu wani wanda ya karbi sako daga wajen Ubangiji Madaukakin Sarki kamar yadda Annabi (s.a.w.a.) ya yi, don haka, ka dauke shi a matsayin jagora da kuma shugabanka mai cetonka.

Hakika, ba zan yi kasa a gwiwa ba wajen ba ka shawarwari, lalle ba za ka iya gano wa kanka wani abin da zai kyautata rayuwarka sama da abin da na gano maka ba, koda kuwa ka yi kokarin yin hakan(4). Ka sani Ya kai dana, cewa idan da Ubangijinka Yana da wani abokin tarayya, to da manzanninsa su ma sun zo maka, kuma da ka ga alamun iko da mulkinsa, kuma da ka san ayyuka da kuma siffofinsa. Sai dai kawai Shi kadai ne Ubangiji kamar yadda Ya siffanta kanSa, babu wani wanda zai kishiyance Shi cikin mulkinSa, kuma ba Zai taba gushewa ba. Shi ne wanda ya rigayi kowani abu Wanda kuma ba Shi da farko, sannan kuma Shi ne na karshe Wanda kuma ba Shi da karshe. UbangijintakanSa ta daukaka zuciya ko gani su kewaye Shi. Idan har ka fahimci haka, to ka aikata kamar yadda ya dace irinka ya aikata cikin kaskantaccen matsayi, karancin iko, yawan gazawa da kuma yawan bukatuwansa ga Ubangijinsa wajen neman biyayya gare Shi, tsoron azabarSa da kuma fushinSa, don kuwa ba Ya umurtanka face sai ga alheri, sannan kuma ba Ya hana ka face sai ga abu mai muni. Ya dana, hakika ni na sanar da kai duniya da kuma yanayinta, gushewarta da kuma karewarta, sannan kuma na sanar da kai lahira da kuma abin da aka tanadar wa ma'abutanta, kana kuma na buga maka misalin kowanne daga cikinsu don ka dau darasi da su ka kuma kula da su. Lalle misalin wadanda suka fahimci duniya kamar matafiyan da suka sami kansu a bushashshen wuri ne kana suka yi aniyar barin gurin zuwa ga wuri mai ni'ima. Suka jurewa wahalhalun hanya, rabuwa da abokai, tsananin tafiya da rashin abinci don su cim ma burinsu da kuma isa ga mazauninsu. To (irin wadannan mutane) ba za su ji zafin hakan ba, sannan kuma ba za su ga sun yi aikin baban giwa ba. Babu wani abin da ya fi soyuwa a gare su sama da abin da ya kusanta su ga manufarsu da kuma gidansu(5).

Sannan kuma misalin wadanda wannan duniya ta rude su, kamar mutanen da suke wuri mai ni'ima, to amma sai suka kyamace shi suka koma zuwa ga bushashshen wuri. Lalle babu wani abin da ya fi zama abin ki da kuma kyama a gurinsu kamar barin yanayin da da suke ciki, zuwa ga wurin da za su je gare shi ba tare da sun shirya ba kana kuma suna kan dosansa(6).

Mu'amala Tsakanin Mutane Ya kai dana, ka sanyakanka ya zama maka ma'aunin (mu'amalarka) da wasunka, ka so wa waninka abin da kake so wa kanka, kana kuma ka ki masa abin da kake ki ma kanka, kada ka zalunci wani kamar yadda ba ka so a zalunce ka, ka kyautata wa waninka kamar yadda kake so a kyautata maka. Ka ki wa kanka duk abin da kake ganinsa mai muni ne ga waninka, ka yarda da abin da mutane suka maka wanda kai ma za ka so su yarda da shi daga gare ka, kada ka fadi abin da ba ka sani ba ko da yake sanin naka kadan ne, sannnan kada ka fadi abin da ba ka so a fada maka. Ka sani fa cewa jiji da kai kishiyar daidai ne sannan kuma bala'in hankali ne.

Don haka, ka kara kokarinka kada ka kasance asusun wasunka(7) (ka tara dukiya domin wasu su kwashe a bayanka). A lokacin da ka sami shiriya da kuma isa ga manufarka, to ka kaskantar da kanka iyakacin kaskantarwa ga Ubangijinka. Ka san cewa a gabanka akwai tafiya mai nisan gaske da kuma tsananin wahala, sannan ba makawa sai ka yi ta. Don haka ka dauki gwargwadon abin da kake iyawa kana mai la'akari da karfinka, kada ka dauki abin da ya fi karfinka don kada nauyinsa ya kasance musiba gare ka(8). A duk lokacin da ka sami wani mabukacin da zai iya dauka maka wannan guzuri naka zuwa ranar lahira lokacin da kake bukatansa, to kada ka yi kasa a gwiwa wajen amfanuwa da wannan dama wajen ba shi ya dauka maka. Ka yi kokarin ka ga ka yi ta kara masa wannan guzuri matukar dai kana iyawa, don kuwa mai yiyuwa ne (daga baya) za ka bukace shi amma ba za ka same shi ba. Ka yi kokarin ribantuwa da wanda yake son bashi a wajenka a lokacin da kake da shi, don ya biya ka a lokacin da kake bukatuwa da shi(9).

Ka fa sani cewa a gabanka akwai wani kwari mai wuyan wucewa(10) wanda mutumin da yake da karancin nauyi a kansa zai fi mai nauyi da yawa saurin wucewa, kuma halin wanda ya gagara wucewa da sauri zai fi muni a kan wanda ya wuce da sauri, kuma karshen wannan kwari dayan biyu ne, ko dai wuta ce ko kuma aljanna. Don haka, ka yi tanadi wa kanka kafin faduwarka, sannan kuma ka tanadi waje wa kanka kafin gazawarka, don kuwa babu wani shiri bayan mutuwa kana kuma babu komowa wannan duniya.

Tausayawan Ubangiji ga BayinSa

Ka sani fa cewa Mamallakin dukiyar sama da kasa Ya ba ka izinin ka roke (addu'a) Shi, sannan kuma Ya yi maka alkawarin karbar (addu'arka). Ya umurce ka da ka roke Shi don Ya ba ka, sannan ka nemi gafararSa don Ya gafarta maka, kuma bai sanya wani abin da zai katange ka daga gare shi ba. Bai bukaci ka koma ga wani wanda zai maka iso zuwa gare shi ba, kuma idan ka yi kuskure, bai hana ka neman gafara ba (tuba), kuma ba Ya gaggawa wajen azabtar da kai, kuma bai kaskantar da kai saboda tuba ba kana kuma ba ya wulakanta ka a lokacin da kafi cancanta a wulakantaka. Ba ya matsa maka a lokacin karban tuba, Ba ya yawaita tambayarka kan sabon da ka aikata, sannan kuma ba ya sa ka yanke kaunar rahamarSa(11), face ma dai Ya sanya rashin aikata zunubinka a matsayin abu mai kyau. Yakan kirga kowane zunubi guda da ka aikata a matsayin abu guda, amma Yakan kirga duk wani aikin alheri guda da ka aikata a matsayin guda goma. Ya bude maka kofar tuba; don haka a duk lokacin da ka kira Shi Zai ji ka, haka nan a duk lokacin da ka kiraye Shi a boye, Zai san ka kiraye Shi. Don haka ka bijiro maSa da bukatunka, ka gabatar da kanka gaba daya gare Shi, ka gaya maSa dukkan matsalolinka, ka neme Shi da ya yaye maka musifunka, ka nemi taimakonSa cikin al'amur-ranka, ka roka daga cikin asusun rahamarSa wanda babu wani wanda zai iya bayarwa daga cikinsa in ba Shi ba, na daga tsawon kwana, lafiyar jiki da kuma yawan arziki. Sannan kuma Ya sanya mabudan asusunSa a hannunka, ta yadda Ya ba ka izinin rokonSa(12).

Don haka, a duk lokacin da ka so, kana iya bude kofofin ni'imominSa da addu'a don ruwan rahamarSa su zubo maka, kada ka yanke kauna da jinkirta karbar addu'arka, don karbar addu'a ana yin ta ne gwargwadon niyyarka. A wasu lokuta a kan jinkirta amsa maka bukatarka, hakan kuwa mai yiyuwa don a kara maka ladanka ne, kana kuma don ya kasance babban kyauta ga mai sauraro. A wasu lokuta ka kan roki wani abu a hana ka, a kan musanya maka shi ne da wani abin da ya fi shi alheri cikin gaggawa ko kuma bayan dan jinkiri, ko kuma a kan dauke maka wani abu wanda dauke shi din shi ne ya fi alheri gare ka(13).

Don mai yiyuwa ne cikin abin da ka tambaya akwai wani abin da zai halakar da kai idan da an ba ka, don haka ka tambayi abin da a kullum kyansa zai saura maka, kuma zai gusar maka da bala'insa; don kuwa dukiya ba za ta dawwama maka ba kamar yanda kai ma ba za ka dawwama mata ba. Ya dana, ka sani cewa an halicce ka ne don lahira ba don duniya ba, don gushewa ba don dawwama ba, don mutuwa ba don rayuwa ba; ka sani cewa kana kan guri ne wanda ba naka ba, gidan shiryawa da kuma wucewa zuwa ga lahira. Kai abin bin mutuwa ne wanda kuma mai gudu mata ba zai tsira ba, kuma ba makawa za ta riske shi, don haka, ka kasance cikin shirin kada ta riske ka alhali kana cikin mummunan hali (sabo) kana mai tunanin tuba, kwatsam ta shiga tsakaninka da ita (tuba). A irin wannan halin ka halaka kanka.

Yawaita Tunawa da Mutuwa Ya dana, ka yawaita tuna mutuwa da kuma tunanin wurin da dole ka je bayan mutuwa, ta yadda a duk lokacin da ta zo kana nan cikin shiri, kada ta yi maka ba zata ta ba ka mamaki. Ina gargadinka da kada nitsuwar da ma'abuta duniya suka yi zuwa ga (kyalkyalin) duniya ya rude ka, lalle Allah Ya gargade ka a kanta sannan kuma duniyar da kanta ta yi maka bayanin kanta da cewa ita ba gurin tabbata ba ce. Hakika, wadanda suke rige-rigen nemanta kamar karnuka ne masu haushi ko kuma mahaukatan namun daji masu gaba da junansu, mai karfi yakan cinye maras karfi kana kuma babba yakan danne karami. Wasu daga cikinsu kuma kamar daurarrun shanu ne wasu kuwa kamar sakakkun shanu ne wadanda suka rasa hankalinsu suna gudu zuwa ga wurin da ba su sani ba. Su garke ne na musifu da suke yawo cikin kwari (ba tare da sun san inda za su je ba). Babu wani makiyayin da zai kula da su ko kuma ya kai su wurin kiwo. Duniya ta sanya su a fagen makanta kana ta dauke idanuwan-su daga hasken shiriya, don haka suka kasance cikin dimautuwa da kuma fadawa cikin kyalkyali-kyalkyalinta. Suka dauke ta a matsayin ubangiji, don haka sai ta yi wasa da su, su ma suka yi wasa da ita, ta haka sai suka mance da abin da ke gabanta (lahira).

Ƙara sabon ra'ayi