Hadin Kan Musulmi
Jagoran juyin Musulunci na iran ya yi kakkausan suka ga wahabiyan da suke kafirta musulmi suna halatta jininsu. Su dai wannan aqida ta wahabiyanci tana samun kariya daga saudiyya ne kai tsaye, kuma duk in da suke son tarwatsawa a duniya sai su yada ta su fara kashe mutane musulmi da wanda ba musulmi ba da sunan jihadin kafirai. Don haka ne ko da yaushe suke zama matsala ga ci gagan kasashen musulmi da kuma dagula duk wani yankurin hadin kan musulmi.
Ƙara sabon ra'ayi