Ginshikin Tunani da fatan Juyin Musulunci
Ginshikin Tunani da fatan Juyin Musulunci
Juyin musulunci ya kai ga yin nasara ne a karshen karni na ashirin. Babu wani juyin juya hali da ya faru a duniya nan ba tare da wani tubalin tunani da ya ginu akansa ba. Ba kuma zai iya kafa tsarin da zai tafiyar da al'umma ba tare da wannan irin tsarin na tunani ba. Haka nan dukkan juyin juya halin da aka yi a duniya su ke. Juyin musulunci na Iran kamar yadda wani manazarci dan kasar Faransa ya ambaya, ya share fagen shekara dari mai zuwa na sauyin da ya kamata ya kasance anan gaba fiye da akidojin siyasa da ake da su a wannan zamanin.A baya,ma'abota nazariyyoyi na akidun siyasa da zamantakewa kamar Karl Max da Emile Durkheim suna daukar cewa dole ne a rayu bisa tsarin dokoki na duniya kadai. Sun yi imani da cewa addini ba shi da wata rawa da zai taka a cikin rayuwar yau da kullum ta jinsin biladama. Sai dai juyin musulunci na Iran ya yi wa wannan nazariyyar juyin waina ta yadda ya shigar da addini a cikin tsarin zamantakewa na yau da kullum. Daniel pipes wanda ba'amerike ne mai ra'ayin 'yan mazan jiya, ya fada a wani taron karawa juna sani a kasar Turkiya cewa:" Dole ne mu yi furuci da cewa kafin cin nasarar juyin musulunci a Iran, mu Amerikawa ba mu taba damuwa da yin bincike akan addini ba. Sai dai tun bayan juyin musulunci ya zama wajibi a gare mu Amerikawa mu rika gudanar da bincike da nazari akan addini."Imam Khumaini da ya dogara da tunani da akida ta musulunci, ya sake dawo da matsayin addini a tsakanin al'umma. Ya kuma tabbatar da cewa addini zai iya zama mai taka gagarumar rawa kuma mai amfani a cikin siyasa da kuma tsarin zamantakewa. Sakon juyin musulunci shi ne cewa addini zai iya tafiya kafada da kafada da hankali, kuma kyawawan halaye za su iya tafiya tare da siyasa. Saboda haka tsarin da jamhuriyar musulunci ta kafa na demokradiyyar addini ba shi da tamka a fagen siyasar kasa da kasa.A wannan lokacin mutanen duniya da dama sun fahimci cewa musulunci addini ne da riko da shi ya ke samarwa da mutum sa'ada da kyakkyawar rayuwa. A hakikanin gaskiya juyin musulunci na Iran ya gabatar da musulunci ne bisa dacewa da yanayi da zamanin da ake rayuwa a cikinsa. Peter Sholator wanda marubuci ne dan kasar Jamus ya rubuta cewa:" A wannan lokacin da yunkurin ci gaba na addini ya fara, bisa albarkacin juyin musulunci na Iran, mutanen duniya sun fahimci cewa hanyar samun sa'ada tana tattare da musulunci."Shekaru talatin da daya sun wuce daga cin nasarar juyin musulunci a Iran. A cikin tsawon gomiya uku ta juyin musulunci, ya fuskanci kalubale mai tsanani wanda kuma ya tsallake shi. A cikin watannin bayan nan da aka yi zaben shugaban kasa anan Iran,an fuskanci wata jarrabawa mai girma sai dai duk da haka ya tabbata a fili cewa juyin musulunci na Iran ya wuce yadda ma'abota nazariyya na yammacin turai su ke zato.Shahid Mutahhari ya bayyana juyin musulunci na Iran da cewa ya yi kama da farkon bayyanar musulunci. Mutahhari yana daukar musulunci a farkon bayyanarsa a matsayin gagarumin juyi a karkashin jagorancin annabi muhammadu mai tsira da aminci da iyalan gidansa. Juyi ne wanda ya kawo gagarumin sauyi a cikin bangarorin siyasa da zamantakewa da tattalin arziki da al'adu.Juyin musulunci a Iran bisa shugabancin jagora da ya ke da karbuwa a wurin al'umma yana a matsayin daya daga cikin siffofin da ya kebanta da su. A tsawon lokacin da Imam Khumaini ya ke jagorantar juyin musulunci, makiya sun kitsa da kulla makirce-makirce masu yawan gaske da zummar kau da juyin daga kan hanyar da yake tafiya akanta. Sai dai jagorancin Imam Khumaini da hikimarsa sun hana wancan makircin kaiwa ga manufarsa. Dagane da rawar da Imam Khumaini ya taka wajen tafiyar da juyin musulunci, jagoran juyi Ayatullah Sayyid Ali Khamnei yana fadin cewa:" Shi jagora ne mai hikima da ilimi wanda ya ke jan gaban wannan yunkurin, yana da karfin imanin da kuma aiki da suka zamar masa jini da tsoka ta yadda hatta wadanda ba su yi imani ba su ke tasirantuwa da shi matuka."Juyin musulunci ya ginu ne bisa tubali uku da su ne addini da jagoranci da kuma hadin kan al'umma. Daga farkon yunkurinsa har zuwa yanzu yana bada muhimmanci ga mutunta mutum da kuma kai mutum ga rayuwa ta sa'ada. Sannan kuma ya kai ga kafa tsarin musulunci bisa taken 'yanci da cin gashin kai. Imam Khumaini ya bada taken cewa: "Babu mika kai ga tsarin gabaci na kwaminisanci, babu mika kai ga tsarin yammacin turai na jari-hujja." Bayan cin nasarar juyi wannan taken ya ci gaba kuma an kafa hukuma mai cin gashin kanta a daidai lokacin da Amerika da Tarayyar Soviet su ke shimfida ikonsu a duniya. Ficewar da Iran ta yi daga karkashin ikon Amerika da danniyarta yana a matsayin wata babbar nasara ce ga Iran.A karkashin juyin musulunci, samun cikakken 'yanci bai tsaya a cikin kawo karshen danniyar kasashen waje ba daga cikin Iran, An ci gaba da kokarin samun 'yanci acikin dukkan bangarorin siyasa da tattalin arziki da tunani da al'adu. Imam Khumaini ya yi imani da cewa matukar kasa ba ta sami cikakken 'yanci ba to babu wani abu da zai gyaru a cikinta. Juyin musulunci yana fafutukar samun 'yanci da cin gashin kai da son shimfida adalci da kuma fada da masu danniya wanda shi ne abinda ya jawo hankalin duniya akansa. Ya kuma sa al'ummu da dama na duniya yunkurawa domin ganin sun sami 'yanci daga danniyar masu danniya da 'yan mamaya.Shimfida adalci a cikin al'umma yana daga cikin abubuwan da dukkan al'ummun duniya su ke ganin shi da kima da daraja kuma su ke fafutukar ganin haka ya tabbata. Domin kuwa duk wani mutum ma'abocin hankali yana kaunar adalci. Shimfida adalci yana daga cikin muhimman manufofin da juyin musulunci ya ke son ganin sun tabbata. Imam Khumaini a matsayinsa na jagoran juyin musulunci ya yi imani da cewa tushen ci bayan da mafi yawancin al'ummu su ke da shi, shi ne wawason dukiyarsu da shugabanni su ke yi. Kuma matukar ba a sake tsarin siyasa da tatalin arziki ba a duniya to shimfida adalci a tsakanin al'umma zai yi wahala.A daidai wannan lokacin da aka shiga cikin gomiya ta hudu daga cin nasarar juyin musulunci, jamhuriyar musulunci ta Iran tana ci gaba da bada taken raya kasa da kuma shimfida adalci.Tsarin Jamhuriyar musulunci na Iran yana tafiya akan hanyar gina rayuwa mai inganci anan gaba ta hanyar tunbuke talauci daga tushensa da magance matsalar tattalin arziki da kuma shimfida adalci. Yau da gobe kuwa ta tabbatar da cewa tsarin jamhuriyar musulunci na Iran yana samun nasara ta magance matsalolin da ya ke fuskanta domin kaiwa ga manufar da ya sanya a gaba.
hausa.irib.ir
Ƙara sabon ra'ayi