Tasirin Kafafen Wats labaru akan mace da iyali.

Tasirin Kafafen Wats labaru akan mace da iyali

AllahءMusulunciءAddiniءMohammadءAliءshiءmahdiءtvshiaءTasirin Kafafen Wats labaru akan mace da iyali

A wannan zamanin da mu ke ciki, kafafen watsa labaru mabanbanta sun yi mana kawanya ta kowace kusurwa. Daga kan Rediyo da Telbijin da Tauraron Dan'adam da Internet zuwa wayar tafi da gidanta. Mutane kadan ne a duniyar nan wadanda za a wayi gari kuma rana ta fadi ba tare da sun yi mu'amala da daya daga cikin wadannan kafafen watsa labarun ba. Hanyoyin sadarwa da kafafen watsa labaru suna da tasiri mai girma a cikin rayuwar yau da kullum.Abin takaici ne cewa a yau mafi yawancin kafafen watsa labaru suna a matsayin makami ne a hannun yan jari hujja. Su ne su ke amfani da batutuwa na al'adu domin su sami kutse a cikin kasashe da dama na duniya. Herbert Schiller wanda marubuci ne dan kasar Amurka yana fadin cewa: Idan wata kasa tana son yin kutse a cikin harkokin wata kasa to tana son al'adunta su share fage."A ra'ayin Schiller, hanya mafi girma wajen yin tasiri a cikin al'adun al'ummu ita ce kafafen watsa labaru da su ka kunshi rediyo da telbijin da jaridu. A wannan lokacin kuwa masana sun maida hankali wajen yin nazari dangane da tasirin kafafen watsa labarun akan mata da iyalai. Akan haka ne kuma aka yi taron kasa da kasa anan Iran da zummar tattauna wannan batu. Fitattun mata da su ka fito daga Kasashe 19 ne suka halarci wannan taron.Iyali cibiya ce mai tsarki da muhimmanci a cikin tsarin al'umma. Ci gaban jinsin biladama da wanzuwa anan duniya yana da alaka ne da kare tsarin iyali. Lalacewar al'umma kuwa tana farawa ne daga fara lalacewar iyali. Idan kuwa iyalai su ka gyaru to al'umma za ta fara gyaruwa. Daya daga cikin ma'aunan iyalai na gari shine alaka da kauna da soyayya a tsakaninsu. Tabbas da akwai matsaloli da yawa wadanda suke sa kauna da soyayya su yi rauni. Daya daga cikin wadannan dalilan shi ne amfani da kafafen watsa labaru ta hanyar da ba ta dace ba.Mace a cikin kowace al'umma da kowace kabila tana taka gagarumar rawa wajen bunkasar al'adu. Yadda mata su ke maida hankali akan kawa yana daga cikin abubuwan da su ke kawata iyali. Sai dai wannan sha'awar ta yin kawa da mata su ke da ita wacce dabi'a ce ta su za ta iya sanadin haifar da barna idan ba a kula da ita kamar yadda ya dace ba. Matsayin mace a cikin al'umma zai iya daukaka wannan al'ummar ko kuma ya yi sanadiyyar faduwarta.Malam Laleh Iftikhari wacce 'yar majalisa ce ta Iran ta gabatar da jawabi a wurin wannan taron inda ta ce:" Matsayin mace zai iya zama abin koyi mai bunkasa ci gaban al'umma da kuma samar da kyakkyawar tarbiyya ga 'ya'ya. Haka nan kum zai iya zama mai yin barna wajen yi wa yara tarbiyya. A cikin kafafen watsa labarun yammacin turai ana amfani da mace a matsayin 'yar tallar haja da kayan masarufi. wannan ya sa ana kau da kai daga hakikanin kasantuwar mace a matsayinta na mutum. Da sauko da matsayin ta kasa da haka."Bugu da kari malama Laleh ta yi ishara da yadda a jamhuriyar musulunci ta Iran aka tsara dokokin da su ka baiwa mata damar taka rawa a cikin iyali da kuma a cikin al'umma.Rawar da mace ta ke takawa ta fuskar tattalin arziki yana daga cikin abubuwan da aka tattauna a wurin wannan taron. Kafafen watsa labarun da su ke tallata batun zaman duniya falle daya, suna kokarin cusawa mace jin cewa aikinta a fagen tattalin arziki shi ne ta sayi abinda za ta yi amfani da shi ba ta zama mai yin wani abu ba da wasu za su amfana.Malama Mehrshady wacce mai koyarwa ce a jami'a anan Iran ta bayyana cewa:"Kafafen watsa labaru suna taka gagarumar rawa wajen cusawa mace a cikin gida zaukin wani abu da sha'awar kayan da ake amfani da su."Tasirin kafafen watsa labaru wajen cusawa mata ra'ayin sanya suturar hijabi abin nema ne. Musamman a wannan lokacin da nuna tsiraici ya zama abinda ake alfahari da shi ta hanyar fina-finai. Manufar wannan kuwa shi ne sauya al'adun mata da nuna musu cewa yin tsiraici abin nema ne.Malama Hayya Thamir wacce malamar jami'ar kasar qatar ce ta yi ishara da rawar da kafafen watsa labaru su ke iya takawa wajen cusawa mata son mutunta kawunansu da sanya hijabi. Rawar da hijabi ya ke takawa kuwa ba ta tsaya akan ita mai daurawa ba ya kuma shafi ita kanta al'umma saboda zai bata tsaro ta fuskar kyawawan halaye da kame kai."Ita kuwa malama Shu'ulah Shakib daga kasar Bahrain ta yi ishara da rawar da kafafen watsa labaru za su iya takawa wajen kare al'umma daga gurbata.Taron na Tehran ya tabo abubuwa masu muhimmanci da suka shafi rayuwar mata da kuma rawar da za su iya takawa wajen kare al'umma daga gurbata.

hausa.irib.ir

Ƙara sabon ra'ayi