Shahid Mutahhari Da Tarbiyyar Addini

 Shahid Mutahhari Da Tarbiyyar Addini

 Shahid Mutahhari Da Tarbiyyar AddiniAllahءMusulunciءAddiniءMohammadءAliءshiءmahdiءtvshiaء

Normal 0 false false false EN-US JA FA MicrosoftInternetExplorer4 Malamai da kuma masana daidai su ked a taurari masu haske. Su ne masu hasakak samaniyar ilimi da sani. Ta hanyar kwazo da kokarin malaman ne tunani da nazarce-nazarce na musulunci su ka samu. Daya daga cikin malamai ma'abota tunani shi ne shahid Ustaz Murtada Mutahhari. Shi mutum ne wanda ya sadaukantar da rayuwarsa wajen kwazo da kokari domin bayyana mahangar musulunci a cikin fagagen siyasa da al'adu da tsarin zamantakewa. Yana daga cikin tsirarun mutane wadanda rubuce-rubucen da su ka yi suka zama madogara mai girma da aka gina tsarin jamhuriyar musulunci ta Iran akansa. Kasantuwar mutumin da ya ke tunani fiye da zamanin da ya ke rayuwa a cikinsa, ya yi nazari akan batutuwan da suka shafi dukkanin al'ummar musulmi. Yana daga cikin mutanen da su ke fada da tunanin raba addini da siyasa ko kuma nesanta shi daga cikin tsarin zamantakewa na al'umma. Domin hakan yana nufin mika al'umma ga 'yan mulkin mallaka. Ya yi imani da cewa dokokin musulunci dokoki ne da su ka dace da kowane zamani kuma wadanda za su iya warware matsalolin al'umma na duniya da kuma na ruhi. Ya kuma bayyana fifikon da musulunci ya ke da shi a cikin fagagen akida da ilimi da zamantakewa da siyasa. Ta hanyar kafa dalilai na mandiki da ilimi ya rusa akidun kafircewa addinai da ake da su a cikin wannan zamanin musamman ma dai a cikin karni na 20 da ya gabata irin kwaminisanci da sakulanci na yammacin turai. A cikin tsarkin zuciya da son gaskiya shahid Mutahhari rika yin nazarinsa a cikin koyarwar musulunci domin biyan bukatun matasa na addini da tunani. Ya kuma saukaka ma'anoni masu zurfi na falsafa da ilimi ta yadda za su yi saukin fahimta ga bangarori daban-daban na al'umma. Wannan abinda shahid Mutahhari ya kebanta da shi, ya zama wata hanya mafi tasiri ta farfado da tunanin addini a tsakanin al'umma.Mutahhari, mutum ne ma'abocin tunani wanda ya ke kallon batutuwan daban-daban da mahanga faffada da su ka kunshi kyawawan halaye da tarbiyya. Shi a kanshi yana a matsayin abin koyi ne ta fuskar cikar tunani. Kasantuwar batun tarbiyya da kuma kyawawan halaye a matsayin muhimman abubuwa na zamani, za mu yi dubi akan mahangar wannan shahidin dangane dasu.A bisa mahanga ta shahid Mutahhari, tarbiyya a musulunci ta ginu ne akan turbar tauhidi. Wannan turbar ta tauhidi kuwa tana baiwa rayuwar mutum ma'ana. Abinda turbar tauhidin ta ke nufi shi ne kallon rayuwa a matsayin wacce ta ke tafiya bisa hikima da kuma cikakken tsari na alheri da rahama kuma domin halittu su kai ga kamalar da ta dace da su. Mutum yana da matsayi na musamman a tsakanin dukkanin halitu kuma wajibi ne a gare shi ya kai ga zama kamili a rayuwarsa ta duniya."Mahangar tauhidi," Inji Shahid Mutahhari, " Tana hana mutum faduwa a cikin ramin na rashin imanin da wani abu, ta ke kuma baiwa mutum din karfin guiwa da daukaka matsayinsa. Daga cikin abubuwan da musulunci ya kebanta da su a cikin koyarwarsa da akwai yi wa mutum tarbiyya bisa wannan turbar ta tauhidi. Cewa mutum zababbe ne kuma zabar da ubangiji ya yi masa tana da manufa, yana baiwa rayuwarsa wata ma'ana ta musamman.Hakan nan kuma mutahhari ya yi imani da cewa, tarbiyyar musulunci ta kunshi komai, wato babu wani bangare na rayuwar mutum wacce musulunci bai tabo ba a karkashin tarbiyya. Mutahhari yana fadin cewa:" Babu wani addini ko wata akida wacce ta shiga cikin kowane bangare na rayuwar mutum kamar musulunci. A cikin koyarwar addinin musulunci yana da tsararriyar ibada da kyawawan halaye. Kuma kamar yadda ya tsara yadda alakar mutum da Allah za ta kasance haka nan kuma ya tsara yadda alakar mutane a tsakaninsu za ta kasance da kuma hakkokinsu da nauyace-nauyacen da su ka rataya a wuyansu.Yana fadin cewa: " A cikin musulunci, dukkanin bangarorin rayuwa an yi musu madogara. Kama daga gangar jikin mutum da kuma ruhinsa. An kuma shiryar da mutum din akan yadda zai yi tafiya akan tafarkin kaiwa ga kamala."Daya daga cikin abubuwan da tarbiyya ta kebanta da su, shi ne matsakaicin matsayi. Yana fadin cewa: "Al'ummar da kur'ani ya yi mata tarbiyya, ita ce mai nisantar wuce gona da iri da kuma saku-saku. A kodayaushe tarbiyyar musulunci tana ginuwa ne bisa matsakaicin matsayi.Haka nan kuma Mutahhari yana bada muhimmanci akan kare karamar mutum wanda ya ke lazumtar yin masa tarbiyya. Yana fadin cewa:"Ruhin mutum yana da matsayi da kima, kuma yana daukar kyawawan halaye a matsayin abubuwan da su ka dace, halayen marasa kyau kuma a matsayin abinda ba su dace ba. Wajibi ne ga mutum da ya zama mai yi wa kansa hisabi saboda kada ya rasa tsarkin zuciyarsa."Tare da fahimta mai zurfi da kuma cikakken sani da musulunci, shahid mutahhari ya yi bayani akan koyarwar addinin musulunci wanda ya dace da kowane zamani da bagire. Da fatan cewa tunani da zanarce-nazaren wannan masani za su zama fitila mai hasakawa a kan hanyar kaiwa daraja ta koli ta ilimi a cikin al'ummar musulmi.

Ƙara sabon ra'ayi