Sojojin Haramtacciyar Kasar Isra'ila Sun Jikkata Palasdinawa Da Masu Rajin Kare Hakkin Bil-Adama.
Sojojin Haramtacciyar Kasar Isra'ila Sun Jikkata Palasdinawa Da Masu Rajin Kare Hakkin Bil-Adama.
Palasdinawa da masu rajin kare hakkin bil-Adama da dama ne suka jikkata sakamakon hare haren da sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila suka kai kan masu zanga zanga a yankin yammacin garin Ramalla da ke gabar yammacin kogin Jordan. Majiyoyin Palasdinawa a yau Asabar sun habarta cewar a hare haren da sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila suka kai kan masu gudanar da zanga zangar nuna adawa da ginin katangar wariya da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ke yi a yankunan Palasdinawa da nufin killace su, hare haren sun yi sanadiyyar raunata Palasdinawa da masu rajin kare hakkin bil-Adama da suka fito daga sassa daban daban na duniya. Sojojin na gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila sun harba harsasan roba da iskar gas mai guba ne kan Palasdinawa da masu rajin kare hakkin bil-Adama da suke gudanar da zanga zangar lumana domin nuna adawa da ginin katangar wariya a yankin garin Ramallah da ke gabar yammacin kogin Jordan a jiya juma'a.
hausa.irib.ir
Ƙara sabon ra'ayi