Siriya ta Bukaci A Dau Mataki Kan Saudiyya Saboda Goyon Bayan Ta'addanci
Siriya ta Bukaci A Dau Mataki Kan Saudiyya Saboda Goyon Bayan Ta'addanci
Kasar Siriya ta kirayi kasashen duniya da su hada karfinsu waje guda wajen fada da kasar Saudiyya sakamakon irin goyon bayan da take ba wa ayyukan ta’addanci a duniya wanda hakan babbar barazana ce ga zaman lafiyan duniya.
Ma’aikatar harkokin wajen kasar Siriyan ce ta yi wannan kiran cikin wata sanarwa da ta fitar inda ta ce ta aike da wasika zuwa ga MDD da kuma kwamitin tsaron MDDn inda ta bukaci da a dau matakan da suka dace a kan kasar ta Saudiyya saboda irin goyon bayan da take ba wa kungiyoyin ‘yan ta’adda da kuma masu kafirta mutane da take turo su kasar Siriyan inda suke ci gaba da zubar da jinin al’ummar kasar.
Wannan bukata da ma’aikatar harkokin wajen Siriyan ta gabatar ta zo ne a daidai lokacin da tsohon shugaban hukumar leken asirin kasar Faransa Bernard Squarcini ya zargi kasar Saudiyya da goyon baya da kuma taimakawa kungiyoyin ‘yan ta’addan da suke gudanar da ayyukan ta’addanci a yankin Gabas ta tsakiya.
Tsohon shugaban leken asirin na Faransa ya bayyana hakan ne cikin wani sabon littafi da ya buga inda ya ce shugaban kungiyar leken asirin Saudiyyan Bandar bn Sultan yana da hannu cikin ayyukan ta’addancin da ke faruwa a kasashen Afghanistan, Siriya, Labanon, Masar da kuma arewacin Afirka.
hausa.irib.ir
Ƙara sabon ra'ayi