Ijara {Haya} 2
Ijara {Haya} 2
A shirinmu da ya gabata mun fara bayani ne kan Ijara, inda muka bayyana cewa; Ijara nau'i biyu ne:- Ijarar da mutum zai yi na kansa don gudanar da wani aiki a kan wata lada da aka tsadance a kai za a biya shi, da Ijarar da mutum zai bayar na wani abu da ya mallaka don a yi amfani da shi a kan wata lada da aka yi jinga a kai.A shirinmu na yau zamu fara bayani ne kan hukunce hukuncen nau'in Ijara na farko wato Ijarar da mutum zai yi na kansa don gudanar da wani aiki a kan wata lada da aka tsadance a kai za a biya shi.Da farko kulla yarjejeniyar Ijarar da mutum zai yi na kansa baya da bambanci da sauran yarjejeniyoyi da ake kullawa na mu'amala misalin ma'amalar kasuwanci da makamancinsa, don haka dole ne a samu amincewar bangarorin da zasu kulla yarjejeniyar ta ijara da gindaya sharuddan da zasu kai su ga manufar da suke son cimmawa saboda kaucewa bullar matsalar sabani a tsakaninsu.Amincewar bangarorin da suke bukatar kulla yarjejeniyar ijara a tsakaninsu tana tabbata ce ta hanyoyi kamar haka:- Kulla yarjejeniyar ijarar ta hanyar furuci tsakanin mutumin da zai gudanar da wani aiki a kan wata lada da za a biya shi, da mutumin da za a gudanar masa da aikin. Misali tela da ke gudanar da sana'ar dinki ya ce wa abokin ma'amalarsa zan dinka maka riga da wando a kan kudi naira goma, sai mutumin da za a dinka masa tufar ya amsa da cewa na amince. Kamar yadda ya halatta mutumin da za a gudanar masa da aiki ya fara furuci da cewa ina son ka dinka mini tufa riga da wando a kan kudi naira goma, sai tela ya amsa da cewa ya amince.Ya halatta a kulla yarjejeniyar ijara da kowane irin yare ko harshe. Haka nan ya halatta a kulla yarjejeniyar ijara ta hanyar rubutu kamar yadda ake gudanarwa a wannan zamani, inda bayan an cimma yarjejeniya kan gunadar da wani aiki tsakanin mutumin da za a gudanar masa da wani aiki da wanda zai gudanar da aikin a kan wata lada da aka tsadance a kai, sai dukkanin bangarorin biyu su rattaba hannu kan takatar yarjejeniyar da aka cimma, ba tare da sun furta kalmar yarda da amincewa da baki ba.Har ila yau idan mutumin da yake bukatar a gudanar masa da wani aiki ya rubuta irin aikin da yake so da sharuddan aikinsa gami da ladan da zai bayar, kawai ya rage ga duk wanda ke son yin aiki a karkashinsa ya rattaba hannu kan takardar yarjejeniyar da ya tsara, to matukar aka samu mutumin da ya amince da yarjejeniyar da ke takardar kuma ya rattaba hannu a kai, to yarjejeniyar ijara a tsakaninsu ta inganta. Dangane da kurma ko bebe ya isar musu su kulla yarjejeniyar ijara ta hanyar ishara da take fayyace manufar kulla yarjejeniyar ijara. Kamar yadda ya halatta su kulla yarjejeniyar ta ijara ta hanyar rubutu. Ya halatta mutum ya dauki hayar mutane da dama kan su taru su gudanar masa da wani aiki, a nan ya isar masa ya kulla yarjejeniyar ijara da su da furuci guda wato ya furta cewa ya dauki hayarsu kan aikin da yake so a gudanar masa akan lada da suka tsadance a kai, sai dukkaninsu su furta kamar amincewa, ko kuma daya daga cikinsu ya wakilce su wajen furta kalmar amincewar, kamar yadda ya inganta kowanne daga cikin masu son gudanar da aikin ya kulla yarjejeniyar ijarar aikin da zai yi kai tsaye da mutumin da ke son a gudanar masa da aikin.
hausa.irib.ir
Ƙara sabon ra'ayi