Ijara {Haya} 1

Ijara {Haya} 1

IjaraءAllahءMusulunciءAddiniءMohammadءAliءshiءmahdiءtvshiaء

Ijara wato kulla yarjejeniyar mallakar amfanin wani abu a kan wani farashi sananne da aka tsadance a kai.Ijara nau'i biyu ne:- Nau'in farko shi ne Ijarar da mutum zai yi na kansa don gudanar da wani aiki, misalin leburan da zai gudanar da wani aiki a kan wata lada da aka tsadance a kai.Nau'in Ijara na biyu shi ne bada Ijarar wani abu da mutum ya mallaka don amfani da shi a kan wata lada da aka yi jinga a kai, misali mutum ya bada hayar gidansa domin a zauna a ciki na wani kayyadajjen lokaci a kan wani farashi.Ma'amalar Ijara tana bukatuwa ga kulla yarjejeniya tsakanin mai bada Ijara da mai karba : Misali Tela da yake neman abinci ta hanyar dinki ya ce wa abokin ma'amalarsa na amince zan gudanar maka da dinkin riga da wando, sai wanda za a dinka masa tufar ya ce na amince, ko kuma mutumin da ya mallaki gida yake son bada gidan haya ya ce na baka gida na haya, sai dan haya ya ce na amince. Kuma ya halatta dan haya ya fara furta cewa na karbi hayar gidanka, sai mai gidan ya ce na amince, kuma kulla yarjejeniyar Ijarar da kowane irin harshe ko yare ya inganta.Kamar yadda kulla yarjejeniyar Ijara ta halatta ta hanyar furuci, haka nan ya halatta a kulla yarjejeniyar ta Ijara ta hanyar rubutu, dangane da kurma ko bebe kuwa ya isar musu su kulla yarjejeniyar Ijarar ta hanyar ishara da take fayyace manufar kulla yarjejeniyar Ijara, har ila yau kulla yarjejeniyar Ijara ba tare da yin furuci ba ta inganta misali idan dan haya ya mika kudi ga mai gidan haya da nufin karban gidan a matsayin haya, sai mai gidan ya karbi kudin da nufin bada gidan haya.Kafin ma'amalar Ijara ta inganta sai mai bada ijarar da mai karba su cika wasu sharudda kamar haka:- Su kasance masu hankali, balagaggu da hukunce hukuncen shari'a suka hau kansu, su kasance masu cikekken 'yanci wajen gudanar da ma'amalar ta Ijara wato ba tilas wani daga cikinsu aka yi a kan kulla yarjejeniyar da karfi ba, su kasance suna da 'yancin gudanar da ma'amala da dukiyarsu wato ba wadanda shari'a ta hana su yin amfani ne da dukiyarsu ba saboda matsalar bashi da tayi katutu a kansu ko wawanci wato wanda bai san hanyar da ta dace ya sarrafa dukiyarsa ba.Ya halatta mutum ya gudanar da ma'amalar Ijara da dukiyar da ba mallakarsa ba ce idan ya kasance wakili ne ga mai dukiyar.Ya halatta mutum ya gudanar da kulla yarjejeniyar Ijara da dukiyar karamin yaro idan ya kasance waliyi ne ga yaron wato wanda hakkin kula da dukiyar yaron ke hannunsa a shari'a misalin mahaifi ko kakan yaron, ko kuma wakili ne ga waliyin yaron.Yaron da baya da waliyi baya halatta a bada hayarsa don aikata wani aiki ba tare da izinin hakimusshara'i ba ko wakilinsa, idan kuma babu hakimusshara'i ko wakilinsa, ko kuma babu hanyar samun izini daga gare su, to ya halatta a bada Ijararsa kan wani aiki da izinin wasu muminai adilai.

hausa.irib.ir

Ƙara sabon ra'ayi