Sallar Ijara

Sallar Ijara

Sallar IjaraءAllahءMusulunciءAddiniءMohammadءAliءshiءmahdiءtvshiaء

Sallar Ijara, Wato Sallar Da Aka Dauki Hayar Mutum Yayi Wa Mamaci ko Mamaciya. Ya halatta a biya mutum wata lada kan yayi ramakon sallah da ke kan mamaci. Haka nan, sauran ayyukan ibadu da suke kan mamaci da bai yi su ba a lokacin da yake raye, misalin azumi, hajji da makamantansu; wanda idan mutumin da aka biya shi ladar yayi ramakon sallolin da ke kan mamacin ko yayi ayyukan ibadu da suke kansa, to hakan yayi sanadiyyar sauke nauyin da ke kan mamacin. Babu matsala ya kasance mutumin da za a biya shi lada domin yayi ramakon sallolin da suke kan mamaci ya zama shi ne aka masa wasici kan ya dauki hayar wanda zai yi ramakon sallolin ko kuma daya ne daga cikin makusantan mamacin. Misalin Dansa ko kuma wani bare ne aka dauki hayarsa.Don haka, idan kafin mutuwa ta riski mutum ya riga yayi wasici kan a dauki hayar mutumin da zai masa ramakon sallolin da suke kansa bayan mutuwarsa, wanda za a biya mutumin hakkinsa daga cikin dukiyarsa da ya bari, to matukar aka dauki hayar mutumin da zai yi ramakon sallolin kuma yayi ramakon, to wajabcin daukar nauyin ramakon sallolin da suke kan mamaci ya fadi a kan babban dansa da ke raye.Sharadi ne mutumin da za a dauki hayarsa kan yayi ramakon sallolin da ake bin mamaci, ya kasance mai hankali, mai imani, balagagge kuma masanin hukunce-hukuncen fiqihu, wanda zai gudanar da ayyukan sallolin na ramako daidai da ijtihadinsa idan mujtahidi ne shi, ko daidai da fatawar mujtahidinsa da yake masa taqalidi idan muqallidi ne shi ko kuma daidai da ihtiyadi idan muhtadi ne shi, wato wanda ya san yadda ake aiki da ihtiyadi.Ba sharadi ba ne mutumin da za a dauki hayarsa domin ramakon sallolin da suke kan mamaci, ya kasance adali ne shi, wanda idan ya kasance amintacce ne hakan ya wadatar. Ya halatta a dauki hayar namiji domin yayi ramakon sallolin da suke kan macen da ta mutu. Haka nan, ya halatta a dauki hayar mace domin ta yi ramakon sallolin da suke kan mamaci, wanda kowane daga cikinsu zai yi aikin da ya rataya a kansa ne a matsayinsa na miji ko mace wajen gudanar da ayyukan sallolin da yake ramakonsu. Misali namijin da yake ramakon sallah wa mamaciya idan sallar da ake bayyana karatu ne a cikinta kamar sallar Asubahi, to zai bayyana karatunsa ne, sallar da ake boye karatu kuma ya boye, misalin sallar Azahar.Ita ma macen da take ramakon sallah ga mamaci, zata kiyaye halinta ce a matsayinta mace. Misali a ramakon sallar Asubahi zata yi karatu ne a boye kamar yadda take sallolinta na yau da kullum. Bai halatta a dauki hayar mutum mai uzuri ba domin yayi ramakon sallolin da suke kan mamaci, matukar za a samu lafiyayye da zai yi ramakon sallolin ba tare da wata matsala ba. Misali mutumin da baya iya mikewa tsaye ko wanda yake da cutar yoyon fitsari wato baya iya rike fitsari, ba za a dauke shi haya domin yayi ramakon sallolin da suke kan mamaci ba.Wajibi ne mutumin da aka dauki hayarsa kan yayi ramakon sallolin da suke kan mamaci ya kudurta niyyar yana ramakon salloli ne a madadin mamacin da ake bin sa salloli kafin ya mutu, wanda sallolin da zai yi zasu zame sun dauke nauyin da ke kan mamacin. Haka nan, wajibi ne mutumin da aka dauki hayarsa ya kudurta a zuciyarsa yana ramakon salloli ne ga wani kebantaccen mamaci. Misali yana ramakon sallah ne ga malam wane da ya dauki hayarsa kafin ya mutu ko yana ramakon sallah ne ga mahaifin malam wane da ya mutu. Wato dai, kada ya zame yana ramakon sallah ne ga mamaci ba tare da tantance mamacin ba.Idan aka dauki hayar mutum kan yayi ramakon salloli da suke kan mamaci, to zai yi sallolin ne daidai da ijtihadinsa ko takalidinsa, wanda idan rafkanuwa ko mantuwa ta auku a cikin sallar, to Dan Hayar zai yi aiki da ijtihadinsa ko takalidinsa ne wajen magance matsalar da ta auku na rafkanuwa ko mantuwa. Amma idan an gindaya wa Dan Haya sharadin cewa zai yi ramakon sallolin ne daidai da ijtihadi ko taqalidin mamaci, to dole ne yayi sallolin a kan sharadin da aka gindaya masa.Idan aka dauki hayar mutum kan yayi ramakon sallolin da suke kan mamaci kan sharadin shi da kansa ne ake son yayi ramakon sallolin, to bai halatta ya wakilta wani mutum na daban yayi ramakon sallolin ba, ta hanyar daukansa haya ko yin sallolin kyauta. Amma idan an dauki hayar mutum kan yayi ramakon sallolin da suke kan mamaci ne, ba tare da an gindaya masa sharadin sai yayi sallolin da kansa ba, to ya halatta gare shi ya wakilta wani mutum na daban yayi masa sallolin a matsayin kyauta ko kuma ya dauki hayar wanda zai yi sallolin a kan wani lada da zai biya. Sai dai a nan, akwai hukuncin Ijara da ya zame dole ya kiyaye. Wato bai halatta ladar da zai biya mutumin da ya dauki hayarsa ta kasance kasa da ladar da aka biyashi ba, sai dai idan yayi wasu sallolin da kansa; sai kuma ya dauki hayar wani mutum na daban kan ya gudanar da sauran sallolin ramakon. To a nan, ya halatta ladar da zai bayar ta kasance kasa da wadda aka ba shi kan yayi ramakon sallolin.Idan aka dauki hayar mutum kan yayi ramakon sallolin da suke kan mamaci, sai ya mutu kafin yayi ramakon sallolin, to idan an gindaya sharadin cewa shi da kansa ne zai yi ramakon sallolin, to batun haya ya rushe. Idan kuma babu sharadin sai shi da kansa ne zai yi ramakon sallolin, to za a iya daukar hayar wani mutum na daban yayi ramakon sallolin, wanda za a biya shi ladarsa daga cikin dukiyar mutumin da a fari shi aka dauki hayarsa. Idan aka dauki hayar mutum kan yayi ramakon sallolin da suke kan mamaci a tsawon wani lokaci da aka gindaya masa, misalin watanni shida, sai watannin shida suka cika ba tare da yayi ramakon sallolin ba, to anan hayar ta rushe har sai ya sake neman wani sabon izini daga wanda ya dauki hayarsa. Idan kuma ya fara ramakon sallolin wanda bai kare ba sai lokacin da aka diba masa ya cika , to nan ma dole ne ya koma ga wanda ya dauki hayarsa domin samun izinin karasa sauran sallolin da suka rage, wanda idan ya ci gaba da sallolin ba tare da samun wani sabon izini daga wanda ya dauki hayarsa ba, to bai cancanci ladar da za a ba shi ba kan sallolin da yayi bayan cikar lokacin da aka diba masa ba, duk kuwa da cewa sallolin da yayi bayan cikar lokacin da aka diba masa sun karbu a madadin sallolin da suke kan mamacin, wato dai kamar yayi sallolin ramakon ne kyauta ga mamacin.

hausa.irib.ir

Ƙara sabon ra'ayi