Sallar Rokon Ruwa

Sallar Rokon Ruwa

Sallar Rokon RuwaءAllahءMusulunciءAddiniءMohammadءAliءshiءmahdiءtvshiaء

Sallar rokon ruwa mustahabi ce a shari'a, kuma ana gudanar da sallar rokon ruwan ce sakamakon kafewar koguna ko karancin ruwan sama ko kuma lokacin da ruwan sama ya bar saukowa kwata-kwata sakamakon watsuwar sabon Allah a tsakanin mutane, kafirce wa ni'imarsa, hana masu hakki hakkokinsu, tauyaye mudu da sikeli, watsuwar zalunci, cin amana, barin umurni da kyakkyawan dabi'u da rashin yin hani da mummunar dabi'u, kin fitar da zakkah, hukunci da abin da Allah bai saukar ba da sauran ayyuka da suke janyo fushin Allah da suke sanadiyyar rashin saukan ruwan sama kamar yadda ya zo cikin ingantattun hadisan Manzon Allah {S.A.W}. Sallar rokon ruwa kamar yadda ake gudanar da sallar idi ce kuma ana gudanar da sallar ce cikin jam'i. Yadda ake gudanar da sallar rokon ruwa: Bayan kudurta niyyar sallar ta rokon ruwa, sai mutum yayi kabbarar harama, inda a raka'a ta farko zai karanta fatiha da surah, sannan yayi kabbarori biyar, inda a bayan kowace kabbara zai yi kunuti, sannan bayan gama kunuti na biyar sai mutum yayi wata kabbarar domin dukawa zuwa ga ruku'u, sannan bayan ruku'u mutum zai tafi zuwa sujjada, sannan bayan ya mike domin raka'a ta biyu, zai sake karanta fatiha da surah, sannan yayi kabbarori hudu, inda a bayan kowace kabbara zai yi kunuti, sannan bayan gama kunuti na hudu sai mutum yayi wata kabbara domin dukawa zuwa ga ruku'u, sannan bayan dagowa daga ruku'u zai duka zuwa sujjada har ya idar da sallarsa.Ya halatta a kunutin da mutum zai yi a sallar rokon ruwa yayi kowace irin addu'a, amma abin da aka fi so addu'ar ta kasance ta kunshi rokon ruwa da shayarwa daga Allah tare da neman jinkansa ta hanyar saukar da ruwan sama da bude kofofin rahamarsa dake sama. Kuma mutum ya kasance ya fara gudanar da addu'ar ce ta hanyar gabatar da yin salati ga Manzon Allah da Iyalan gidansa tsarkaka {A.S}.Yana daga cikin sunnonin sallar rokon ruwa:- -1- Bayyana karatun fatiha da surah. Mustahabi ne da aka fi so mutum ya karanta suratush-shams bayan fatiha a raka'a ta farko, sannan a raka'a ta biyu bayan fatiha ya karanta suratul-Ghashiya, ko kuma a raka'a ta farko suratul-A'alah, a raka'a ta biyu suratush-shams.-2- Yin azumin kwanaki uku a jere, inda za a fita zuwa sallar rokon ruwan a rana ta uku, kuma ranar ta uku ta kasance ranar Litinin ce, inda kuma hakan bai samu ba, to rana ta ukun ta kasance ranar juma'a saboda daukakan wannan ranar.-3- Limamin da zai jagoranci sallar rokon ruwan ya fita tare da mutane zuwa wajen gari cikin nutsuwa da kaskantar da kai ga Allah, kuma yana da kyau fitar ta kasance cikin shiga irin na tawali'u, misalin sanya kaya ba na alfarma ba da fita babu takalmi.-3- Fita zuwa sallar rokon ruwan ta kasance tare da tsoffi da kananan yara gami da dabbobi, kuma a raba kananan yara da iyayensu mata saboda su yawaita kuka da kururuwa, inda hakan zai zame sanadiyyar saukar ni'ima da jin kai cikin hanzari. Kuma a hana wadanda ba musulmi ba fita zuwa rokon ruwan tare da musulmi.-4- A fita zuwa rokon ruwan dauke da munbarin da Liman zai yi huduba a kai bayan idar da sallar, kuma ladanai su kasance a gaban Liman a tafiya zuwa wajen da za a gudanar da sallar ta rokon ruwa a bayan gari. Ana gudanar da sallar rokon ruwa ce a kowane lokaci, amma yafi kyau a gudanar da sallar a lokacin da ake gudanar da sallar Idi wato daga lokacin fitowar rana zuwa lokacin gotawarta daga tsakiyar sararin samaniya wato shigan lokacin sallar azahar.Babu kirar sallah ko ikama a sallar rokon ruwa, iyaka dai Ladan zai sanar da fara sallar ce da cewa "Assalat, Assalat sau uku.Bayan Liman ya idar da sallar rokon ruwa, mustahabi ne ya juyar da rigarsa ko mayafinsa yadda dama zai koma hagun, hagun ya koma dama. Sannan ya hau kan mumbari ya fuskanci alkibla ya daga muryarsa yayi kabbara sau dari, sannan ya juya ga gefensa na hannun dama ya daga murya yayi tasbihi ga Allah sau dari, sannan ya juya ga gefen hannunsa na hagun ya daga murya yayi hailala ga Allah sau dari, sannan ya juyo ya fuskanci mutane yayi godiya ga Allah madaukaki sau dari, kuma babu laifi mutane su yi koyi da Liman a dukkanin zikirorin da yake yi, wato duk lokacin da yayi kabbara su ma su daga muryarsu suyi kabbara, haka nan tasbihi da hailala da hamdala.Bayan gama zikiriron da muka ambata, sai Liman ya daga hannuwarsa sama yayi addu'a, su ma mutane su daga hannayensu su yi addu'a, kuma yana da kyau Liman da sauran mutane su tsananta yin addu'a tare da kaskantar da kai ga Allah madaukaki da neman jinkansa, kuma babu laifi a lokacin da Liman yake addu'ar mutane su dinga cewa amin. Sannan bayan addu'a sai Liman yayi huduba, kuma yana da kyau hudubar ta kasance daga cikin hudubobin da aka ruwaito daga shugabannin shiriya na iyalan gidan Manzon Allah {s.a.w} kuma hudubar ta kasance guda biyu kamar ta sallar idi, sai dai Liman zai yi huduba ta biyun ce a matsayin tsammmanin neman dacewa.Idan aka samu jinkirin samun ruwan, mutane zasu ci gaba da fitowa rokon ruwan har zuwa lokacin da za a samu dacewa daga wajen Allah madaukaki mai rahama mai jin kai. Idan har ba a kai ga samun ruwan ba, to hakika Allah ne mafi sanin abin da yafi dacewa ga bayinsa, mutane ba zasu nuna bijirewarsu ga Allah ko fitar da rai daga rahamarsa ba.Ya halatta mutane su ci gaba da fitawa rokon ruwa ba tsagaitawa ba tare da sun sake maimaita yin azumin kwanaki uku ba, wato azumin da suka yi tun da fari ya isar. Kamar yadda ake gudanar da sallar rokon ruwa saboda rashin ruwan sama, ya halatta a gudanar da sallar rokon ruwan saboda kafewar idon ruwa.

hausa.irib.ir

Ƙara sabon ra'ayi