Aikin Hajji {1}
Aikin Hajji {1}
Aikin Hajji.Aikin hajji ya na daga cikin rukunnan addinin musulunci kuma daya ne daga cikin wajibai da aka karfafasu a kan duk wani musulmi da ya samu ikon ziyartar kasa mai tsarki.Allah Madaukakin Sarki yana cewa:
{Kuma Allah ya dora ziyartar dakin "ka'aba" a kan mutane ga wanda ya samu ikon zuwa gareshi, kuma wanda ya kafirta, to lalle Allah mawadaci ne daga barin talikai}.Inda ma'anar kafirci a cikin wannan ayah ke nufin barin zuwa aikin hajji ga wanda ya samu iko, kuma barin zuwa aikin hajji ga wanda yake da iko kafircewa ni'imar Allah ne.Har ila yau, ya zo cikin hadisi cewa: Wanda har ya mutu bai yi aikin hajjin wajibi ba, kuma ba talauci ko rashin lafiya ko kuma hana shi zuwa aka yi bisa zalunci ba, to idan ya ga dama ya mutu bayahude ko banasare.Rabe-Raben Aikin Hajji. Aikin Hajji Nau'i Uku Ne Kamar Haka:- Nau'i na farko shi ne: Hajjin Tamattu'i.Nau'i na biyu shi ne: Hajjin Kirani.Nau'i na uku shi ne: Hajjin Ifradi.Rabe-Raben Aikin Umurah.Umurah Nau'i Biyu Ne Kamar Haka:-Nau'i na farko shi ne: Umuran Tamattu'i.Nau'i na biyu shi ne: Umuran Mufradi.Aikin Hajjin Tamattu'i shi ne wajibin da ya hau kan mutumin da yake zaune nesa da garin makkah, nisan da ya kai kilometer tamanin da takwas.Aikin Hajjin Kirani ko Ifradi shi ne wajibin da ya hau kan mutumin da yake zaune a garin Makkah da kewayensa, wato duk wanda yake zaune a cikin garin Makkah ko wajen garin da bai kai nisan kilometer tamanin da takwas ba, to aikin hajjin Kirani ko Ifradi ne ya hau kansa.Amma dangane da hukuncin aikin hajjin mustahabi ko bakance ko kuma aikin hajjin da aka yi wasici da shi, to ya halatta ga mazaunin garin Makkah da kewansa ko wanda yake nesa da garin Makkah, ya zabi duk aikin hajjin da ya dama a tsakanin nau'o'in aikin hajji guda uku da muka ambata ya aikata.Aikin umuran tamattu'i na wajibi shi ne umuran da ya hau kan mutumin da yake zaune nesa da garin Makkah, nisan da ya kai kilometer tamanin da takwas. Yayin da aikin umuran mufradi na wajibi shi ne umuran da ya hau kan mutumin da yake zaune a garin Makkah da kewayensa, wato mazauninsa bai kai nisan kilometer tamanin da takwas daga garin Makkah ba. Ganin aikin hajjin tamattu'i shi ne wajibin da ya hau kan mafi yawan al'ummomin duniya, domin su na zaune ne nesa da garin Makkah, don haka zamu yi takaitaccen bayani kan yadda ake gudanar da aikin hajjin na tamattu'i kamar haka:-Mutumin da aikin hajjin tamattu'i ne wajibin da ya hau kansa, zai fara ne da gudanar umurah, sannan ya kare da aikin hajjin tamattu'i. Wato Umarah ita ce juzu'in farko na aikin hajjinsa.Wajiban umuran tamattu'i guda biyar ne: Na farko shi ne Ihrami, na biyu Dawafi, na uku Sallar Dawafi, na hudu Sa'ayi wato tafiya tsakanin Safa da Marwa, na biyar Saisaye wato rage wani abu daga gashi ko farce.Yadda ake gudanar da aikin umuran tamattu'i a aikace shi ne: Wajibi na farko a aikin umuran tamattu'i shi ne Ihrami. Mutumin da yake da niyyar gudanar da aikin hajjin tamattu'i, zai fara ne da daura harami a daya daga cikin wajaje guda biyar da maniyyata aikin hajji ke daura harami, da ake kiran wajajen da Miqati a larabce. Kuma wajibi ne mutum ya daura haraminsa a miqatin da ta wajen ne zai shige zuwa cikin garin Makkah.Wajajen da ake daura haramin kuwa wato miqati sune kamar haka:- {1} Masjidu-Shajara wato Zu-khulaifah. {2} Juhfah. {3} Wadil-Aqiq. {4} Qarnul-Mana'zil. {5} Yalamlam.Amma maniyyata aikin hajjin da suke zuwa kasa mai tsarki ta hanyar jirgin sama dake sauka a filin jirgin saman Jiddah, ba za su daura haraminsu daga Jiddah ba, domin baya daga cikin wajajen da ake daura harami wato baya daga cikin miqati, don haka maniyyata aikin na hajji za su koma daya daga cikin miqatin da ya fi kusa da su domin daura haraminsu, misalin Juhfah ko Qarnul-Mana'zil dake Da'ifa ko Masjidu-Shajara dake Madinah.Bayan maniyyaci ya daura harami ta hanyar sanya tufafin haraminsa wato kyalle guda biyu, inda zai daura daya da zai suturce tsakanin cibiyarsa da gwiwarsa ko fiye da haka, ya kuma yi mayafi da daya, wato ya yafa kyalle daya da zai suturce kafadunsa da wani bangare na bayansa, sannan sai ya kudurta niyyar yin harama da umuran tamattu'i na hajjin wajibi domin neman kusanci da Allah. sannan ya fara talbiyya da cewa:
.Idan mutum ya daura harami, to ya zame muhrimi-wato aikata wasu abubuwa ya haramta a gareshi, misalin saduwa da mace, sumbantarta, shafan jikinta ko kallonta domin sha'awa, kamar yadda ita ma mace aikata wadannan abubuwa suka haramta gareta. Haka nan sanya turare, shafa mai, sanya tufa kewayye ga namiji, farauta da sauransu. Amma dangane da hukuncin mace wajen daura harami, tufafinta na al'ada shi ne haraminta, wato ba kamar namiji ba ne da zai daura harami ta hanyar sanya kyalle biyu.Akwai kuma wasu ayyukan mustahabbi a wajen daura harami, misalin yin wanka kafin daura harami da makamantan haka, amma tun farko mun bayyana cewa a takaice zamu yi bayanin hajji tamattu'i, don haka sai mutum ya koma ga littattafan da suka yi magana a kan aikin hajji don samun cikekken bayani.Wajibi na biyu a aikin umuran tamattu'i bayan Ihrami shi ne dawafi: Dawafi yana nufin kewaya dakin ka'aba. Yadda ake gudanar da dawafi kuwa shi ne: Mutum zai fara zagaya dakin ka'aba ne daga hajrul-aswad, dakin ka'aba yana hannunsa na hagun, sannan yayi niyyar yin dawafin umuran tamattu'i, sai ya fara zagaya dakin na ka'aba, inda zai zagaya har sau bakwai, wato idan ya fara daga wajen hajrul-aswad idan ya zagayo ya zo wajen da ya fara, yayi daya ke nan, haka har sau bakwai.Wajibi ne mutum ya gudanar da dawafin cikin tsarki kuma ya kasance cikin alwala. Haka nan mutum ya kasance cikin tsarkin jiki dana tufa. Wajibi na uku a aikin umuran tamattu'i bayan dawafi shi ne sallar dawafi: Sallar dawafi raka'a biyu ne da mutum zai yi da zarar ya gama dawafi, kuma ba dole ba ne sai mutum yayi sallar a bayan maqama-Ibrahima, ya isar masa ya gudanar da sallar a duk wajen da ya samu sarari a kusa da makama-Ibrahima.Wajibi na hudu a cikin aikin umuran tamattu'i bayan sallar dawafi shi ne sa'ayi: Sa'ayi yana nufin tafiya tsakanin safa da marwa sau bakwai. Yadda ake gudanar da shi kuwa shi ne: Mutum ya kudurta niyyar yin sa'ayi tsakanin safa da marwa na umuran tamattu'i na wajibi, sai ya fara tafiya daga safa ya zo marwa, tafiya daya ke nan, sannan daga marwa ya dawo safa, tafiya biyu ke nan, har sau bakwai, wato tafiya daga safa zuwa marwa sau hudu daga marwa kuma zuwa safa sau uku, inda cikon tafiya na bakwai zai kare a marwa.Wajibi na biyar kuma na karshe a umuran tamattu'i shi ne: Taqsir wato saisaye. Abin da ake nufi da saisaye a nan shi ne: Mutum ya aske wani abu daga cikin gashin kansa ko gemunsa ko gashin bakinsa ko kuma yanke farcen hannunsa ko na kafarsa.Wanda da haka ne mutum ya kawo karshen aikin umuran tamattu'i. Kuma abubuwan da aka haramta masa sanadiyyar daura harami, bayan gama saisaye sun halatta a gareshi, misalin saduwa da mace, sanya turare da sauransu. Sannan sai mutum ya jira lokacin daura haramin hajjin tamattu'i.
hausa.irib.ir
Ƙara sabon ra'ayi