Hukumce-Hukumcen Riba

Hukumce-Hukumcen Riba

Hukumce-Hukumcen RibaءAllahءMusulunciءAddiniءMohammadءAliءshiءmahdiءtvshiaء

to yanzu kuma zamu yi magana game da haramcin riba . sai a biyo mu sannu a hannkali. Tambaya: Manene ake nufi da Riba?Amsa: Riba shi ne siyar da wani abu tare da amsar makwafinsa amma da kari, kamar mutum ya siyar da mudun masara biyu amma a bashi mudun masara biyu da rabi. Ka ga a nan abin da aka kara akai din nan shi ne Riba .Tambaya : Shin Riba tana gudana a cikin harkokin siye da sayarwa ne kawai ko kuma tana gudana a sauran mu'amaloli .Amsa : Riba bata takaita ga bangaren siye da siyarwa ba, tana gudana a sauran mu'amaloli dake gudana a cikin rayuwar yau da kullum.Tambaya: Riba ta kasu kashi nawa ne?Amsa: Riba ta kasu kashi 2.Na daya : Ribar mu'amala ko kuma musaya. Kuma ita ce take gudana a bangaren siye da siyarwa ko kuma musaya kamar mutum ya bada kilo na masara a ba shi kilo daya da Naira goma. Ko kuma ka bada masara mudu biyu sai ka karbi kwatankwacinta yanzu amma a nan gaba kuma za'a kara masa mudu daya. Wato za'a baka wani kwatanckwacin abin da ka bayar yanzu. amma kuma za'a kara maka mudu masara ko kuma wani mikidarin kudi a nan gaba.Na biyu: Riba a shi. Ita kuma tana gudana ne a bangare ba shi kamar mutum ya bada bashin naira 100 amma idan an tashi biyan shi za'a biya shi naira 110 wanda wannan abin da ya karu a kai shi ne ake kira Riba. Tambaya : Wadanne sharudda ne idan suka cika Riba take tabbata?Amsa: sharuddan da sai sun cika Riba take tabbata guda 3 ne Na daya. Dole ne ya zamana abin da za'a yi musayar ko za'a siyar ya kasance abin da za'a iya aunawa ne a sikeli, ko kuma abin da za'a auna da Mudu , amma babu riba a cikin abubuwan da ake kirgawa ko kuma wadanda ake kimantawa da Ido bisa fatawowin wasu malamai.Na biyu: Dole ne ya zama abin da za'a yi musayar ko kuma za'a siyar su kasance iri daya ne, ko kuma jinsin su daya wato kamar tsakanin alkama da alkama ba tsakanin alkama da wake ba.Na uku: kada a samu bam-banci tsakanin jinsin da za'a yi musayar ko kuma za'a yi ciniki tsakaninsu. wato kada jinsin su ya kasance sun sha ban-bam.Tamabaya : Manene hukumcin riba kuma wadannne dalilai ne suke tabbatar da haramcin Riba Amsa : Hukumcin riba a cikin Addinin Musulunci Haramu ne kuma All.. ya la'anci wanda yaci riba ko ya zama sanadin samun ta. Amma hujjojin haramcin ta kuma kamar yadda suka zo a cikin Alkur'ani da hadisan Manzon All.. tsira da amincin All.. su tabbata gareshi da iyalan gidansa, Kuma Ayoyi 7 ne suka yi magana akan haramcin Riba a cikin Alkur'ani amma ga wasu daga cikin su, a cikin suratu Ali Imran aya ta 130 All.. madaukakin Sarki yana cewa "Ya ku wadanda kuka bada gaskiya kada kuci riba ninkin ba ninkin kuma kuji tsoron All.. don ku rabauta"Acikin suratul bakara aya ta 276 All. madaukaki yana cewa " All. yana shafe albarkar riba yana kara ladan sadaka kuma All.. baya son duk wani mai yawan butulci mai yawan sabo.To masu saurare ganin lokacin da aka dibar ma shirin ya kawo jiki ya zama wajibi in dasa aya a anan sai makkon gobe za mu kawo muku kadan daga cikin hadisan da suka yi magana akan riba amma kafin nan ni dana kasance tare daku nake cewa. Wassalamu Alaikum warahmatullah

hausa.irib.ir

Ƙara sabon ra'ayi