fatawowoin musulunci Kan Ciniki
fatawowoin musulunci Kan Ciniki
Auzu Billahi minashaidanir Rajim Bismillahir rahmanir rahim thummas salatu wassalamu ala sayyiduna wa na biyyuna Mohammad khatamunnabiyyin wa immul mursalin waalihiddyyibinad dahirin wa asahabihil muntajabin. Jama'a Assalamu Alikum barkanku da warhaka barkanmu da sake saduwa da ku a cikin shirin fatawowin musulunci wanda a cikinsa muke kawo muku hukumce-hukumcen Addini da suka kun shi mu'amalolin mu da ibadunmu. Idan masu saurare za su iya tunawa muna cikin bayani ne game da sharuddan abubuwa da ake yin siye da siyarwa akansu wato kudi da kaya ke nan. To yanzu shirin zai ci gaba amma sai an saurari wannan.Tambaya: shin akwai sharuddan da Addini ya shimfida kan abubuwan da ake siye da sayarwa da su wato kamar kaya da kudi ko kuma makwafinsu?Amsa: Na'am akwai sharudda guda 5 da Musulunci ya shimfida a kan kaya ko kudi ko kuma makwafinsu da ake siye da siyarwa akansu.Na daya: Dole ne abin da za'a yi siye da siyarwa da shi wato kudi da kaya ko kuma makwafinsu ya kasance sannan ne ta fuskacin yawa, da nauyi da dukkan siffofinsu.Na biyu: Dole ne abin da za'a yi ciniki ko siye da siyarwa da shi, su kasance ana da ikon karbansu ko kuma yin amfani da su.Na uku: Dole ne a tantance ko kuma a bayyana siffofi abubuwan da za'a yi ciniki a kan su.Na Hudu: Dole ne abubuwan da za'a yi ciniki da su ya kasance babu wani mutum na daban da yake da hakki akan su , kamar Rahan wato kudin ajiya bai halarta asiya wani abu da shi ba, ba tare da izinin mai shi ba.Na biyar: dole ne ya kasance abin da za'a yi ciniki da shi ya kasance yana da samuwa a waje ana ganin sa , idan da za' siyar da manfa'ar gidansa wato kamar amfani da za'ayi da gidansa a matsayin abin da zai bada ya sayi wani abu to da cinikin bai kullu ba, misali kamar ya siyar masa da dadduma amma zai zauna a gidansa na wani lokaci.Tambaya: idan ana amfani da kilo ko mudu wajen siye da siyarwa a wata kasa shin dole ne yayi amfani da wannan tsarin da ake bi akasarsa idan yaje siyan kaya a wata kasa ko kuma idan wani yazo kasarsa siyan kaya?Amsa: ba dole ba ne ya yi amfani da kilo ko mudu da ake amfani da shi a garinshi idan yaje siyan kaya wani gari ko kuma idan wani yazo garinsa, ya halarta yayi amfani da dukkan abin da ake amfani da shi ne a kasar ko da kuwa ta hanyar ganin da ido ne kawai.Tambaya: shin ya halarta asiyar da kayan itatuwa da furensu ke zuba da suka fara âya'ya, kafin su nuna a fara tsinkewa? Amsa: Ya halarta a siyar da âya'yan itatuwan da suka fara zubar da fure amma ba su gama nuna ba, koda ba'a tsinkesu daga jikin bishiya ba.Haka zalika ya halarta mutum ya siyar da âya'yan itatuwa kafin a tsinkesu ko da furensu basu fara zuba ba. Amma da sharadin zai hada da wani abu da za'a iya sayar da shi, koda shi kadai ne.Tambaya: shin ya halarta a siyasar da zangarniyar hatsi kamar alkama da sha'ir bayan ta fara fitar da âya'ya? Amsa: ya halarta a sayar da zarganniyar hatsi na alkama ko na sha'ir bayan ta fara fitar da âya'ya amma da sharadin abin da za'a bayar a Makwafinshi ya Kasance wani Abu ne na daban ba na hatsi ba. To Masu saurare ganin lokacin da aka dibar shirin ya kawo jiki anan zan yi bankwana daku sai amakon gobe sai aboyo mu domin jin ci gaba shirin sai dai kafin nan nake cewa wasalamu Alikum warhmatullahÂ
hausa.irib.ir
Ƙara sabon ra'ayi