Hadin Gwuiwan Kungiyoyin Palastinawa Sun Jinjinawa Wa Jagora

Hadin Gwuiwan Kungiyoyin Palastinawa Sun Jinjinawa Wa Jagora

Hadin Gwuiwan Kungiyoyin Palastinawa Sun Jinjinawa Wa Jagora  Hadin gwuiwan kungiyoyin gwagwarmayar Palastinawa sun aike wa Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei da sakon godiyarsu a gare shi saboda irin goyon bayan da yake ba wa al’ummar Palastinu wajen fada da wuce gona da irin yahudawan sahyoniya a kan al’ummar Gaza. A cikin wata sanarwa da suka fitar a yau din nan juma’a kungiyoyin  sun ce suna isar da godiya da kuma jinjinawarsu ga Ayatullah Khamenei saboda matsayar da yake dauka da kuma jajircewa da ya yi wajen goyon bayan al’ummar Palastinu. Har ila yau hadin gwuiwan kungiyoyin Palastinawa sun bayyana jin dadi da kuma godiyarsu ga Iran da al’ummar kasar saboda irin goyon bayan da suke bawa kungiyoyin gwagwarmayar Palastinawan suna masu cewa wannan goyon bayan ya taimaka nesa ba kusa ba wajen nasarar da al’ummar Gazan suka samu a kan HKI. Wadannan kungiyoyin dai sun hada da Jabhatish Sha’abiyya Li Tahrir al-Palastine –Qiyadatul amma, Jabhatul Nidha al-Sha’abi al-Palastini, Munazzimat al-Sahhiqa, Al-Hizb al-Shuyu'i al-Palastini, Harkat al-Fath al-Intifadha, Jabhat al-Tahrir al-Palastine, bugu da karin kan kungiyoyin Hamas da Jihad al-Islami.ءAllahءMusulunciءAddiniءMohammadءAliءshiءmahdiءtvshiaء

Hadin gwuiwan kungiyoyin gwagwarmayar Palastinawa sun aike wa Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei da sakon godiyarsu a gare shi saboda irin goyon bayan da yake ba wa al’ummar Palastinu wajen fada da wuce gona da irin yahudawan sahyoniya a kan al’ummar Gaza.
A cikin wata sanarwa da suka fitar a yau din nan juma’a kungiyoyin  sun ce suna isar da godiya da kuma jinjinawarsu ga Ayatullah Khamenei saboda matsayar da yake dauka da kuma jajircewa da ya yi wajen goyon bayan al’ummar Palastinu.
Har ila yau hadin gwuiwan kungiyoyin Palastinawa sun bayyana jin dadi da kuma godiyarsu ga Iran da al’ummar kasar saboda irin goyon bayan da suke bawa kungiyoyin gwagwarmayar Palastinawan suna masu cewa wannan goyon bayan ya taimaka nesa ba kusa ba wajen nasarar da al’ummar Gazan suka samu a kan HKI.
Wadannan kungiyoyin dai sun hada da Jabhatish Sha’abiyya Li Tahrir al-Palastine –Qiyadatul amma, Jabhatul Nidha al-Sha’abi al-Palastini, Munazzimat al-Sahhiqa, Al-Hizb al-Shuyu'i al-Palastini, Harkat al-Fath al-Intifadha, Jabhat al-Tahrir al-Palastine, bugu da karin kan kungiyoyin Hamas da Jihad al-Islami.

hausa.irib.ir

Ƙara sabon ra'ayi