Kasar Masar Ta Sake Fadawa Cikin Wata Sabuwar Dambarwar Siyasa

Jama’a masu saurare Assalamu Alaikum barkanku da warhaka, barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na Afirka a mako, inda muke kawo muku wasu daga cikin muhimman abubuwa da suka faru a wannan nahiya a cikin mako, a yau ma da yardar Allah za mu leka kasashen Masar, Mali, Tarayyar Najeriya, Guinea Bissau, Zimbabwe  da kuma Burkina Faso.

 

Masar

 

To ba ri mu fara shirin namu na yau daga kasar Masar, inda tun a ranar Lahadi da ta gabata ce miliyoyin mutanen kasar suka fara gudanar da zanga-zanga da aka ce ita ce mafi girma a tarihin kasar Masar, domin nuna adawa ga shugaban kasar Muhammad Morsi, tare da kiransa da ya safka daga kan karagar shugabancin kasar.

 

Ana gudanar da zanga-zangar ne a dukkanin biranan kasar ta Masar, inda aka cika dukkanin wuraren taruka na mayan birane musamman ma dandalin Tahrir da kuma yankin Ittihadiyya da ke kusa da fadar shugaban kasa a birnin Alkahira, miliyoyon masu zanga-zanga sun cika wuraren suna rera taken kira ga Morsi da ya safka.

 

A daya bangaren wasu daga cikin magoya bayan Morsi sun taru a masallacin Rabi'at Adwiyyah da ke birnin Alkahira domin nuna goyon bayansu, rahotanni sun ce an kashe masu adawa da Morsi 5 a ranar Lahadi a biranan Asyut, Afyum da kuma Alkahira yayin da wasu kimanin 200 suka samu raunuka.

 

Rundunar sojin kasar Masar dai ta ce tana bin diddigin abin da ke gudana, kuma za ta dauki matakan da suka dace matukar dai suka ga kasar za ta shiga wani hali na yakin basasa.

 

 

Najeriya

 

A can tarayyar Najeriya kuwa wani rikici ne aka yi tsakanin Fulani da kuma wasu mutane da ke yi musu saar shanu a wasu kauyuka da ke cikin karamar hukumar Lantang da ke cikin jahar Plateau, lamarin da ya kai ga kashe mutane akalla 32 kamar yadda mahukunta suka fada, mun tuntubi shugaban karamar hukumar ta Lantang Nanman Darko.

 

Zimbabwe

A can kasar Zimbabwe kuwa, shugaban kasar Robert Gabriel Mugabe da firayi ministan kasar Morgan Richard Tsvangirai sun yi rajistar sunayensu domin tsayawa takarar neman shugabancin kasa, wanda shi ne karu na uku da za su mutanen biyu za su kara da juna a zaben shugaban kasa.

Robert Gabriel Mugabe da Morgan Richard Tsvangirai, ta hannun wakilan jam'iyyunsu, sun mika takardun nasu ne zuwa ga kotu da ke karbar sunayen 'yan takarar ne ta hanyar wakilansu tun a ranar 28 ga watan Yunin da ya gabata, haka nan kuma kotun ta samu takardar ministan masana'antu da kasuwanci Welshman Ncube.

Tun a kwanakin baya ne dai shugaba Mugabe ya sanar da ranar 31 ga wanann wata na Yuli a matsayin ranar da za a  gudanar da zaben shugaban kasa a kasar ta Zimbabwe, amma Firayi minista Morgan Tsvangirai bai amince da hakan ba saboda bai shirya ba, amma kotun tsarin mulkin kasar ta tana yin dubi a kan batun, domin amincewa ko kuma kuma yin watsi da hakan.

 

Guinea Bissau

 

To har wala yau dai muna nan kan batun na zabe dai, amma a wannan karon a kasar Guinea Bissau, inda fadar shugaban kasar ta bayar da sanarwa cewa, za a  gudanar da zaben shugaban kasar da na 'yan majalisa a ranar 24 ga watan Nuwamba na wannan shekara.

Sanarwar ta nuna cewa, bayan tattaunawa tsakanin shugaban rikon kwarya da jam'iyyu da kungiyoyi daban-daban na kasar, daga bisani shugaban kasar Raimundo Pereira ya tabbatar da lokacin yin zabe, sanarwar ta ce, hukumar zabe ta kasar ta tabbatar da cewa lokacin da aka tsayar domin gudanar da zaben ya dace.

Tun daga farko dai an shirya gudanar da zabukan ne a watan Mayun da ya gabata, kafin daga bisani a dage lokacin gudanar da zabukan, saboda abin da hukumar zaben ta kira rashin cikakken shiri domin gudanar da zaben, amma jam'iyyun adawa sun dora alhakin hakan kan shugaban kasar, inda suka ce yana jan lokaci ne kawai domin ya ci gaba da zama kan kujerar shugabancin kasar.

 

Burkina Faso

To a kasar Burkina Faso kuwa 'yan sanda ne suka yi amfani da barkonon tsohuwa wajen tarwatsa wasu masu zanga-zangar nuna rashin amincewa da shirin gwamnatin kasar na kirkiro majalisar dattawa, inda suke ganin hakan a matsayin kokarin shugaban kasar Blaise Compaore na kara wa’adin mulkinsa na shekaru 26 a kasar.

 

Rahotannin sun ce ‘yan sandan sun fada wa masu zanga-zangar wadanda suke dauke da kwalayen da aka rubutu a kansu na kalmomin nuna rashin amincewa da ci gaba da mulkin kasar da shugaba Compaoren yake yi, a daidai lokacin da suka ketare wasu shingai da ‘yan sandan suka kakkafa. Shugaban ‘yan adawa na kasar dai Zephirin Diabre ya ce da dama daga cikin masu zanga-zangar sun sami raunuka.

 

Gwamnatin kasar Burkina Fason dai tana shirin kirkiro da majalisar dattawan ne a watan Satumba mai zuwa don kara karfafa tsarin demokradiyya a cewarta, sai dai ‘yan adawan suna ganin shugaba Compaore wanda yake kan karagar mulkin kasar tun shekarar 1987 zai iya amfani da hakan wajen soke wata doka da ta takaita mulkin nasa bayan zaben shekara ta 2015.

 

Mali

 

Daga kasar Burkina faso bari mu leka makwabciyarta kasar Mali, inda ofishin hukumar kula da 'yan gudun hijra na Majalisar Dinkin Duniya (UNHCR) ne  ya bayyana cewa zai  kara himma a kan ayyukan taimaka wa kasashe masu makwabtaka da kasar Mali,  domin taimaka wa 'yan gudun hijira na kasar Mali da ke cikin kasashensu su jefa kuri'a kafin 28 ga watan Yuli, wato ranar da aka ayyana domin gudanar da zaben shugaban kasa a Mali.

Bayanin ya ce akwai 'yan kasar Mali da suke gudun hijira a kasashen Burkina Faso, Nijar da Mauritaniya, wadanda yawansu ya kai mutane dubu 175, wadanda suka gudu suka bar gidajensu a yankunan arewacin Mali domin kauce wa gumurzun da aka yi tsakanin mayakan 'yan tawaye da kuma sojoin Faransa na da kasar Mali a cikin yankunansu.

Shugaban ofishin  na hukumar  kula da 'yan gudun hijra na Majalisar Dinkin Duniya (UNHCR) Mr Del Buey ya bayyana cewa, hukumar na taimakawa wajen ganin 'yan gudun hijiran sun gudanar da zaben, duk da cewa ayyukanta na jin kan bil Adama ne ba na siyasa ba.

Zaben kasar Mali mai zuwa yana da muhimmanci wajen maido da martabar kasar da kuma mulki bisa tsari na dimokradiyya, bayan juyin mulkin sojoji suka jagoranta a kasar a ranar 22 ga watan Maris na shekarar data gabata, wanda kuma hakan ne ya haifar da shigowar 'yan tawaye da ke da alaka da kungiyar Al-Qaida a arewacin kasar Mali, inda suka kwace iko da yankunan na tsawon watanni.

 

Ƙara sabon ra'ayi