Afirka A Mako
Jama'a masu saurare assalamu alaikum barkanmu da yau da kuma sake saduwa da ku a cikin wani sabon shiri na Afirka a mako, shirin da a cikinsa muke bitar wasu daga cikin muhimman batutuwan da suka faru ko kuma ke kan faruwa a cikin kasashen nahiyar Afirka, sai a biyo mu domin jin cikakken shirin wanda a yau zai kai mu kasashen Nijar, Najeriya da kuma Ghana. ....................Kida........................ To madalla, a cikin makon da ya gabata ne aka gudanar da bukukuwan cika shekaru 52 da samun 'yancin-kai a jamhuriyar Nijar bukukuwan da ake yin amfani da su domin yin dubi a game da matsayin kasar wacce take daya daga cikin kasashen da Faransa ta yi wa mulkin mallaka, yayin da a wannan rana ake gudanar da dashen itatuwa a sassa daban-daban na kasar domin yaki da matsalar gurgusowar Hamada. Har ila yau a lokacin bikin na bana, an bayar da lambobin girmamawa ga mutanen da suka taka wata rawa ta a-zo-a-gani wajen ciyar da kasar gaba, yayin da kuma aka bayar da wata lambar yabo ga tsohon shugaban tarayyar Najeriya kuma mai shiga tsakanin da kungiyar Ecowas ta nada domin warware rikicin siyasa na Tazarce a kasar ta Nijar wato janar Abdussalami Abubakar mai ritaya a game da abin da hukukomin kasar ta Nijar suka ce kokarinsa wajen dawo da dimokuradiyyar a kasar. A jajibirin zagayowar wannan rana ta samun 'yancin-kai, shugaban kasar Alhaji Isufu Mahammadu ya gabatar da jawabi ga 'yan kasar inda kuma ya ambaci abubuwa da dama, wakilinmu na Maradi Salisu Isa ya saurari jawabi ya kuma fassara mana wani bangare na wannan jawabin. .............................Salisu Isa................... A cikin makon da ya gabata ne ministar ma'aikatar kudi ta tarayyar Najeriya Dr Ngozi Ikonjo-Ewela ta gabatar da kanta a gaban Majalisar Dattawa ta kasar domin amsa tambayoyin 'yan Majalisar dangane da dalilanda suka sa gwamnati ke yin tafiyar hawainiya wajen aiwatar da kasafin kudin kasa na wannan shekara. An dai yi cacar baki matuka tsakanin ministar da kuma 'yan Majalisar dangane da wannan batu, yayin da ministar ke cewa gwamnati ta aiwatar da kasafin kudin da kimanin 52%, su kuwa 'yan Majalisar sun ce ko kadan abin da aka aiwatar bai kai haka ba. Dr Yerima Lawan Ngama shi ne karamin minista a ma'aikatar kudi ta kasar, ya yi wa wakilinmu na Abuja Karin bayani a game da abin da ke kawo tafiyar hawainiya wajen zartas da kasafin kudin na bana. .............................Ministan Kudi..................... To bari mu je kasar Ghana, inda bayan mutuwar tsohon shugaban kasar John Atta Mills da kuma rantsar da mataimakinsa a matsayin sh ugaban kasa, a nashi bangare kuwa sabon shugaban kasar Dakta Dramani Mahama ya zabi wanda zai zame mishi a matsayin mataimaki kamar dai yadda kundin tsarin mulkin kasar ya shata. A ranar litinin da gabata ne dai sabon mataimakin shugaban kasar Mista Kwesi Amissah-Arthur ya bayyana a gaban Majalisar Dokokin kasar domin tantance shi kamar dai yadda dokokin kasar suka shata. Wakiliyarmu ta Accra Halima Kadri Ingilishi ta aiko mana da wannan rahoto. ...................Ghana................ To bari mu sake komawa a Tarayyar Najeriya inda yanzu haka batun nan na bai wa jihohi damar kafa rundunonin 'yan sanda mallakinsu yake ci gaba da daukar hankulan jama'a. A game da hakan ne ma wakilinmu na Abuja Mhd Sani Abubakar ya nemi jin ta bakin babban sipeton 'yan sanda na kasar Muhammad Dahiru Abubakar a game da wannan batu ga kuma Karin bayanin da ya yi masa. ........................IGP....................... To bari mu rufe shirin na yau da ziyarar da Sakatariyar harkokin wajen kasar Amurka Hillary Cliton ta kai a kasashe 6 na nahiyar Afirka a wannan mako da muke bita. Daga cikin kasashen da ta ziyarta kuwa har da Senegal, Unganda, Sudan ta Kudu, Kenya, Malawi da kuma Afirka ta kudu. A duk inda ta ziyarata dai, Hillary Cliton ta fi mayar da hankali ne kan batutuwan tsaro da kuma barazanar da ta ce ayyukan ta'addanci na yi wa duniya. Da ma dai wannan batu na ta'adda shi ne babban makami da Amurka ke amfani da shi domin ci gaba da mamaye kasashen duniya musamman ma masu tasowa. ........................Kida............. To jama'a masu saurare duka duka a nan ya kamata mu yi sallama da ku a cikin wannan shiri na Afirka a mako, sai kuma mako na gaba idan Allah ya kai mu za a ji mu dauke da wani sabon shiri, wassalamu alaikum a huta lafiya.
Ƙara sabon ra'ayi