Harin Ta'addanci A Birnin Nairobi Na Kasar Kenya

Jama’a masu saurare Assalamu Alaikum barkanku da warhaka, barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na Afirka a mako, inda muke kawo muku wasu daga cikin muhimman abubuwa da suka faru a wannan nahiya a cikin mako, a yau ma da yardar Allah za mu leka kasashen Kenya, Masar, Najeriya, Nijar, da kuma Guinea Conakry gwargwadon yadda lokaci ya ba mu hali. To bari mu fara shirin namu daga kasar Kenya, inda a cigaba da halin kiki- kaka da ake ciki a babban birnin kasar Nairobi, jami’an tsaron kasar sun sanar da kashe biyu daga cikin masu garkuwa da mutane a cikin cibiyar kasuwanci ta Westgate, Ministan harkokin cikin gidan kasar Kenya Joseph Ole Lenku ya sheda cewa; bayan kashe mutanen biyu an kuma jikkata wasu daga cikinsu. Maharan da su ka kutsa cikin babban shagon Westgate da ke cikin birnin Nairobi tun a ranar asabar, sun fito ne daga cikin kasashen daban-daban kamar yadda  kwamandan sojojin kasar ta Kenya ya bayyana. Kafafen watsa labarun Amurka ma sun bayyana cewa da akwai Amurkawa biyu a tsakanin maharani da ke karkashin inuwar kungiyar al-shabab na kasar Somaliya. Kawo ya zuwa yanzu an tabbatar da kashe mutane 69 da su ka hada da Amurkawa da ‘yan kasashen turai da dama, sai dai mafi yawancinsu ‘yan kasar Kenya ne.   To daga gabacin Afirka bari mu nufi yammacinta, inda za mu fara yada zango a tarayyar Najeriya, inda a cikin makon nan ne jami’an tsaro suka kaddamar da wani farmaki a kan wani gidan haya a birnin Abuja, inda suka kashe tare da jikkata mutanen da ke cikin gidan tare da yin awon gaba da wasu, bisa zargin da jami’an tsaron suka yi kan cewa mutanen gidan ‘yan kungiyar Boko Haram ne, wanda daga bisani ta bayyana cewa ‘yan ci rani ne da suka zo birnin domin neman na sakawa a bakin salati, akasarinsu kuma suna kabo-kabo ne kekenapel, babban sakataren birnin Abuja John Chuku ya bayyana takaicin gwamnati kana bin da ya faru, tare da shan alawashin kula da wadanda suka samu raunuka da kuma kai dukkanin gawawakin wadanda suka mutu zuwa ga iyalansu a garuruwansu, haka nan kuma ya ce za a gudanar kwakwaran bincike kan lamarin   To a bangare guda kuma wasu kungiyoyin kare hakkin bil adama a Najeriya sun kudiri aniyar bin kadun abin da ya faru dangane da wannan kisa da jami’an tsaro suka yi wa wadannan mutane, da hakan ya hada da neman a kame tare da gurfanar da jami’an tsaron da suka aikata hakan tare da hukunta su. A bangare guda kuma an gudanar da wani jerin gwano a birnin Kaduna wadda kungiyoyi fiye da 50 suka halarta, da nufin yin kira ga al’ummar kasar su zauna lafiya da juna, domin ci gaban kasar da zaman lafiyarta, daga cikin kungiyoyin da suka halarci gangamin har da mabiya addinin kirista da kuma na musulmi, Postor Yuhana Buru daya ne daga cikin limaman addinin kirista a Najeriya da ke fadi tashin ganin an samu kyakkayawar alaka da fahimta tsakanin mabiya addinan kiristanci da muslunci, ya bayyana manufar zanga-zangar da cewa ita ce neman samun zaman lafiya mai dorewa tsakanin dukkanin al’ummomin Najeriya baki daya. A Jamhuriyar Nijar kuwa, ‘yan majalisar dokokin jahar Damagaram ne suka karba goron gayyata da takwarorinsu na jahar kano suka aike musu, domin gayyatarsu zuwa Kano tare da ganin irin ayyukan da suke gudanarwa, da kuma sanin hanyoyin da bangarorin biyu za su yi aike tare domin ci gaban al’ummomin tare da kara dankon zumunci a tsakaninsu   A kasar Masar kuwa Wata kotu ce ta bayyana kungiyar ‘yan ’uwa musulmi a matsayin haramtacciyar kungiya. Babban mai shari’a na kasar ya sanar a ranar litinin cewa kungiyar ta ‘yan’uwa musulmi da dukkanin rassanta, haramtattu ne kuma gwamnati za ta kwace dukkanin dukiyar da  ‘ya’yan kungiyar suka  mallaka. Jim kadan bayan fitar da wannan hukunci, jami’an tsaro sun ci gaba da kame manyan jagororin kungiyar, mutum na bayan nan da aka kama dai shi ne Salahuddin Abdulhalim Sultan, wanda ya taka gagarumar rawa wajen jagorantar Zanga-zangar nuna kin amincewa da  kifar da gwamantin Muhammadu Mursi. To daga Masar bari mu leka Guinea Conakry, inda a kalla mutum guda  ya rasa ransa a taho mu gama  tsakanin magoya bayan gwamnatin kasar da kuma ‘yan hamayyar siyasa. Raotannin daga kasar sun ce an yi taho mu gama ne a tsakanin masu yakin neman zabe na jam’iyyar da ke mulki a kasar da kuma sauran jam’iyyun adawa na siyasa, lamarin da ya yi sanadiyyar mutum guda tare da jikkatar wasu 51. Tun a daren Lahadin da ta gabata ne dai aka fara rikici a tsakanin bangarorin biyu, bayan da  gwamnatin kasar ta bayyana  amincewarta da bukatar ‘yan hamayya na dage lokacin yin zabe daga ranar 14 ga wannan watan na Satumba zuwa 28 gare shi. An shirya cewa za a gudanar da zaben ‘yan majalisar dokoki ne watanni shida bayan zaben shugaba Alfa Konde a cikin watan satumba na 2010, sai dai an rika dage lokacin yin zaben. To jama’a masu saurare a nan za mu ja linzamin shirin namu, saboda lokacin da muke da shi ya kawo jiki, sai idan Allah mai kowa da komai ya kai mu mako na gaba za a ji mu dauke da wasu daga cikin abubuwan da suka faru a nahiyar Afirka, kafin lokacin a madadin wadanda suka hada mana sautin shirin har ya kammala, nake yi muku fatan alkhairi, wassalamu alaikum wa rahmatullah.  
 
 

Ƙara sabon ra'ayi