Dan Ta'addan Da Ya Datse Kawunan Mutane 378 A Kasar Siriya Ya Halaka A Garin Lazikiyy

Sojojin gwamnatin Siriya sun samu nasarar halaka dan ta‘addan nan da ya yi kaurin suna a fagen datse kawunan jama’a a kasar mai suna Abu-Walid.

 

A ci gaba da gagarumar nasarar da sojojin gwamnatin Siriya ke samu a kan ‘yan ta’addan kasa da kasa da aka jibge a cikin kasar ta Siriya; Sojojin gwamnatin Siriya sun samu nasarar halaka da dama daga cikin ‘yar kungiyar Jabhatun-Nusrah musamman a garuruwan Lazikiyya, Halab da gefen birnin Damasqas fadar mulkin kasar a cikin ‘yan kwanakin nan, cikin ‘yan ta’addan da suka halaka a garin Lazikiyya har da shahararren dan ta’addan kasar Checheniya nan mai suna Abu-Walid Muslim da aka kiyasta cewa ya datse kawunan jama’a kimanin 378 a sassa daban daban da ke karkashin ikon kungiyoyin ‘yan ta’adda da suke cikin kasar Siriya.

Shafin Internet na Alhadas News ya habarta cewar Abu-Walid ya shiga cikin kasar Siriya ce ta kan iyakar kasar da Turkiyya a watan Mayun shekara ta 2012 kuma yana yaki ne karkashin kungiyar Jabhatun-Nusrah ta masu tsaurin ra’ayin Islama, inda ya yi kaurin suna a fagen datse kawunan mutane da ba su goyon bayan ‘yan ta’adda da suke cikin kasar.

Ƙara sabon ra'ayi