Sojojin Syria Sun Kwace Wasu Yankuna Masu Matukar Muhimmanci Daga 'Yan Ta'adda

Rahotanni daga kasar Syria sun ce dakarun kasar sun samu nasarar kwace iko da wasu yankuna masu matukar muhimamnci daga hannun mayakan ‘yan bindiga, bayan kwashe tsawon kawanaki ana gumurzu tsakanin bangarorin biyu.

 

Dan rahoton tashar talabijin ta Al-alam daga kasar Syria wanda ya kasance tare da sojojin na Syria ya bayar da rahoton cewa, dakarun na kasar Syria sun yi wa daruruwan bindiga kofar raggo a yankunan Hatita Turkman da ke karakshin iko ‘yan bindiga wadanda kasashen yamamcin turai gami da Saudiyya da Qatar suke marawa baya, inda suka samu nasarar kashe adadi mai yawa daga cikinsu, wasunsu kuma suka tsere, inda ya zuwa yammacin jiya dukkanin yankunan Hatita suka dawo karshin ikon hukuma.

Wasu rahotannin kuma daga kasar ta Syria sun tabbatar da cewa a jiya an yi wata musayar wutar mai tsanani tsakanin mayakan kurdawa da kuma ‘yan alka’ida a a kan iyakokin Syria da Iraki, bayan da ‘yan alkaida suka nemi shiga cikin kasar ta Syria ta kauyen Ya’arabiyya da ke kan iyakar Syria da Iraki, wanda galibin mazauna cikin sa Kurdawa ne, rahoton ya ce mayakan kuradawan sun hallaka mayakan alkaida da dama, lamarin da ya tilasta su komawa cikin kasar ta Iraki.

Ƙara sabon ra'ayi