Kotun Kasar Bahrain Ta Aike Wa Jagoran Aadawar Siyasa A Kasar Da Sammaci

Jami’an tsaro a kasar Bahrain sun bukaci babban sakataren babbar gamayyar jam’iyyu da kungiyoyi masu adawa ta Al-wifaq sheikh Ali Salman da ya kai kansa gobe Lahadi a gaban babbar kotun kasar da ke birnin Manama.

 

Kakakin jam’iyyar Alwifaq Majid Milad ne ya bayyana hakan a yammacin yau, inda ya ce jami’an tsaron sun aiko da wata takarda zuwa ga sheikh Ali Salman, da a cikinsa suka bayyana shi a matsayin wanda ake tuhuma, amma ba tare da bayyana bain da ake tuhumarsa da aikatawa ba.

A ranar laraba da ta gabata ce jami’an tsaro a cikin kayan sarki dauke da manyan bindigogi da motoci masu sulke, suka kai farmaki kan ofishin gamayyar jam’iyyun adawa ta kasar, inda suka lalata ofishin tare da sace kaddarorin da ke cikinsa ba tare da bayyana dalilin yin hakan ba.

Tun a cikin watan Fabrairun shekara ta 2010 ne al’ummar kasar Bahrain suke bukatar mahukuntan kasar da su gudanar da sauye-sauye na demokradiyya a cikin harkokin mulkin mulukiya na kasar, amma masarautar kasar tare da taimakon gidana sarautar Saudiyya da hadaddiyar daular larabawa gami da kasashen turai musamman ma Amurka, sun dauki matakin murkushe duk wani yunkurin neman gyara ta hanyar lumana da al’ummar kasar suke yi , inda ake yin amfani da karfin bindiga domin murkushe su.

Ƙara sabon ra'ayi