Iran A Mako 7-11-2013

Masu saurare assalamu alaikum barkanmu da warhaka da kuma sake saduwa cikin wani sabon shirin Iran A Mako da ke leko muku wasu daga cikin muhimman al’amurran da suka faru a Iran cikin mako wanda ni Muhammad Awwal Bauchi na saba gabatar muku da shi da fatan masu saurare suna cikin koshin lafiya.

 

 

Kamar yadda muka saba ga wasu daga cikin muhimman al’amurran da suka farun kana mu yi karin haske kansu daga baya.

 

Daga cikin lamurran da suka dau hankula cikin makon har da jawabin da Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya yi a yayin ganawa da daliban makarantu don tunawa da zagayowar ranar kasa ta fada da girman kan duniya inda ya yi karin haske kan batun tattaunawa tsakanin iran da Amurka, wannan shi ne lamarin da shirin na mu na yau zai fi ba shi muhimmanci. A bangaren shirin nukiliya kuwa batun da ya fi daukan hankula shi ne batun tattaunawa ta masana da ta gudana tsakanin Iran da manyan kasashen duniya a birnin Geneva. Sai kuma ziyarar da shugaban majalisar shawarar Musulunci Ali Larijani ya kai kasar China bisa gayyatar takwaransa na Chinan, da kuma wanda ministan harkokin wajen Iran ya kai Turkiyya don tattaunawa kan batutuwa daban-daban musamman rikicin kasar Siriya A bangaren tattalin arziki kuma daga cikin lamurran da suka dau hankula akwai taron hadin gwiwa tsakanin Iran da Afirka ta kudu sai kuma ziyarar da ministan man fetur na Iran ya kai kasar Rasha da kuma taron kungiyar kasashe masu arzikin iskar gas da aka gudanar a nan Tehran. A bangaren ilimi kuwa lamarin da ya dau hankali shi ne batun nasarar da likitocin Iran suka samu a fagen cutar ciwon ido.

 

Wadannan watakila da ma wasunsu suna daga cikin lamurran da za mu yi dubi cikinsu a shirin na mu na yau. Sai a biyo mu sannu a hankali.

 

-----------------------------------------/

 

Masu saurare barkanmu da sake saduwa.

 

Kamar yadda watakila kuka ji a farkon shirin a safiyar ranar Lahadin da ta gabata ce Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya gana da dubban daliban makarantu da jami’oin Jamhuriyar Musulunci ta Iran don tunawa da ranar kasa ta fada da girman kan duniya inda ya yi karin bayani dangane da dalilan da ya sanya ma’abota girman kan duniya adawa da al’ummar Iran, kamar yadda kuma ya yi karin haske kan batun shirin tattaunawa da Amurka da gwamnatin Iran take yi kan shirin nukiliyan zaman lafiya na kasar inda ya ce: a ranar 13 ga watan Aban 1358 (1979) matasan Iran sun sanya wa ofishin jakadancin Amurkan sunan shekar leken asiri. A yau bayan gushewar sama da shekaru talatin, sai ga shi ana kiran ofisoshin jakadancin Amurka a kasashen Turai, wadanda abokan Amurkan ne ma, da sunan shekar leken asiri. Hakan lamari ne da ke nuni da cewa matasanmu suna gaba da duniya da shekaru talatin da wani abu wajen fahimtar wannan lamarin.

 

Haka nan kuma yayin da yake jaddada cewa gwamnatin Amurka gwamnatin girman kai ce wacce take ganin kanta a matsayin wacce take da hakkin tsoma baki cikin lamurran cikin gidan wasu kasashe, Ayatullah Khamenei cewa ya yi: A hakikanin gaskiya al’ummar Iran sakamakon wannan juyin juya hali na su sun tabbatar da tsayin dakan su na rashin yarda da wannan girman kai na Amurka, sannan kuma bayan nasarar juyin juya halin Musuluncin sun gutsure tushen wannan girman kan a cikin gidansu, sannan kuma sabanin wasu kasashen, ba su bar gyauron wannan tushen ba, ballantana daga baya ya cutar da su.

 

Har ila yau kuma yayin da ishara da cewa babu wani amfani da kasashe da al’ummomin duniya za su samu sakamakon mika kansu ga ma’abota girman kan, Ayatullah Khamenei cewa ya yi: Irin mu’amala da girman kan Amurka ne ya sanya al’ummomin duiya kyama da kuma rashin yarda da ita, baya ga cewa tarihi ya tabbatar da cewa duk wata al’umma ko wata gwamnatin data dogara da Amurka, to kuwa ta sha kashi koda kuwa tana daga cikin kawayen Amurkan ne.

 

A wani bangare na jawabin nasa, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya yi magana kan batun tattaunawar da ake shirin yi tsakanin Iran da Amurka inda ya yi karin haske kan dalilan gabar da Amurka take yi da al’ummar Iran inda ya ce: tarihin Amurka da kuma halayenta sun tabbatar da cewa batun nukiliya wani lamari ne kawai da take fakewa da shi wajen ci gaba da adawar da take yi da Iran. A saboda haka bai kamata wani ya yaudaru da sakin fuska ta yaudara da makiya suke yi ba. Idan har (tattaunawar da ake yi din) ta haifar da da mai ido, to me ya fi hakan, idan kuwa ba haka ba, to hakan yana tabbatar da maganganun da muka sha yi ne na cewa za a iya magance matsalolin da ake da su ne kawai ta hanyar dogaro da kai.

 

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya kore maganganun da wasu suke yi na cewa tattaunawar da ake yi tsakanin Iran da manyan kasashen duniya ciki kuwa har da Amurka ta kumshi wasu batutuwa na daban baya ga batun nukiliya inda ya ce batun nukiliya shi ne kawai batun da ake tattaunawa kansa, kamar yadda kuma ya sake jaddada matsayar Iran kan HKI da cewa haramtacciyar kasar Isra’ila dai wata kasa da gwamnati ne maras halalci.

 

Ita dai wannan ranar ta fada da girman kan duniya ana gudanar da ita ce a duk ranar 13 ga watan Aban (4 ga Nuwamba) don tunawa da wasu muhimman al’amurran guda uku da suka faru a Iran wadanda kuma Amurka ta ke da hannu cikinsu. Na farkonsu shi ne tilasta wa marigayi Imam Khumaini (r.a) gudun a shekarar 1964 saboda jawabin da ya yi na adawa da dokar kariya da gwamnatin Shah (ta wancan lokacin) ta ba wa sojoji da ma’aikata Amurkawa da suke Iran. Na biyu kuma shi ne kisan gillan rashin imani da jami’an tsaron gwamnatin kama karya ta (Shah) da take samun goyon bayan Amurka suka yi wa daliban makarantu a Tehran a shekara ta 1978 sai kuma na uku yunkuri na jaruntaka da daliban jami’a mabiya tafarkin marigayi Imam suka yi na kame ofishin jakadancin Amurka a shekarar 1979.

 

--------------------------------------------/

 

Masu saurare barkanmu da sake saduwa.

 

A makon da ya gabata ne aka gudanar da zaman tattaunawa ta kwararru tsakanin Iran da manyan kasashen duniya, wadannan ake kira da kungiyar 5+1 wato Rasha, China, Birtaniya, Faransa, Amurka da Jamus a birnin Vienna a ci gaba da tattaunawar da ake yi tsakanin bangarorin biyu da nufin kawo karshen matsalar da ke tsakanin Iran da wadannan kasashe kan nukiliyanta na zaman lafiya.

 

Ita dai wannan tattaunawar an gudanar da ita ne tsakanin masanan bangarorin biyu don tattaunawa kan shawarwarin da Iran ta gabatar kan yadda za a bi wajen magance wannan matsalar.

 

Yayin da yake magana kan wannan tattaunawar babban daraktan hukumar kula da makamashin nukiliyan ta duniya Yukiyo Amano ya ce wannan tattaunawar dai tattaunawa ce mai matukar muhimmanci yana mai cewa a bisa mahangar hukumar shirin da ake gudanarwa a cibiyoyin nukiliyan na Iran ayyuka ne na zaman lafiya.

 

A yayin wannan zaman dai Iran ta gabatar da wasu sabbin shawarwari wadanda hukumar nukiliyan ta duniya tace tana darasinsu sosai don haka ne ma aka tsayar da ranakun 7-8 na wannan wata na nuwamba da muke ciki don sake zama tsakanin bangarorin biyu da tattaunawa kan wadannan shawarwarin.

 

-------------------------------------------------/

 

Masu saurare barkanmu da sake saduwa.

 

Kamar yadda kuka ji a farkon shirin a ranar Lahadin da ta gabata ce ministocin mai na kasashe 17 membobin kungiyar kasashe masu arzikin iskar gas suka gudanar da taron kungiyar na 15 a nan Tehran.

 

Kasashe Algeria, Bolivia, Masar, Equatorial Guinea, Iran, Libya, Nigeria, Qatar, Rasha, Trinidad and Tobago, Venezuela, the UAE da kuma Oman, sune membobin wannan kungiyar yayin da kasashen Netherlands, Kazakhstan, Iraq da Norway kuwa kasashe ne masu sanya ido a cikin kungiyar.

 

Wadan nan kasashe dai su ne ke samar da kashi 42% na iskas gas ga kasashen duniya. Sannan su ne suke da kashi 70 % na iskar gas da ke karkashin kasa a duniya. Har’ila yau wadannan kasashe ne suke da kashi 38 na bututun kwarara iskar gas ga kasashen duniya daban daban. Haka nan kashi 85 % na iskar gas wanda ake kira LNG a duniya mallakin wadan nan kasashe ne.

 

Gwamnatin Iran ce ta fara bada shawarar kafa kungiyar kasashen masu arzikin gas a duniya, inda aka kafa ta a shekara ta 2001, inda kasashe ukku, wato Iran Rasha da kuma Qatar suka gudanar da zaman kungiyar na farko a nan Tehran, sannan su ne kasashe membobi a kungiyar na farko.

 

Kasancewar iskar gas na daga cikin makashi wanda bai da hatsarin lalata yanayi, kasashe da dama a duniya suna kara rungumarsa a matsayin makamashi wanda yafi kiyaye lafiyar mutanen da sauran halittu. Har’ila yau isakar gas yana da farashi mai sauki, da kuma saukin samuwa idan an kwatanta da sauran makashi a duniya.

 

A yayin wannan taron dai ministocin man, sun tattaunana hanyoyin aiki tare, shigar da wasu kasashe a cikin kungiyar, da kuma hanyoyin bunkasa harkokin kasuwancin iskar gas a duniya. Kamar yadda kuma aka zabi Muhammad Husain Adeli dan kasar Iran a matsayin babban sakataren kungiyar na shekaru biyu masu zuwa.

 

------------------------------------------/

 

Masu saurare barkanmu da sake saduwa.

 

Ministan harkokin wajen kasar Iran Muhammad Jawad Zarif ya jaddada cewa hanyar tattaunawa da fahimtar juna ita ce kawai hanyar kawo karshen rikicin kasar Syria.

 

Muhammad Jawad Zarif ya bayyana hakan a wata ganawa da manema tare da takwaransa na kasar Turkiya Ahmad Dawud Oglo a birnin Ankarah, inda ya ce a halin yanzu kasashen duniya sun fahimci cewa aikewa da makamai da kuma sojojin haya zuwa kasar Syria babu abin da zai jawo sai kara rusa kasar, tare da cutar da al’ummarta.

 

Minista Zarif ya ce dole ne dukkanin bangarorin da suke rikici a Siriya su zauna kan teburin tattaunawa domin kawo karshen wannan rikici, domin kuwa  a cewarsa al’ummar kasar ta Syria ne kawai suke da hakkin su fayyace makomar kasarsu ba wasu gwamnatocin kasashen ketare ba.

 

Ziyarar ta Mr. Zarif zuwa Turkiyya ta zo ne a daidai lokacin da da manzon MDD kan Syria Lakhdar Ibrahim ya ke ci gaba da zaga kasashen yankin Gabas ta tsakiya don tsara yadda za a gudanar da taron Geneva 2 don magance rikicin Siriyan.

 
 
 

Ƙara sabon ra'ayi