Halittar Duniya A cikin Al'kur'ani mai girma ( 1)
Tun a lokaci mai tsawo, masana su ka dukufa wajen fahimtar abubuwan da su ka hadu su ka yi wannan duniyar da mu ke rayuwa a cikinta. Sun gudanar da nazarce-nazarce domin sanin hakikanin yadda rana da wata da taurari su ke. Hanya mafi dacewa da dabi’a wacce masanan su ka yi domin fahimtar wadannan abubuwan shi ne ta gano sanadarorin da su ka hadu su ka yi su. Wannan ne ya sa za mu ci karo da yadda masana tun a dauri su ke maganar cewa sanadarorin da su ka hadu su ka yi duniyar tamu su ne ruwa da iska da wuta da kasa. Wasu kuwa suna magana akan wani sanadarin mai daure kai wand aba a kai ga sanin hakikaninsa ba. Wannan sanadarin shi ne wanda masanan da su ka zo daga baya su ka bayyana shi da zarra bayan gudanar da bincike akansa a cikin dabunan nazari. Ita kanta kwayar zarra tana kunshe da wasu sanadarorin da su ne su ka hadu su ka yi ta, wadanda kuma za a iya bayyanawa da cewa akansu ne halitta ta ginu. Alkur’ani mai girma shi ne littafin Allah na karshe wanda ya sauka ga bil’adama. A cikin ayoyinsa kuwa ya yi bayanai masu jan hankali akan halitta. Haka nan kuma yana kunshe da bayanai akan samuwar halitta da kuma zango-zango da ta ci. A tsakanin wadannan ayoyin muna cin karo da da bayani akan tururi wanda a lokaci daya ya ke dauke da ma’anar iskar gaz a wani lokacin kuwa ruwa a matsayin wanda shi ne tubulin halitta. Abdulganiyu al-khatib wanda marubucin littafin “ Alkurni wa ilmil Asr” ya rubuta cewa: “ Ubangiji madaukaki ya fara halittar ruwa ya kuma halicci wasu sanadarorin a tare da shi. Idan ruwa ya yi zafi kuwa yana fitar da tururi. Wannan tururin yana da kauri daidai da hayaki da kuma duhu. Ubangiji ya halicci wannan tururin da nau’oi daban-daban.” Imam Bakir ( a.s) yana fadin cewa: “ Asalin dukkanin abubuwa shi ne ruwa. kuma akan ruwan ne al’arashin Ubangiji ya ke. Daga ruwa ne Ubangiji ya samar da babbar fashewa. Harshen wuta da turinta ya mutu sannan kuma ya samar da iskar gas wanda shi ne sanadarin halittar sama.” Aya ta 11 a cikin suratu Fusilat ta yi ishara da halittar sama daga gas inda Ubangiji madaukakin sarki ya ke fadin cewa: “ Daga nan kuma sai ya halicci samma, ita kuwa hayaki ce, sai ya ce da ita da kuma kasa; Ku zo kuna so, ko kun ki. Suka ce mun zo muna masu so.” A karkashin tafsirin wannan ayar, Ayatullah Makarim shirazi yana fadin cewa: Jumlar da ke cewa “ Sama ta kasance hayaki” shi ne mafarin yin halittar sammai, wanda hakan ya ke nufin hayaki na iskar gas mai turnukewa. Hakan kuwa ya zo daidai da abinda masana kimiyya da nazari su ka cimmawa. Hatta taurari masu yawan gaske da su ke a cikin sama, sun kasance ne daga iskar gas da kuma hayaki.” Wasu masu tafsiri bisa dogaro da ayoyi na 27 da 32 na suratu “Nazi’ati” sun yi imani da cewa, an fara halittar sammai ne kafin kassai da ruwa da tsire-tsire da duwatsu. Wannan ma wani lamari ne wanda ilimin a wannan lokacin ya kai ga riska. Ya zo a cikin suratun-Nazai’ati cewa: “ Yanzu ku ne ku ka fi karfin halitta ko kuwa sama ce? Shi fa ya gina ta!” Ya daukaka rufinta sannan ya daidaita ta. Ya sanya darenta mai duhu ya kuma haskaka hantsinta.” Kasa kuma bayan haka ya daidaita ta.” Ya fitar da ruwanta da makiyayarta daga gare ta. Ya kuma kafa duwatsunta.” Sanannen masanin kimiyyar nan dan kasar Rasha Goerge Gamov ya amince da cewa hayaki ko kuma iskar gas su ne sanadarorin farko na halittar sama. Ya rubuta cewa: “Dalilai da mu ke da su daga taurari suna nuni da cewa; taurari marasa iyaka da su ke a sama, suna da mafari, kuma dukkaninsu sun fara ne daga iskar gaz mai kauri.” A bisa zahirin ayoyin kur’ani sammai da kassai sun samu ne bayan matakin farko na hayaki da su ka kasance. Kuma kafin matakin hayaki, wani mataki da ya gabace shi shi ne na ruwa wanda ya taka rawa kai girma. Wasu masu tafsiri suna fassara Kalmar “Ma’a” da ruwa, wasu kuwa suna fassara ta da wani sanadari mai narkakke kamar ruwa kuma mai zafi, wanda daga cikinsa ne iskar gas ta ke fitowa. Daga cikinsa ne kuma taurari su ka samu. Wannan nazariyyar ta zo daidai da nazariyyar “Fashewa Mai Girma” ta ( Big Bang).
Ƙara sabon ra'ayi