Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai

Dukkan godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai. Tsira da amincin Allah su tabbata ga Shugaban Annabawa da Manzanni, tare da Iyalen gidansa tsarkaka da kuma zababbun sahabbansa.
 
 
Wajibi ne a dauki zagayowar lokacin aikin Hajji a matsayin wani babban idi na al’ummar musulmi. Irin damar da wadannan ranaku masu tsananin muhimmanci suke samar wa al’ummar musulmin duniya a kowace shekara, tamkar wata mu’ujiza ce maras tamka, wacce matukar aka fahimci matsayinta sannan kuma aka yi amfani da ita kamar yadda ya kamata, to kuwa za a iya magance da dama daga cikin matsaloli da barazanar da duniyar musulmi take fuskanta.
 
Aikin Hajji, wani idon ruwa ne na ni’ima da falalar Ubangiji. A halin yanzu kowane guda daga cikinku, Ya ku maniyyata, wadanda kuka sami wannan falala ta tsarkake zukata da rayukanku ta hanyar gudanar da wadannan ayyuka da suke cike da tsarki da kusaci da Ubangiji, saboda haka ku yi kokarin dibar wani abu daga cikin wannan mabubbuga ta rahama, daukaka da karfi, don yin guzuri ga dukkanin rayuwarku. Kaskantar da kai da mika wuya ga Allah Mai rahama; kudurce aniyar sauke nauyin da ke wuyan musulmi; yunkuri da kokari cikin ayyukan duniya da lahira; tausayi da yafuwa cikin mu’amala da ‘yan’uwa; jaruntaka da dogaro da kai wajen tinkarar matsaloli; fata da kuma yarda da samun taimako na Ubangiji a ko ina kuma cikin dukkanin lamurra; takaita magana da nuna kyawawan halaye na Musulunci a wannan fage na koyo da samun tarbiyya ta Ubangiji, dukkanin wadannan abubuwan suna iya zama tanadi kana kuma abin da za ku iya kawa da su, sannan kuma abin guzuri ga kasa da kuma al’ummarku. A takaice dai ga dukkanin al’ummar musulmi.
 
A yau, sama da dukkan komai, duniyar musulmi tana bukatar mutanen da suka hada tunani da ayyukansu waje guda cikin imani da tsarkin zuciya da ikhlasi, bugu da kari kan tsayin daka wajen tinkarar makiya masu bakar aniya haka nan kuma tare da gina kansu a fagen neman kusaci da Allah. Wannan ita ce hanya guda daya tilo ta ‘yantar da al’ummar musulmi daga matsalolin da suke fuskanta wadanda ko dai kai tsaye makiya ne suka haifar musu da su ko kuma sun kunno kai ne sakamakon raunin da suka samu cikin azama, imani da basirar da suke da ita tsawon zamani.
 
Ko shakka babu wannan lokacin, lokaci ne na farkawa da dawo da mutumcin da musulmi suke da shi; wannan kuwa wani lamari ne da za a iya fahimtarsa cikin irin kalubalen da kasashen musulmin suke fuskanta. A irin wannan yanayin kuwa, azama da iradar da ta ginu bisa imani da dogaro da Allah da basira da tunani, su ne za su iya ‘yantar da al’ummar musulmi daga kalubalen da suke fuskanta da kuma samar musu da daukaka da mutumci. Su kuwa makiya wadanda ba sa fatan ganin wannan farkawa ta musulmi, sun shigo fage da dukkanin karfinsu ta hanyar amfani da dukkanin hanyoyi na makarkashiya, kashe gwiwa, amfani da karfin soji da tattalin arziki da farfaganda wajen raunana musulmi da hada su fada da junansu don cimma manufar da suke da ita. Dubi cikin yanayin da kasashen yammacin Asiya kama daga Pakistan da Afghanistan har zuwa Siriya da Iraki da Palastinu da kasashen Tekun Fasha, haka nan da kasashen arewacin Afirka kama daga Libiya da Masar da Tunusiya har zuwa Sudan da sauran kasashe na daban suke ciki, zai iya bayyanar da wannan hakikar. Irin yakukuwan basasa da ke faruwa, tsaurin ra’ayi na addini da mazhaba ido rufe; rashin tabbas na siyasa; yaduwar ayyukan ta’addanci da rashin tausayi, bayyanar kungiyoyi masu tsaurin ra’ayi da dabi’ar dabbanci ta zamanin jahiliyya, wadanda suke tsaka kirazan mutane da tauna zukatansu; ‘yan bindiga dadin da suke kashe kananan yara da mata; suna gille kawukan mazaje da kuma keta hurumin sauran mutane, sannan a wasu ma suna aikata wadannan ayyuka abin kunya da tada hankula ne a karkashin tuta ta addini; dukkanin wadannan ayyuka ne da ake iya ganin hannayen shaidanci da girman kan kungiyoyin leken asiri na ‘yan kasashen waje da ‘yan amshin shatansu na gwamnatocin wannan yankin da suke kutsawa lamurran kasashe da bakanta rayuwar al’ummomin wadannan kasashen. Ko shakka babu a irin wannan yanayin, ba za a iya tunanin cewa kasashen musulmi za su iya magance matsalolin da suke da su ba, sannan kuma su tabbatar da tsaro da jin dadi da ci gaba na ilimi da tsayin daka na kasa da kasa da ya kamata su samu karkashin wannan farkawa da suka samu. Wannan yanayi mai cike da matsaloli, yana iya cutar da wannan farkawa ta Musulunci da aka samu da kuma lalata irin karfin gwiwan da aka samu a duniyar musulmi, sannan kuma al’ummar musulmi su ci gaba da zama cikin wannan yanayi na koma baya da kuma ci gaba da mancewa da batutuwan da suka shafe su masu muhimmanci irin su ‘yantar da Palastinu da sauran al’ummar musulmi daga ‘yan siyasar Amurka da yahudawan sahyoniya.
 
Ana iya takaita maganin wadannan matsaloli cikin wadannan jumloli guda biyu wadanda kowane guda daga cikinsu yana daga cikin fitattun darussan aikin Hajji:
 
Na farko: Hadin kai da ‘yan’uwantaka ta musulmi karkashin inuwar tauhidi.
 
Na biyu: Fahimtar makiyi da kuma fada da makirce-makircensa.
 
Karfafa ruhin ‘yan’uwantaka da aiki tare wani babban darasi ne na aikin Hajji. A wannan wajen an hana hatta mujadala da maganganu masu zafi a tsakanin juna. Haka nan kuma sanya tufafi iri guda da kuma ayyuka iri guda, bugu da kari kan mu’amala ta tausayawa a wannan waje tana nuni ne da daidaito da ‘yan’uwantaka tsakanin dukkanin wadanda suka yi imani da kuma girmama wannan tushe na tauhidi. Hakan kuwa fitacciyar amsa ce ga masu riko da tunani da akidar fitar da wata jama’a ta musulmi da suka yi imani da Ka’aba da kadaita Ubangiji daga da’irar Musulunci. Ya kamata masu kafirta musulmi wadanda a yau suka zamanto kayan aikin siyasar sahyoniyawa mashaya jini da masu goyo musu baya na daga kasahen yammaci, wadanda a yau suke aikata ayyukan ta’addanci da zubar da jinin musulmi da sauran wadanda ba su ci ba su sha ba, haka nan kuma da wadanda suke da’awar riko da Musulunci da kuma sanya rigar malanta wadanda suke ci gaba da ruruta wutar sabani tsakanin Shi’a da Sunna da makamancin hakan, su san cewa shi kansa aikin hajji, lamari ne da ke rusa wannan da’awa ta su.
 
A wannan karon ma ni, da kuma da dama daga cikin malaman Musulunci da masu fatan alheri ga al’ummar musulmi, ina sake sanar da cewa duk wata magana da aiki da za su kara ruruta wutar sabani tsakanin musulmi haka nan kuma da cin mutumcin ababe masu tsarki (ababen girmamawa) na dukkanin al’ummar musulmi, ko kuma kafirta daya daga cikin mazhabobi na Musulunci, lalle hakan hidima ce ga sansanin kafirci sannan kuma tarayya ce cikin cutar da Musulunci. Hakan kuwa a shar’ance haramun ne.
 
Fahimtar makiyi da hanyoyin da yake bi, shi ne rukuni na biyu. Da farko dai bai kamata a mance da kuma gafala daga samuwar makiya masu bakar aniya ba. (Ko shakka babu) jifar Shaidan da ake yi a lokacin aikin hajji, alama ce dake tabbatar kasantuwar wannan lamarin a zukatan al’umma. Abu na biyu shi ne cewa bai kamata a yi kuskure wajen fahimtar makiyi na asali wanda a yau su ne dai wadannan ma’abota girman kan na duniya da sahyoniyawa mashaya jini ba. Na uku kuma shi ne wajibi ne a fahimci hanyoyin da wadannan makiya masu bakar aniya suke bi wajen haifar da rikici da sabani tsakanin musulmi, wadanda suka hada da yada lalata ta siyasa da dabi’u, barazana da kuma kwadaitarwa ga masana, matsin lamba na tattalin arziki kan al’ummomi da haifar da shakku cikin koyarwar Musulunci, haka nan kuma wajibi ne a fahimci ‘yan amshin shatansu wadanda suke taimaka musu wajen cimma manufofinsu, shin sun san da hakan ko kuma ba su sani ba.
 
Gwamnatoci ma’abota girman kai karkashin jagorancin Amurka, suna amfani da kafafen watsa labarai da suka ci gaba ainun wajen boye hakikaninsu, sannan kuma ta hanyar fakewa da batun goyon bayan kare hakkokin bil’adama da demokradiyya, suna ci gaba da yaudarar al’ummomin duniya. Suna magana kan kare hakkokin bil’adama ne kuwa alhali a kowace rana al’ummar musulmi suna ci gaba da dandanar zafin wutar fitinar da suka kunna. Dubi cikin yanayin al’ummar Palastinu wadanda shekaru aru-aru kenan suke fuskantar zaluncin gwamnatin sahyoniyawa da masu goya musu baya; ko kuma kasashen Afghanistan da Pakistan da Iraki wadanda suke dandana dacin ayyukan ta’addancin da ya samo asali daga siyasar girman kai da ‘yan amshin shatansu na yankin nan; ko kuma kasar Siriya wacce saboda goyon bayan kungiyoyi masu gwagwarmaya da sahyoniyawa da take yi take fuskantar kiyayyar ‘yan mulkin mallaka na kasa da kasa da yaransu na wannan yankin da kuma haifar mata da yakin basasa na cikin gida; ko kuma kasar Bahrain da Myammar, wadanda kowace guda daga cikinsu, suke fuskantar zaluncin makiyan da ake goya musu baya ko kuma sauran al’ummomin da suke fuskantar barazana ta soji da matsin lamba ta tattalin arziki daga wajen Amurka da kawayenta, dubi cikin dukkanin wadannan abubuwa za su iya tabbatar wa kowa hakikanin wadannan ‘yan mulkin mallakan.
 
Wajibi ne dukkanin ‘yan siyasa da masana na al’adu da addini, a duk inda suke a duniyar musulmi, su ji cewa bayyanar da wannan hakikar, wani aiki ne da ke a wuyansu. Wannan wani nauyi ne na ‘yan’adamtaka da kuma addini da ke wuyan kowannenmu. Wajibi ne kasashen arewacin Afirka, wadanda abin bakin ciki suke fuskantar gagarumar sabani da rikici na cikin gida, su yi la’akari da wannan nauyi mai girman gaske na fahimtar makiya da kuma hanyoyin da suke bi wajen gudanar da ayyukansu. Ci gaba da wanzuwar irin wadannan sabani tsakanin kungiyoyi da jam’iyyu na kasa da kuma gafala daga hatsarin yakin basasa a wadannan kasashe, hatsari ne mai girman gaske, wanda ba cikin  sauki za a iya cike gibin da hakan zai haifar ba.
 
Tabbas ba mu da shakka cikin cewa al’ummomin wannan yanki wadanda suka mike da kuma samar da irin wannan farkawa ta Musulunci, da yardar Allah, ba za su taba bari a mai da hannun agogo baya ba da kuma sake dawo da lokutan lalatattun shugabanni ‘yan amshin shata kuma ‘yan kama karya ba. To amma ko shakka babu gafala daga kokarin ma’abota girman kai na haifar da fitina a tsakaninsu da kuma irin tsoma bakin da suke yi cikin harkokin cikin gidan al’ummomi, lamari ne da zai kara wa aikinsu wahala da kuma jinkirta zuwan lokacin dawowar daukaka da tsaro da kuma jin dadinsu da shekaru.
 
Lalle mu mun yi amanna da irin karfin da Allah Madaukakin Sarki ya arzurta al’umma da shi, sannan kuma tsawon shekaru talatin da wani abu mun ga hakan da idanuwanmu a Jamhuriyar Musulunci ta Iran. Don haka muna kiran dukkanin al’ummar musulmi zuwa ga amfanuwa da wannan kwarewa da ‘yan’uwansu na wannan madaukakiyar kasa kuma ma’abociyar himma suka samu.
 
Muna rokon Allah Madaukakin Sarki da ya tabbatar da alherorinsa ga al’ummar musulmi da kuma kare su daga sharrin makiya, (kamar yadda kuma mu ke rokonsa) da ya sanya aikin Hajjinku, Ya ku alhazan Dakin Allah, ya zamanto karbabbe, Ya kuma ba ku lafiya ta jiki da kuma guzuri mai amfani.
 
Wassalamu alaikum wa rahamatullah.
 
Sayyid Ali Khamenei
 
(5, ga watan Zul Hajji, 1434 wadda ta yi daidai da 19 ga watan Mehr, 1392 sannan 11 ga watan Oktoba, 2013)

Ƙara sabon ra'ayi